← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 86

Sashe 41

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta fice daga ɗakin ba tare da ya sani ba jin matar so ta dawo yayin da hankalinta ya tashi,amma ta wani gefen ta na jin ina ma ace Zainab ta riske su a wannan yanayi koma mai zai faru ya faru,don ta gaji da tarin raɗaɗin azabar da take kurɓar ruwan baƙin cikinsa a cikin rayuwarta.
Ta na shiga É—aki sai ta fashe da kuka sosai har ta yi mai isar ta sannan ta rarrafa ta shiga bayi ta gana ma kanta,azaba da ruwan zafi don ta rage ma kanta ciwo da nauyin da jikinta ya yi.
Bayan ta yi wanka ta fito ta yi sallah a zaune sai bacci mai haɗe da zazzaɓi ya kama ta wanda faɗan su ya tashe ta,ba wai don ta gaji da baccon ba tunna duka yaushe ta kwanta sai dai ta ji daɗin baccin don ya ɗan rage mata wani ƙunci daga cikin damuwarta.

Ta din ga jin hayaniyar su da kukan Zainab har da saukar marin da ya yi mata.
Ta saka hannunta ta toshe kunnin ta amma sai ta ji sun sauko ƙasa suna ta faɗa sosai,ya faɗa ta faɗa sam babu tsari a rayuwar auren su don ba sa daraja juna.

Gabaki ɗaya sai ta ɗauki laifin ta ɗora akan A.m wanda yanzu take jin haushin sa fiye da komai a rayuwarta,ga wani irin kishinsa da ya ƙara ninkuwa a ranta mai girma wanda take jin kamar ta illata duk wadda ta raɓe shi.

Ta na jin suna faÉ—a daga bisani ta ji shiru sai muryar namiji ta ji ya na sasanci,wanda daga baya ta game mahaifin A.m ne.

Sasancin da aka yi a tsakanin su suka koma ciki shi ya ba ta damar yin baccin wahala,duk da ta san ya kamata ta shirya ma mutanen gidan abinci,sai dai ba za ta iya ba saboda jikinta da ko ina yake mata ciwo.

A tare suka sauko ƙasar sun ci gayu sosai an sha kyau.
Zainab ta tsaya ta na kallon dinning cike da mamaki ganin ba komai wayam.
Ta kalli A.m ta na faÉ—in." Ina wannan wawiyar take ba ta shirya min abinci ba duk da na kira ta ba É—auka ba na tura mata da text."

A.m ya da gaban sa ya faɗi amma sai ya taɓe bakin sa ya ce.

" Ina zan sani ko kin bani ajiyar ta ne?Ni da ba'a gida nake kwana ba."

Ya faÉ—a ya na wani cin magani har da É—an harara yake sakin mata.
Ƙwala mata kira ta yi sau uku sai ga Juwairiya ta fito a wani yanayi ta na jan ƙafarta.
Da masifa Juwairiya ta kalle ta ta fara magana da ce wa." Ina abinci na kuma gidan uban wa kika shiga na kira wayar ki na gaya miki zan dawo amma baki É—auka ba."

Ta faɗa tare da tsare Juwairiya da ido kamar ta na son ta gano dalilin ƙin ɗaga wayar da ta yi.
Juwairiya ta saci kallon A.m da yake zaune a É—aya daga cikin kujerun dinning ya na danna waya,kamar bai san da mutane a gurin ba amma kuma a zahirin gaskiya hankalin sa na gurin su ya na son ya ji mai za ta ce,yayin da gaban sa yake faÉ—i duk a tsorace yake sai dai ya yi ta maza ya dake.
Juwairiya ta mai da kanta ƙasa hawaye na bin fuskarta jikinta har kyarma yake yi,saboda har yanzu zazzaɓi take ji,ita kanta ba za ta ce ga in da wayarta take ba don rabon ta ita tun jiya da ya ce ta gyara masa ɗakinsa.

" Ki yi haƙuri wayata ba caji na gaya ma maigadi ya kunna jannareto don ba wuta,amma ya ƙi tashi sannan na so na kunna sola sai dai ban iya ba ina gudun kar na ɓata na haƙura k....."

" Rufe min baki nɓbanza daƙiƙiya jahila solar ce kika kasa kunnawa abu a rubuce ba na tunanin kin yi firamari,ni tsoro nake karki din ga ƙona min kayan wuta ko ki ta da gobara ai dai yi asarar kuɗin tara wallahi.To uban me ya hana ki yin abinci."

Zainab ta ce ta na hararar ta don ranta ya ɓace ta so ta samu abincinta da ta yi rashin sa na kwana biyu mai daɗi da,shi ya sa taƙi sakin jikinta ta ci abinci da za ta taho.

Wannan karon A.m ya yi tsubbul da bakinsa ya ce." Wa za ta dafa ma abincin ni da na gaya miki a hotel na ke kwana ita da masu aiki ne kawai ƙila sun yi sun ci,tunna ba ta san za ki dawo ba."
Ya ce cikin sauri ya na tsoron kar ta yi katoɓara don ganin ta fara kuka.
Juwairiya kuwa gwalalo idanunta ta yi ta na kallon sa jin ƙaryar da ya shirya mata.
Karab! Kuwa suka haÉ—a ido kowa ya yi saurin É—auke kansa.
A.m sai da ya sakin mata harara sannan ya É—auke kansa,Juwairiya kuwa wani irin kunyarsa ya kama ta ta rintse idanunta da sauri.
" Ke."

Ta daka mata tsawar da ya firgita ta." To uban wa kike ma kuka daga tambayarki?Maza ki je ki É—ora min abinci yunwa nake ji kuma ki kawo min abun da zan iya ci kafin ki É—ora girkin."

Sai hawayen Juwairiya ya ƙara zarya a fuskarata ta kalli Zainab ta ce " Don Allah ki yi haƙuri bani da lafiya zazzaɓi nake ji,ba zan iya girki ba."
Ta faÉ—a cikin muryar da ta bayyana irin kukan da ta sha tun daren jiya.
Zainab ta harare ta ta ce." Allah ya sa mutuwa za ki yi amma sai kin yi min abinci kin san yunwar da nake ji maza wuce.Kuma ki kawo min abin da zamu taɓa ni da zauji."

Ta zauna tare da ɗaukar remote ta kunna kallo ta na karkaɗa ƙafa ta na jan A.m da hira wanda ya kasa ko da tari ne ya na ta kallon fuskar wayarsa,da ya kasa ɗauke idanunsa a kanta bayan babu abin da yake yi.
Juwairiya na shiga ta haÉ—a kanta da bangon kicin É—in ta na kuka sosai take jin jikinta ba daÉ—i.
Ta daɗe a haka sannan ta soya dankalin turawa da ƙwai ta kuma haɗa musu da tea mai kauri ta kai musu,ta na tafiya tamkar wacce ƙwai ya fashe mawa a cikin ta.

" Ok maza ki je ki haɗa mai nauyi don wannan ba zai ƙosar da ni ba."

Ta ce mata ba yan ta ije mata ba tare da ta kalle ta ba.
"Anty Zainab ki yi haƙuri ba ni da lafiya don Allah sa..."
Mari ta wanka mata a fuskarta da take jiƙe da hawaye ta ce.
" Ban san lokacin da kika raina ni ba har kike musayan yawu da ni banza dangin matsiyata!Maza wuce ki yi abin da na saki."

A.m ya tashi da sauri ya na faÉ—in " Haba Zainab ta ce miki ba ta da lafiya ba ki da tausayi ne.."
Katse shi ta yi ta ce." Ba da kai nake yi ba ba ta da lafiya ta sha magani,uban wa take son ya yi mana girkin meye amfanin ta a gidan?Ko ubanta yake neman ma na kuÉ—in da za mu biya ta?"

SAUKAR MARIN YA SA NA FIRGITA AMMA NA CI GABA DA RUBUTU SAI DAI KUMA TAUSAYIN JUWAIRIYA YA HANANI ƘARASAWA,DON NA KASA GANE MAI NAKE RUBUTA AN YA ZAINAB KIN KYAUTA KUWA.
KUCI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN BARI NA ƘARA TUNA MUKU DA SUNAN LINTAFIN
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO

TUNATARWA

DON ALLAH ƳAN'UWANA MATA KADA KARATUN LINTAFI YA ƊAUKE HANKULANMU MU MANTA DA BAUTAR UBANGIJI,KU TUNA ALLAH YA HALICCE MU DON MU BAUTA MASA NE.

GOBE JUMA'A KAR A MANTA KARATUN SURATUL KAHAFI ALLAH YA BA MU ALKAIRUN DA KE CIKINTA AMIN

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha shidda.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 20*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

A.m har ya buɗe baki zai ƙara magana sai kuma ya fasa,ya ɗauki wayar sa ya haye sama ba tare da ya ƙara kallon ɗaya daga cikin su ba.

Juwairiya ta dafe ƙuncinta hawaye na zarya a fuskarta da ma ta san dole watarana Zainab za ta dake,ta tun da halinta ne sai dai yadda ta ji saukar marin ta ji sam ba za ta iya ɗauka ba,domin da ya zo neman aurenta bai gaya mata har da duka a ciki ba.

Hawaye ta share ta juya ta nufi kicin saboda rashin ƙarfin da take ji,tsayuwa ma wahala take mata don haka ba ta ƙara ce wa komai ba ta shige kicin ɗin.

Jingina ta yi da slinder na gas ɗin kicin ta saki kuka duk da ta na jin cewar,lokaci ya yi da za ta dai na asarar hawayen a banza akan su saboda ta fahimci bayan damuwar da suke saka mata,har da na auren su da suke faɗa kamar kaji su hana ƙwaƙwalwarta sukuni.

Da ƙyar ta samu ta kammala girkin da taimakon Baba da ta dameta da tambayar mai ke damunta,ganin ta ƙi tanka mata sai ta kalle ta ta ce bayan ta gama kwashe abinci ta saka a kula.

"Ƴar nan ya kama ta ki naimi maganin basir saboda shi yake damun ki,ji yadda kike cije baki ki na tafiya da ƙyar."

Da takaicin maganar da ta yi mata É—aki ta wuce ba tare da ta tanka mata ba.

Tun daga wannan ranar Juwairiya ta kame kanta ba ta barin ko haÉ—uwa da shi su yi,saboda wani irin kunyar sa da take ji kamar ta nitse in ta gan shi,don ko gyaran muryar shi ta ji sai jikinta ya kama rawa kamar za ta ruga.
Chapter 41 · 0% Book details