← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 86

Sashe 56

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ba na son wulaƙanci Nabila mijina za ki din ga haɗa shi da wata.A kwai yadda a tsakaninmu da shi,muddin kika ce za ki faɗi wani abu na rashin kirki a garesa wallahi yanzu za mu raba jaha da ke."

Ta buɗe baki za ta ƙara magana ta ɗaga mata hannu tare da nuna mata ƙofa."Ki fitar min daga gida na yanke duk wata alaƙar da ke tsaƙaninmu."

Miƙewa ta yi ta ɗauki jakarta ta na kallonta.
" Bazan yi fushi da ke ba ƙawata zan yi miki uzuri har zuwa lokacin da za ki gane gaskiya,ni na san dole wata rana za ki neme ni bayan kin gane cin amanarki yake yi."

Har ta fara taku bayan ta gama magana sai kuma ta dawo,ta tsaya gaban Zainab tare da riƙe hannunta ta na hawaye ta ci gaba da magana.

" Ba wai ina son na tona miki rayuwar aurena ba ne a'a sai don na gaya miki don ki ɗauki darasi a ciki.Kamar yadda kika ba wa A.m amana haka na ɗauki yaddata na ɗora akan Al'amin,ba ni da haufi akan sa na yadda da shi fiye da yadda na yadda da kaina.Kwasam na kama shi da kwandom a aljihun sa wanda hakan ya ɗaga hankalina matuƙar gaske har sai da na kwanta jinya.Na yi kuka sosai rikici sosai muka yi sai daga baya na haƙura bayan duk mutuncin sa ya zube a idanuna."

Fara tafiya ta yi bayan ta gama gaya mata ta na kuka.

Jikinta ya yi sanyi da sauri ta kama hannunta ta riƙe tare da faɗawa jikinta ta fashe da kuka sosai.

"Don Allah Nabila karki saka zuciyata ta gasganta abin da kike faÉ—a min domin zuciyata ba za ta iya jure ganin A.m da wata mace ba!Kin ji na rantse miki duk ranar da A.m ya yi gigin kallon wata Æ´a mace to ni ce ajalinmu baki É—aya,nufin sa zai iya ganin É—ansa a duniya bayan ni na lalata rayuwata saboda shi?"

Ta ce ta na kuka tamkar wata wacce aka yi wa mutuwa sai kuma ta janye jikinta tare da share fuska.
" Kai ina! Zuciyata kasa karɓar zargin da kike masa A.m ya yi min alƙawarin ba zai kula ko wace ƴa mace ba kuma na yadda da shi,in kuwa zargin da kike masa ya zamo gaskiya wallahi sai na canza kamannin ko wace ya mace da ta haɗa jiki da shi, ke bama Juwairiya wulaƙantacciya ba ko yar gidan uban waye acid zan wasa ma shegiya ta mutu kowa ya huta."
Cikin matsancin kuka take magana gabaki ɗaya hankalinta ya tashi,sosai duk da ta yi ƙoƙarin ta saka zargin da take ma A.m,amma in ta tuna ko kallon fuskarta ba ya yi bare ya riƙe sunanta sai ta ji sanyi ta kauda zarginta.

" Haba Zainab kamar ba ki waye ba ina bokon na ki yaje? Ai yanzu karki nuna komai ki nuna tamkar ba ki san da wannan maganar ba,sannan ki saka matakan tsaro ki sa ido sosai a tsakanin su duk wata hanya da zai saka ki fahimci ko da wani abu ki kula da ita sa..."

" Kai."

Zainab ta ce sannan ta kalle ta taci gaba da magana." Ta ya ya za'ai na kauda kishina na saka ido don in gano abin da suke yi,ba zan iya ba ni kawai zan tambaye shi ne in ya gaya mini ƙona su duka zan yi,in ya so duk abin da zai faru ya faru!" Ta furta cikin tashin hankali yayin da take ji sam ba za ta iya ba.

"Na san ba zai iya auren Æ´ar aiki ba,amma yanzu sun cika É—ora kwaÉ—ayin su ba sa iya É—auke idanun su.
Ki É—an danne kishinki ki gano wani abu in har kika gane ya na tare da ita, ni zan siyo miki acid ki watsa mata,ko ki bani kwangilar watsa mata babu uban da zai É—aure ni yar manya ce ni mijina kuma canal."

Da ƙyar Nabila ta yi nasarar kwantar mata da hankali,duk da har yanzu ta kasa amincewa,don haka ta saka a ranta ya na dawowa za ta tambaye shi dole ya gaya mata komai.

A tare suka fito daga É—akin suka nufi kicin in da Lantana take aiki,ganinZainab da gudu ta ruga ta na faÉ—in.

"Wallahi Hajiya na gan...."

Da sauri Zainab ta ɗora ɗan yatsa a bakinta kan ta yi shiru,don ta na jin kamar ta ƙara mata wani dukan.Kuɗi ta ƙara ma Lantana da take ta murna sosai ga duka ga samun kuɗi ita kam yau gulma ta yi riba.

Zainab na zaune a gaban madubi ta na tsantsara kwallliya zuciyarta cunkushe da tunani kala-kala.

Ji ta yi an rungume ta ta baya sannan ya ɗora kan sa a bayanta,ba ta juya ba kasancewar tun kafin ya shigo ƙamshin turaren sa ya bayyanar masa da shigowar sa.

Fuskarta a ɗaure ta juyo ta kalle shi sama da ƙasa haka kawai sai ta ji wani mugun haushin sa da tsanar haɗa jiki da shi.

Sakar mata murmushi ya yi tare da kamo hannunta.

" Gibbiyar mata sarauniyar mata a cikin birnin zuciyar Abdurrahman mai na yi ake fushi da ni? Ko don rashin dawowata da wuri ne am so so sorry babyna wallahi wani uzuri ya tsare ni na kira wayarki ba ta shiga."

Ya faÉ—a da muryar sa mai sanyi da take kwantar mata da hankali ya kuma san ya na sace zuciyarta da ita.

Ganin ta ƙi kula shi sai ya kamata suka faɗa gado ya na shaƙan kamshin turarenta ya na faɗin.

" Wane irin turare kika sa yau kamar yafi wanda kike shafawa daɗi,don ban taɓa jin ƙamshi mai kwantar da zuciya da saka nishaɗi a rai ba..

Gaskiya kuma kwalliyar ta yi na kuma yaba bari kiga in siye ta koma nawa ne babu tayi."

Ƙoƙarin warware tawul ɗin dake jikinta yake yi ya na gaya mata kalamai masu daɗi da kwantar da hankali.

Da sauri ta ƙwace jikinta ta harare shi ta saki tsaki ta saka kayanta ta fice daga ɗakin ba tare da ta kalli in da yake ba.

Tsayawa ya yi yana kallonta ran sa ya ɓace saboda ya tsani tsaki ita ma ta san haka,don haka bai ƙara kula ta ba ya tuɓe kayan sa ya watsa ruwa,bai nemi abincin ba saboda sai da ya tsaya gidan A.k ya ci abinci tun da ya san Juwairiya ba ta nan gashi ya kasa iya cin abincin Lantana.

Kwanciyar sa ya yi ba tare da ya ƙara kula ta ba,wanda hakan ya sa ta fara yadda da abin da Lantana ta faɗa mata,tun da har zai iya ƙyaleta ganin ta yi fushi ba tare da ya rarrashe ta ba ko ya tambayi ba'asi.

Tun tana saka ran zai zo ya rarrrasheta amma sai ta ji shiru,ta kalli agogon hannunta ƙarfe ɗaya na dare sai ta sauka a chert ta shige ɗakin sa tare da buga ƙofar da ƙarfin gaske.

Tsayawa ta yi a kan sa ta na huci kamar wata mesa ganin bacci yake yi,filo ta ɗauka tare da maka masa ya buɗe ido cikin razana ganin ta tsaye a kan sa sai ran sa ya ɓace,ya kalle ta bai ce mata komai ba amma idanun sa suna masa kallon gargaɗi.

" Kaga Malam ka tashi magana nake son mu yi da kai."Ta ce dashi tana girgiza ƙugu idanunta a bushe kamar ba dare ba.

" Zainab."

A cikin wata irin murya ya yi magana sannan ya É—ora da ce wa." Don Allah bacci nake ji ki bari sai da safe."
Ya rungume filo tare da mirginawa ya ci gaba da bacci,komai ya tuna sai ya juyo ya na kallonta ya miƙo mata hannu yana nufin ta zo su kwanta.

Wani irin kallo ta watsa mishi." Ka ga Malam wallahi sai ka tashi ba za ka barni da baƙin ciki na kasa bacci ba don ba zan iya bari gari ya waye ba."

Sai ta fara tsiya ta na mishi wasu irin maganganu da ya kasa gane mai take ce wa,sannan kuma ta hana shi bacci da ga ƙarshe dole ya tashi saboda magana take da murya mai ƙarfi,kuma abin da take faɗi ya yi mugun ɗaga masa hankali duk da bai wani fahimce ta ba.
Tashi ya yi zaune ya na mata wani mugun kallo.

" Wallahi baki da mutunci ga shi na tashi gaya mini damuwarki,amma ki sani in na ji maganar ba ta da mahimmanci kin san sauran."

Ya faÉ—a da muryar gargaÉ—i ganin ta hana shi bacci.

Hararar shi ta yi tana faɗin" Oh koma me za ka ce kai ka sani tun da ka zama munafuki, ka bani mamaki fir'auna a zuci Annabi Musa a baki." Ta faɗi hakan ne don ta gane ko ƙarya Lantana take mata don har yanzu ta kasa yadda da abin da ta faɗa mata.

Bai ce mata komai ba ya ƙara watsa mata mugun kallo na na gargaɗin ta iya bakinta.

Cikin tsanani mamaki A.m ya ji ta watso mishi tambayar da ya girgiaza shi ta ce.

" Mene ne alaƙar ka da Juwairiya?"

Ya shiga cikin tsanani tashin hankali ya ruɗe matuƙa ya kuma razana domin jikin shi rawa yake ayi,jin tambayar da ta watso mishi ya shiga damuwa Baba Sani ya faɗo mishi a rai yana tunanin ko shi ya faɗa mata,ya san zai iya don ya na shakkar sa ba shi da mutunci na ƙarshe.

Allah ya so babu wadatacciyar haske a ɗakin sai fitila mara haske na bacci dake kunne mai kama da babu,domin da a kwai ya tabbata babu abin da zai hana ba ta gano gaskiya ba,saboda jikin sa ya jiƙe sharab da gumi sai zufa yake karyo mishi,ya na ji a ran sa in Allah ya haɗa shi da Baba Sani sai dai Allah zai raba su.
Chapter 56 · 0% Book details