← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 86

Sashe 26

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ta ina zan sanar maka bayan ka kashe wayarka.Son ya yi laifi a yafe mishi don kawai kun samu saɓani za ka dai na zuwa aiki, in ka ƙara hakan zan hukuntaka ta hanyar turaka ƙasar waje ka yi wata biyu ba tare da ka dawo gurin iyalin ka ba,saboda ka ɓata min rai kuma na yi fushi da kai."

Jin abin da ya faɗa da sauri maman Najwa ta miƙe tare da ficewa ko gaisuwar da ta tsaya ta yi ma Daddy ba ta yi ba,don ya ba ta kunya duk da ta san in ya yi hakan ya cutar da rayuwar masoya.

" Ka yi haƙuri Daddy na yi nadama hakan ba zai ƙara faruwa ba! Da ma A.m ɗin ne ya...."

" Daddy ya yi haƙuri kawai ya koma aikin sa ni nama haƙura akan maganar da muka yi na fasa na janye."

Yace da sauri ya na kallon A.k don ya tsorata ya ɗauka gaya ma Daddy zai yi.Daddy ya kalle su duka kamar a kwai abin da suke ɓoye mishi wanda shi ne ya kawo musabbabin faɗan.

" To wai me ya kawo rikicin?"

Ai kafin ya rufe bakinsa A.m yace."Daddy ba komai ai mun shirya ya wuce."

A.k dai bai ce komai ba Daddy ya kama hannunsa ya haɗa." Kar na ƙara jin kun yi faɗa ku yi min alƙawari."

"Hakan ba zai ƙara faruwa ba Daddy komai ya wuce."Kamar sun haɗa baki don a tare suka faɗa. " Ok ka shirya ka taho aiki dama ina son na ƙara maka girma."

A ranar dai ba wata magana na amininai da ya shiga tsakanin su,amma tare suka fita zuwa aikin sai dai A.k ko zuwa su tafi cin abinci kamar yadda suka saba bai yi ba,don har yanzu ya na jin haushin abin da ya yi mishi hakan ya sa yake yin azumi don ya rage mishi fushinsa tunna ko Allah muna mishi laifi kuma ya yafe,amma shi mutum ne wanda ya san mahimmancin kansa.

Ƙin zuwa su je suci abinci hakan ya tabbatar ma A.m bai huce ba sai da ya daidaici ya gama tarin aiyukansa da ya jibga ma kansa,ya shiga ya na zaune a kan kujerar ofishin ya rintse idanun shi wataƙila bacci yake.

Shigar shi ya farkar da shi ya tashi ya zauna." Don Allah ka yi haƙuri haba na san ina da fushi,amma ba ni da riƙo na lura kafi son Juwairiya da ni na haƙura da haihuwar don ni ba zan aure ta ba don na rayu da ita har abada,amma tunna ba ka so mu manta da zancen.

Ga mamakinsa sai A.k ya bugi bayan sa ya na dariya yace." Haba na manta da wannan kuma akan maganar Juwariya na yadda ka aure ta Allah zan ba ka gudummuwa in har Daddy zai amince ya nema maka auren ta a sirri."

Ya ɗan kalle shi ko ya yi tunanin wasa yake masa amma bai ga alamun haka ba sai ya rungume shi ya na faɗin." Na ji daɗin amincewar ka yamzu mu tafi gurin ƙanin mahaifin ta."

Tofa masu karatu kun dai jin yadda ta kaya game da waÉ—annan aminan juna,Baba Sani zai yadda ya basu auren ta.Ku ci gaba da bibiyata na gode da yaba lintafina da kuke.

ÆŠUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ÆŠIN KU YA NA SAKA NI NISHAÆŠI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha huɗu.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 14*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Sakamakon aiki da ya yi musu yawa sai hakan ya hana su zuwa kamar yadda suka shirya a ranar,saboda ba su tashi daga gurin aiki ba sai bayan sun yi sallar magariba daga nan kowa ya nufi gidan sa.

A.m ya ji daɗi sosai ranar kasa bacci ya yi gani yake kamar ya auri Juwairah ya gama musamman da aminin sa ya amince,duk da a cikin zuciyar sa har yanzu ya na tunanin mai ya saka A.k ya sauko har ya amince duk da dokin naƙi da ya hau daga farko.

A haka dai ya yi ta saƙe-saƙen shi amma ya rasa gano komai daga ƙarshe ya janyo bargon da Zainab ta rufe jikinta da shi ta na bacci,ya rufa da shi tare da juyawa dai-dai fuskarta ya rungumeta ya na shaƙar daddaɗar ƙamshi daga gareta,yayin da hankalin sa yake kwance kamar ya yi baƙo ya mutu a ransa duk ya ƙosa gari ya waye su ji yadda za su kaya da ƙanin mahaifin Juwairah.

A.k kuwa ko da ya koma gida hankalinsa a tashe gani yake kamar ya aikata zunubi me girma akan amince masa da ya yi,amma da ya auna a mizanin hankali sai ya ga da ta auri wannan tsohon rayuwar ta ta shiga garari gara A.m da ko ba komai za su samu ci gaba a rayuwa,duk kuma abin da zai faru wannan kuma ya bar ma Allah lamuran sa shi yake da iko akan komai,kawai abin da zai yi shi ne ya gaya ma Juwairiya kar ta yadda zuciyarta ta fara son A.m.

Ya daɗe sosai ya na shawara kafin ya furta ya amince da auren musamman da ya ji mahaifiyarta ba da lafiya,a taƙaice dai tsotsan tsamiya suke yi a rayuwar su tare da alhini.

Washegari da safe A.m ya yi mishi dirar mikiya ko karyawa a gidan sa ya yi,wanda Maman Najwa ta yi mamakin sammakon sa amma sai ta yi tunanin ko ya na son A.k ya manta komai.

Bayan sun gama karyawa suka nufi gidan su Juwairiya.

Baba Sani ya na ƙoƙarin fita gurin aiki da ƴar ƙaƙuran motarsa da yake riƙe da makullin ta a hannun sa ya na karkaɗawa.

Ganin su a kofar gidan sai ya yi turus ya na tunanin mai ya kawo waÉ—annan larabawan kofar gidan ko sun yi makuwa ne,saboda ya na da É—agawa sai ya É—auke kansa zai shige cikin motar sa ba tare da ya kalli in da suke ba,duk da tunani ya cika ran shi ganin sun tunkaro sa.

"Assalamu alaika Malam barka gurin ka muka zo,don Allah ko zaka ba mu lokacin ka duk da ba ka san da zuwanmu ba,amma in ka bamu Æ´an mintuna zamu tafi musammam in ka yi ma abin da ke tafe damu kyakykyawar fahimta."

Yace da shi da murya mai sanyi duk ƙoƙarin sa ya tabbatar masa da baƙin sa ne saboda fuskar sa ta nuna kokwanton ko sun yi makuwa ne,duk da ya san ya na da ƴan mata amma ko kaɗan bai yi tunanin za su zo neman ɗaya da ga cikin su.

Ya kalli A.m da ya É—aure fuskar sa kuma bai ce komai ba ya lura wamda ya yi mishi magana ya fi shi sakin fuska,sai ya mai da hankalinsa ga A.m yace a cike da shakku don shi har yanzu bai yadda gurin sa suka zo ba.

" An ya gurina kuka zo ko kuma kun yi makuwa ne wataƙila tambaya ce da ku."

" Ka na shakkun mun zo gurin ka ne mu ba mutane ba ne? Ko aljanu ka gani." A.m ya ce mishi ba tare da ya kalle shi ba hankalin sa na gurin wayar sa dake hannun sa ya na daddannawa.

Baba Sani nan take ya ji ran shi ya ɓace ya kalle sa a ran sa ya na faɗin." Ba ka sanni ba kenan amma bari na ji da wanne kuka zo."

" Gashi kuma sauri nake zan tafi aiki sai fai ku dawo wani lokacin." Ya ce fuskar sa a É—aure ganin A.m ya zo da rainin wayo.Am ya buÉ—e baki zai yi magana sai A.k ya watsa mishi kallo kuma aka ci sa'a ya yi shiru ya ci gaba da kallon wayar sa.

" Don Allah ka yi haƙuri ka bamu ƴan mintina kamar yadda na buƙata da farko ka saurari abin da yake tafe da mu."

A.k ya ce cikin marairaicewar fuska ya kuma haɗa hannun sa biyu ya na roƙon sa.A.m kuwa kofar gidan ya din ga bi da kallo ya na jin wani tsigar jikin shi na tashi,wai shi zai haɗa jini da ƴar wannan wulaƙantaccen gidan mai kama da bola,duk da Baba Sani ya na ƙoƙarin gyarawa amma abincin wani gubar wani.

" Ok to muje in har zaku taƙaita maganar da ta kawo ku a cikin lokacin da kuka iba."

" In sha Allahu."

A.k ya bashi amsa a lokacin da suka shiga cikin gidan zuwa ɗakin Baba Sani A.m ya na ta wulƙita ido ko zai ga Juwairah don shi yanzu ma ya manta da kamannin ta.

"Maza ku gaya min mai yake tafe daku da farko ina fatan ba laifi na yi ba kuka zo kama ni."Ya faÉ—a kamar kuma ya ji tsoro a fuskar sa.

Hakan ya sa A.k ya murmusa shi ko A.m ko kallon sa bai yi ba.A.k ya gyara zama ya kalli Baba Sani ya ma rasa yadda zai fara ya na son ya ce A.m ya faɗi buƙatar da ta kawo su,amma ya san dunƙula maganar zai yi ta yadda ma ba zai fahimce shi ba ya lalata abin,bayan dai in ina da ya yi,ya kuma shiga ƙumbiya-ƙumbiya daga ƙarshe ya faɗi abin da ya kawo su don barin kashi a ciki baya maganin yunwa.

Alokacin da Baba Sani ya ji maganar da A.k ya faÉ—a sai ya ji kamar bai fahimci maganar ba kuma har ga Allah a cikin zuciyar sa ya gasgata hakan da bai ji ba.
Chapter 26 · 0% Book details