← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 86

Sashe 30

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga sakamakon gwajin da muka yi ma mahaifiyar ki nan gaskiya ta na cikin matsala ya kama ta a canza mata asibiti,saboda zuciyar ta ta kumbura dole a yi mata aiki.
Da sauri Juwairiya ta miƙe tare da zare idanun ta jin abin da likitan ya faɗa." Na shga uku Allah ka kawo min ɗauki!Mama za'a yi wa aiki!"

Sai hawaye shar-shar a fuskarta ta koma ta zauna kamar yadda likitan ya umurce ta ganin ta tada hankalinta.

" Ki yi haƙuri! Jarrabawa ce amma kar ki yadda ta ji lalurar da take da shi wannan dalilin ya sa na so namiji ya zo na gaya mishi,amma sai ta nuna ke ɗin dai zan gaya ma wa."

Da sauri ta miƙe tare da ficewa daga ofishin har ta kai ƙofar ɗakin da Mama ke kwance, sai kuma ta ja da baya ta tsaya kamar wata zararra!Tuna likita ya ce kar ta gaya ma Mama komawa ta yi wani guri ta na son ta yi kukan amma ba hawaye sai tuƙuƙi da zuciyarta take yi mata.

Ta ɗauki tsawon lokaci sannan ta koma cikin ɗakin.Da daddare Juwairiya ta kasa bacci sai juye-juye take,abin duniya ya haɗu ya yi mata yawa ji take kamar ta ɓace a cikin duniyar.

Kwana biyu kuma sai Ibrahim ya fara ciwon ƙafa wanda in ya na yi yake fita cikin hayyacin sa,don har tsuma yake na tsawon lokaci bai farfaɗo ba.Abin duniya ya yi mata yawa ga tunanin A.m da yake son ta baƙunci kabarin ta kafin mutuwarta,duk ta yi fari ta rame kamar wacce ba ta da jini a jikinta sai ƙashi da ya zama ado a jikin ta.

Zaune take a gefen Mama ta zura mata ido ta na tausayin halin da suke ciki,don ko wannen su da jinyar da yake yi.Hannu ta sa ta yarfe zufan dake goshin ta,wanda yake tsatstsafo mata duk sanda ta tuna da A.m.
" Inna lillahi."
Ta ce tare da miƙewa ta tsaya bakin windo sai hawaye." Wai dama haka ciwon so yake?Allah na roƙe ka ka cire min soyayyar son maso wani a cikin rayuwata,yayin da nake tsananin son sa shi haɗuwar mu ya zama dama a gare shi ya faranta ma masoyiyar sa rai.

Likitan ne ya yi sallama ya shigo wanda ya saka Juwairiya ta juyo da hawayen dake zuba a fuskarta,ya tausaya mata sosai amma sai ya miƙa mata takadda ya ce." Ga shi Juwairiya an baku sallama duk da jikin mahaifiyar ki bai warke ba,amma baku da kuɗi kuma mai asibitin ya na buƙatar kuɗi."

Juwairiya da ta ji ta daskare amma sai ta kai hannu ta ƙarɓa jikinta a sanyaye ba tare da tace mishi komai ba,ita zuwa yanzu hawaye sun ƙare da ga fuskarta sai wani azaban raɗaɗin baƙin ciki da take kurɓar ruwan sa mara daɗi a cikin zuciyarta wanda yafi na guba illah.

Sai ta fara haÉ—a kaya dai-dai lokacin da likitan ya fice daga cikin É—akin.

Kwana biyu da dawowar su jikin Mama ya rikice Juwairiya a daren ranar ta É—auka ba za ta kwana ba,da safe ta sami Baba Sani ta na kuka ya taimaka ma Mama da ranta yake tsakanin mutuwa da rayuwa.

"Kin ji na rantse miki Juwairiya ko mutuwa za ta yi sai dai ta yi matuƙar ba za ki amince da auren A.m ba.Ya faɗa ya na zare ido sannan ya ɗora da ce wa."Ai dama ba son ta kike ba in banda ƙashin tsiya ne dake Juwairiya irin A.m ko auren kwana ɗaya yace ki yi,ai na ɗauka jikinki na rawa za ki amince."

Haka ta dawo jiki a sanyaye ta zauna ta tare da zuba ma Mama ido ta na hawaye.Sai ta ji ɗakin ya ɗauka da wani irin abu kamar na vibration,da sauri ta miƙe don ita tsoro ta ji sai da ga baya ta koma ta zauna tuna wa da ta yi A.m ya ba ta waya,wace tun ranar ta ije ta amma abin mamaki cajin bai ƙare ba.

Sau uku ana kira amma ba ta tashi ba ta na kallon Mama dake bancin wahala,sakamakon rashin baccin da ba ta samu ba daren jiya,yayin da kiran ya ci gaba da shigo wa sai hakan ya ƙular da Juwairiya ta miƙe da sauri ganin Mama ta fara mutsu-mutsu za ta farka.

Waje ta yi da wayar ta kai hannu da nufin ta kashe don ta tabbata shi yake kiranta sai kuma ta fasa tuna da halin Mama take ciki,ta saki nauyayyar ajiyar zuciya.

Wata gefe na zuciyar ta ta bijiro mata da ta amince da auren A.m don ta ceci rayuwar mahaifiyarta duk da ta san ba ta yi ba Mama adalci ba,amma halin da suke ciki zai saka ta amince ba tare da ta yi tunanin komai ba.

Sannan ko ba komai ai auren sa ya yi mata katanga da auren tsoho a lokacin da suka rabu,ta na matsayin bazawara ba wanda ya isa ya yi mata karan tsaye a rayuwarta.

Sai dai da ta tuna tsananin son shi da take da kuma É—anta da za ta ba ma matarsa,wacce take jin yanzu bayan mutuwarta babu abin da ta tsana fiye da ita.

Ta na wannan tunanin ne ta ji muryarsa ta daki dodon kunninta ya na faÉ—in." Hello Juwairaah ki na ji na?"

Bata san ta danna wayar ba ashe ta amsa kiran da sauri ta kanga wayar a kunninta ba tare da ta yi shirin hakan ba,jin daddaɗar muryarsa da ya saka ta manta komai ta ji kamar ta zuƙo shi ta wayar saboda wani irin ƙaiƙayi na son ganin sa da idanuwanta suke mata.
" Ina jinka."
Ta ce jin ya maimaita maganar har sau uku.Ba tare da ya yi wata doguwar magana ba ya ce." Ya maganar mu kin yanke shawara? Saboda zan yi tafi zuwa India kin ga sai na gama komai kafin na tafi."

A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta sauke cikin baƙin cikin daina magana da ya yi,saboda jin muryarsa take kamar ana busa mata sarewa.

Sai kuma ta fara sheshsheƙar kuka ta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta fasa tare da kecewa da kuka.
" Oh my God! Ni fa ba na son mace mai saurin kuka haka kawai ki dinga kuka,in dai kuka za ki dinga min zamu tsamu matsala dake."
Ya numfasa ko za ta ce wani abu sai ya ji ta yi shiru sai É—an sautin kukan dake tashi a ajiyar zuciyar da take yi.
" Na amince!"

Ta furta tare da ƙara sakin sabon kukan duk da gargaɗin da ya yi mata ya shiga jikinta don umurnin sa kamar yankan wuƙa ne,sai da ta kasa hana kuka a ranta ta na tunanin yadda za su yi a tsakanin su ba a lokacin da aka ɗaura auren.

Ta ƙara buɗe bakinta da ƙyar ta ce " Don Allah ka kawo ma mahaifiyata ɗauki ta na cikin wani hali diɓ!."Ta kashe wayar tare da tsugunawa a gurin ta na jin wani hali wanda duk ƙwaƙwana na kasa gane halin da take ciki domin ita kaɗai ta san halin raɗaɗin da take ciki.

A.m ya ji wani sanyi a zuciyarsa waya ya É—auka ya kira A.k nan take ya fara shirye-shiryen yi ma Mama biza.

A lokacin da aka fita da Mama ba ta san halin da take ciki ba Juwairiya har ta cire ran zai kawo ma Mama agaji,saboda da ta ga kwana uku da maganar su bai kira ta ba wanda hankalinta ya tashi sosai.

A ranar na uku Baba Sani ya sanar ma Juwairiya su fara shiri har sujjada shukuriya sai da ta yi gani take kamar Mama mutuwa za ta yi.

Ba ƙaramin mamaki ta ji ba lokacin da Baba Sani yake gaya mata har da Ibrahim za'ayi tafiyar,zuciyarta ta haƙiƙance mata Allah ya kawo mata A.m a cikin rayuwarta don ya fitar da su halin da take ciki,sai dai in ta tuna son shi da ya mamaye mata zuciya ta na jin tausayin ranar da za su rabu wataƙila shine sanadin ta.

Su Juwairiya na ƙasar waje A.m da A.k suka shirya zuwa gidan Daddy domin su shawo kansa ya amince ya ƙarɓar mishi auren Juwairiya.

Gabansa ne yake faɗi ras! Har suka isa gidan maigadi ya wangale musu get,A.k da shi yake tuƙi ya shigar da motan.
Daddy ya na falonsa ya na ganin A.m ya tashi ya rungume shi tare da jawo A.m suka zauna a kujera me cin mutum biyu." Na yi kewar ka son ya kuka dawo? Wannan mutumim ya kirani don Allah son ka rage zuciya ka san harkan kasuwanci sai an yi haƙuri."

Sumar kan shi ya shafa tare da sakin murmushi duk da mutumim ya ɓata mishi rai matuƙa,amma yanzu ba shi ya kawo su ba.

Bayan sun ci abinci wanda A.m bai so ya ci ba amma Daddy ya matsa mishi,duk yadda yake da hope a kan sa sai gashi ya kasa sanar mishi ya na ta tunanin yadda zai fara magana.
A.k kuma ya yi banza da shi ya na ta kwasar girki shi ko tun da ya kai loma biyu wanda ya ci ne saboda takurawar da da Daddy ya yi mishi.

" Am Daddy don Alah a kwai abin da yake tafe damu,amma muna roƙon ka ka fahimci abin da ya kawo mu don Allah Daddy."
Ya yi ƙundumbalar faɗi da fuskar tausayi ya na hararar A k da ya manta da shi ya na ta aikawa cikin sa bayani,kamar da ma abin da ya kawo su kenan.
" Ina jin ka son dama har a kwai abin da za ka kasa sanar da ni?"
" Aure nake ne ma amma a kwai ƴar matsala."Ya ce ya na kallon Daddy ya ga yadda zai karɓi zancen.
Daddy kuwa tsananin tausayin shi ya kama shi da ya tuna shi ma haka ya din ga aure-aure don ya samu ɗa,amma kuma shi ne ba ya haihuwa ba matarsa ba me ya sa yake son ya ƙara aure.
" Son mata biyu anya za ka iya zama da su kai da baka da haƙuri,ɗayar ma ya ka cika bare ka tara fiye da ita.Amma tunna zaka iya faɗa min ƴar wacece kuma su waye ahalin ta?"
Chapter 30 · 0% Book details