← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 86

Sashe 37

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa bacci ta yi ta na ta juye-juye girman gidan yake matuƙar tsorata ta, sai take ganin kamar wani zai shigo ga ihun karnikan gidan da suka hana kunninta saƙat!

Da ga ƙarshe ma tashi ta yi ta ɗauro alwala ta yi sallah sannan ta ɗauki alkur'ani ta na karatun suratul Ali imran don ta samu ta yi bacci.

A ƙalla mutane gidan sai da suka yi sati biyu ba su dawo ba.A.m ya fara dawowa ranar talata da rana dama tun da safe Zainab ta kira Juwairiya ta gaya mata zai dawo ,don haka ta shirya abinci wanda Zainab ta saka direba ya siyo duk kayan buƙata na girki.

Misalin biyu da rabi ya shigo da jakar shi rataye a kafaÉ—ar sa,sai dai kamar mahaukaci ya shigo saboda zargin sa da yake na Zainab ta yi tafiya zuwa Dubai saro kaya duk da ya hana ta.
Duk da cewa ta ji shigowar shi sai ba ta fita ba ta yi zaman ta a É—aki ta na jan carbi,domin ta sama ma kanta natsuwa.

" Ina Zainab?"

Muryar sa ta ji lokacin da ya banko ƙofa ya shigo da sauri ta matsa ganin kamar zai kai mata duka lokacin da yake tambayarta.

Ba ta ba shi amsa ba amma yanayin da take kallon sa ya tabbatar masa da Zainab ta tafi duk da gargaɗin ta da ya yi,cikin ɓacin rai ya lailayo ashar zai yi ko me ya tuna sai ya fasa ya fita cikin ɗakin da sauri.

Juwairiya da sauri ta bi bayan sa saboda tashin hankalin da ta ga ya shiga,abincin da ta girka masa ya yi jifa da kwanonin da suke jere a dinning É—in,ya zaro wayar sa ya kira ta sai dai har ta gama ringing ba ta É—auka ba.

Jifa ya yi da wayar ta faɗi a kan tayas ta fashe ya dunƙule hannun sa guri ɗaya ya furta." Zainab ki na son sa min hawan jini sai dai wannan karan ba zan ɗauki wannan iskancin ba,ina mijin ki ki tsallake ki tafi wata ƙasa hakan ba zai yiwu ba.

Idanun Juwairiya suka kawo ruwa sai hawaye ganin ita kuma haka Allah ya ƙaddara rayuwar ta su dun ga sauke fushin su akan ta.

" Ke!"

Ya daka mata tsawar da ya firgita ta sannan ya ci gaba da magana da ce wa." Wallahi yanzu jikin ki zai gaya miki dukan ki na yi zaki saka min kuka bayan na gaya miki na tsani kuka a rayuwata,maza fice ki ba ni guri sannan ki ƙara min wani abincin.

Hakan ya ƙara saka ta sakin wani kukan tuna yadda ta sha wahalar girkin ya zubar kuma yake buƙatar ta ƙara yi masa.
Da sauri ta wuce kicin ta bar shi a falon ya kai gwauro ya kai mari da ga ƙarshe wayar sa ya ɗauka da nufin ya kira A.k,sai dai kuma ya ga aika-aikar da ya yi tsaki ya yi da nufi ɗaki don ya ɗauko wata.

Bai jima ba ya fito bayan ya yi wanka ya canza kaya ko kallon abincin da ta girka bai yi ba ya fice daga gidan.

A haka suke ta zama na rashin daɗi duk da A.m na buƙatar ya kawo ƙarshen zamanta a gidan amma ya kasa,haka dai yau ya daure da nufin zai yaƙi zuciyar sa don ta bar mishi gidan sa saboda ba ya son ganin ta a ciki.

Da misalin biyar da rabi ya dawo gida Juwairiya na falo ta na kallo da ƙaton hijabin ta,ya na hango ta ya tsaki wawan tsaƙi saboda shi haushin hijaban da take sawa yake yi bayan ta san ko shi wanene a gurin ta.

" Wawiya ƙazamiya a haka yadda kike ɓoye jikin ki ko uban me take ɓoyewa shi bai ga abin sha'awa a jikin ta ba."

Ganin sa ya sa ta miƙe da sauri za ta shige cikin ɗakin ta.

"Ke."
Tsayawa ta yi ba tare da ta kalle shi ba don ta san wani wulaƙancin zai yi mata.
Hararar ta ya yi ya zauna akan kujera tare da É—aukar remote ya canza tasha,sannan ya kalle ta ya ce " Gidan uban wa za ki saboda dodo ya dawo ko?Wai haka kika ga matan aure suna rayuwa a gidan mazajen su kullum cikin hijabi ke sam baki da wayewa ne?"

Juwairiya ta yi sororo ta na kallon shi jin wani sabon salon da ya fito da shi,amma ba ta ce masa komai ba sai kallon shi da take tamkar baƙo a gare ta.

" Maza ki je ki kawo min abinci."

Ya ce ganin ta kafe shi da ido ba ta san shi ma ransa a ɓace yake maganar ba saboda tsanar ta da yake ji kuma wai ta na matsayin matar sa.

Juwairiya ta so ta bi umurni n shi ta cire hijabin sai dai ina sam ba za ta iya ba,don tsananin kunyar shi take da ke,don haka ta ƙi cire hijabin ta ɗauko abincin ta na ije mishi ta ruga zuwa ɗaki.
Bayan ya ci abinci ya na zaune a falon har aka kira magariba ya yi sallah bai dawo ba sai da aka kira isha'i,sannan ya dawo gida ya rufe gidan duk da ran sa a ɓace yake akan Zainab kuma ya rantse in ta dawo sai ta ga abin da zai yi mata,amma sai ya daure ya ɗauki wayar sa ya shiga ɗakin.

" Ki biyo ni ɗakina kin san ba zan iya kwana a ɗakin ƙasƙantu ƴan aiki ba."

Ya fice kallon sa kawai ta yi amma ba ta ce mishi komai ba har ya fita ta gyara kwanciyar ta tare da karanto addu'ar bacci ta janyo bargo ta kwanta.
" Wataƙila maganar Baba Sani ta yi tasiri a zuciyar sa ya yadda ba ni da kamun kai ne har yake tunanin na bi shi ɗakin sa a she zai bushe da jira na.

Washegari da safe bai ci ko abincin karyawar da ta yi masa ba ya fice daga gidan, don ko da ta gaishe shi harara ya banka mata.
Sai abin ya ba ta dariya kawai ta ruga da sauri ta laɓe a ƙofar falon ta na kallon sa har ya fice saboda wankan da ya yi ya tafi da imanin ta.

Sakin labulen ta yi ta zauna a falo tare da ɗaukar filo ta rungume a ƙirjinta ta na jin wani irin nishaɗi, don ko kaɗan ba ta yi tunanin rayuwa tare da shi ba ko da kuwa a matsayin matar sa kuma ƴar aikin matar sa.
Bai shigo gidan ba sai da daddare tare da A.k suka shigo suna ta hira abin su.
A.k na ta baza ido ya gan ta bai gan ta ba musamman da ya ga Zainab ba ta nan,kallon A.m ya yi da yake ta aika ma cikin sa abinci saboda tun zuwan Juwairiya gidan hankalin sa ya kwanta na rashin samun abinci.

" Kai wai ina maryar ka ne ?Tun na yanzu madam ba ta nan na san ƙila an samu baby?"

Ya faɗa ya na kallon shi ya na dariya tare da kai mishi duka a kafaɗan sa.Taɓe baki ya yi ya ce.Ina zan sani kai kyale ni da wani amarci Juwairiya muguwar bagidajiya ce kullum cikin hijabi ka san kuma ba haka Zainab take min ba."

Ya ɗan kalli A.k da ya daina cin abincin ya na sauraron sa ya ce."Jiya da na kira ta ɗakina ƙin zuwa ta yi ban san tunanin ta a kai na ba."

" To kai in ban da abin ka A.m ai kai za ka bi ta kuma kuma mace take Hausa dole ta ji kunya."
A k ya ce da shi ya na kallon sa.A.m ya ƙara taɓe bakin sa ya ce." Ok ka manta abin da ƙanin mahaifinta ya ce a kan ta ni ban ga abin kunya ba."
"A haba A.m ka san halin sa kar ka yadda da maganar sa kuma koma mene ne kai ka amince za ka aure ta sai ka ba da azama mu sami baby.".
Dariya suka yi duka daga bisani A.k ya matsa mishi ya kira ta su gaisa ya na zaune ya ƙwala mata kira ba ta jima ba sai ga shi ta fito,kamar dama laɓe take musu ta na jin maganar da suke yi.

A.m tashi ya yi ya nufi ɗakin sa zai ɗauko tsaƙon da A.k ya biyo shi ya karɓa ba tare da ya kalle ta ba.

Da ladabi ta gaishe shi ya amsa ya na ta tsokanar ta dai murmushi take masa.
" Na so mu haÉ—u kafin ayi auren ki da shi sai dai kuma Allah bai nufa ba ko Juwairiya?"

Ya faÉ—a tare da mai da maganar ta tsigar tambaya.ÆŠaga masa kan ta ta yi ta na kallon shi " Ok ba komai da ma na so na É—an miki wata magana ne Juwairiya don Allah duk yadda zuciyar ki za tai ki karki yadda ki saka son A.m a ran ki kawai ki sama ran ki zaki ci arziki ki tafi ne.Ki É—auke ni a matsayin Yayan ki duk lokacin da wata matsala ta haÉ—a ku ki sanar da ni."

Ya yi maza ya ƙarashe maganar jin takun A.m daga matakalar bene.Kallon sa ta yi sai kuma ta ji ya burge ta sosai yadda bai ɗauki rayuwar sa da zafi ba.
ÆŠaga masa kanta ta yi alamun ta ji amma kuma a cikin zuciyarta sai ta ce.
" Ka makaro A.k da ce wa ka yi na yaƙi zuciyata da take son sa ƙila da na karɓi shawarar ,amma na riga na daɗe da shiga cikin kogin son sa."

Sai da A.m ya yi masa rakiya sannan ya dawo ya tsaya ya na kallon Juwairiya da ta kasa tashi ta na ta tunani a ranta." Me hawayen banza maza ki tashi ki gyara min ɗakina saboda yau haushina da kike ji sai kika huce akan ɗakin,sam gyaran bai yi kuma ki ƙara wanke bayi."
Ya faÉ—a tare da zama a falon kamar ya na son ta gama sai ya shigo.
Wucewa cikin É—akin ta yi ba tare da ta ce masa komai ba amma ya faÉ—i son ransa ne kawai duba ga yadda take ba da dukkan lokacin ta in ta je É—akin sa gyara.
Chapter 37 · 0% Book details