Sashe 53
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ta nuna kanta da yatsa ta ce."Ba ka sona A.m da gaske ba ka sona kake yi min abubuwa irin na wacce ake so?"
Ƙara masowa ya yi kusa da ita."Yes ni fa ban taɓa jin ina son ki ba,kawai ina girmama lamarin ki kamar yadda na sha gaya miki.Saunawa kike son na gaya miki ba na sonki ko kafin na aure ki na faɗa miki,Zainab ita ce macen da nake so kuma na aure ki da sanin ki akan ki haifa min yaro na bata.Wai mai ya sa kike dawo da hannun agogo baya ne?"
Ya faɗa cikin ɗaga murya duk da babu mutane sosai a gurin sai ɗaya biyu,amma har an fara taruwa ganin ya na magana da ƙarfi.
"Ina sonka ba zan fasa sonka ba!Na fara sonka tun kafin ka bijiro mini da aurenka, kuma na san kai ma ka na sona sau nawa kasha faÉ—a mini ka na son surar jikina da halina,mai ya sa ba za ka so zuciyata ba?"
Ta faÉ—a cikin muryar da tafi nasa amo don ji take kamar za ta yi hauka.
"Ni fa ban taɓa ce wa ina sonki ba sai surar jikinki,kuma ta ya ya zan yi na saka son macen da na san ban ba mu dace ba.Ki tuna mahaifinki har ya mutu bai bar muku komai ba,sanin kan ki ne mahaifina ya yi fice a duniya."
A.m ya faÉ—a ran sa na suya ganin ta na son ta tara mutane, wannan kamar cin mutunci ne mai ya sa ba ta gaya masa a gida ba.
Cikin jin zafin ta ya fara tafiya zuwa motar shi, da gudu ta bishi ta durƙusa a gaban sa ta na hawaye."Tabbas haka ne ka faɗi gaskiya mahaifina bai bar mana komai ba sai talauci,amma ka sani ba kuɗi ba ne kawai Allah yake sawa a so mutum shi ya sa har yanzu na kasa gasganta son Zainab kake yi.
Saboda ka na sonta ne don kawai ita ajin ka ce na san watarana za ka fahinci gaskiya, za ka gane a kwai baiwar da Allah ya kan yi ma bayin sa aso su ba wai sai dukiya ba.
Ni na san watarana za ka soni kuma sai ka yi nadamar abin da ka gaya mini ko ina raye ko ba ni raye."
Ta numfasa ta na jan numfashi ganin ya yi shiru ya na kallonta sai ta É—ora da ce wa."Ina sonka ba zan fasa sonka ba sai ranar da numfashina ya yi bankwana da gangar jikina."
Tafiya ya fara yi bai ce mata komai ba.Kamar wata zararriiya ta miƙe ta juya ta na kallon shi ta kira sunan shi.
"Ina sonka! Ina sonka!! Ina sonka!!!"
Cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya na jin kukan ta na yi mishi zafi sai ya ƙara sauri ya shige motar sa ya fice daga harabar makarantar a guje.
Durƙushewa ta yi a gurin tare da saka razanannen kuka.
Da sauri Hauwa ta fito ganin motar sa ta ɓace tare da kama ta ta na son ta miƙar da ita.
Faɗawa jikinta cikin muryar kuka da sheshsheƙa.
" Ki taimake ni A.m ba ya sona ya tsane ni na tabbata son shi zai kashe ni domin na fi buƙatar na mutu fiye da ina kallon ya na fifita wata a kaina.Wayyo Allah na!Ina ma a ce mutuwa na yi ban haɗu da shi a cikin rayuwata ba."
Hauwa ta ruÉ—e ganin kukan da take ba na wasa ba duk da guy É—in ya cancanki a so shi,amma ita a ganin ta bai kamata ta so shi haka ba ganin za ta cutar da rayuwarta a banza.
Da ƙyar ta ja ta suka bar gurin domin su kaucewa mutanen da suka fara taruwa.
Ruwa ta miƙa mata wanda ta karɓa tare da ɓalle murfin,ba ta ije gorar ba sai da ta shanye duka.
"Ki yi haƙuri ban baki shawarar ki faɗa masa ba don ya wulaƙanta ki,da ace na san abin da zai faru kenan da ban ce ki gaya masa ba.Kici gaba da addu'a babu abin da ya gagari Allah.Amma da kin bari ki samu ciki wataƙila ta nan kawai za mu ci galaba a kan sa."
"In har A.m bai amince da soyayyata ba ni kuma ba zan yadda na samu ciki da shi ba, na gwammace na yi ta rayuwa da shi a haka da na haihu da shi ya gujeni."
Abin da ta faÉ—i kenan cikin murya kaukausa ta É—auki jakarta ta tafi.
Tun daga ranar A.m ya ɗauke mata fuska wanda sai da ta yi mishi kuka,sannan ta ba shi haƙuri ta janye maganar so a tsakanin su sannan suka shirya.
*****
Zainab ta yi kuÉ—i na ban mamaki mace ce mai aji wadda take son ta zama babbar mace a kan komai.
Ta na da kuÉ—i da aji da ilmi ta na jin ta a cikin manyan mata masu amsa sunan su.
Ita kanta ba za ta iya irga iya dukiyar da take da shi ba.A yanzu sam ba ta yawan zuwa aiki domin ta zamo babba, a asibitin da take aiki ba ta wani zuwa sai dai in za ayi aiki tazo ta farÉ—e ta É—inke.
Zainab ta na da matuƙar ƙoƙari a gurin aikin ta shi ya sa kullum take ƙara samun ɗaukaka ta ko ina.
Irin kuɗin da take samu ta zama babbar mace yar lukuta duk da ba ta son ta yi ƙiba, aikuwa saboda kuɗi ya zauna ta cika ta batse tamkar za ta fashe,ta yi wani irin kyau sosai abin ka da farar mace alkyarbar mata.
Duk yadda A.m ya so ya kafa mata doka dole ya watsar da makaman sa ya ɗauki ƙaddarar sa,bayan ya fahimci matar sa mai aji ce kuma mafi ɗaukaka a cikin matan duniya saboda tarin ilmin da Allah ya yi mata.
Saboda ƙarin girmar da ta samu haka ya rage zuwa aiki da take yi,sai dai in yawon ta ya tashi ta fice, sai hakan ya ƙi ba A.m damar kasancewa da amaryar wucin gadi kullum su na tare da Zainab, in dai ba fita ta yi ba wanda kwana biyu ta rage yawo.
Rashin fitar ta sai ya takura su duka musaman A.m da kwana biyu ba su haÉ—uwa sai a waya.
Saboda ƙwarewar Zainab mahaifinta ya yi mata alƙawarin gina mata asibiti na ta mallaki wanda har an fara aikin gini.
Wata tafiyar ta kama A.m a kan kampani da suke ƙoƙarin buɗewa na sarrafa fata,Daddy ya ɗora A.m akan kayan da za ayi amfani da su.
A.m ya shirya viza tare da Juwairiya domin ya yi matuƙar kewarta,ba tare da ta sa ni ba sannan ya na son a duba lafiyarta don ya matsu da ta samu ciki su rabu.
Zuciyar sa ta kan buga daram! A duk lokacin da ya tuna zai rabu da ita,saboda ya shaƙu da ita sosai sai dai ya san dole watarana za su rabu.
A.m da yake ta tunanin hanyar da zai bi ya samu ya tafi da ita,amma ya rasa ko da ya yi musu viza bai sanar da ita ba.
Ranar talata ya kirata bayan ya gaya mata za su tafi sai hankalinta ya tashi matuƙa,don ita ba ƙaryar da ya ce ta yi ba ne yake tada mata da hankali.
Tunanin ta yadda za ta bayyana masa abin da ke faruwa ne,saboda ta san muddin ta gaya masa sai ya kaita kushewarta,ganin yadda A.m yake nuna mata tsantsar damuwar sa akan rashin samun cikin ta.
Kamar yadda A.m ya gaya mata akan ta yi ƙaryar Mama ba lafiya, ta yadda zasu samu su tafi,haka kuwa aka yi bayan ta shirya kayan ta akan za ta je ta yi sati biyu saboda ta yi jinyar Mama.
A jirgi hankalinta ya yashi ƙwarai ta ƙanƙame shi cikin tsananin tsoro ta na jin kamar numfashinta zai ɗauke,kasancewar ta na tsoron hawa jirgi sosai ko lokacin da ta raka Mama haka ta din ga ƙauyanci.
A.m kuwa sai dariya yake mata ya ciro wayarsa ya na musu bidiyo, ganin yadda ta tsorata ta na ƙauyanci,sam bai damu da kallon su da ake yi ba.
Juwairiya ta shiga cikin sabuwar duniya ta din ga zuba ido ta na ƙauyanci,yayin da zuciyarta take yabawa da ƙasar.
Bayan sun sha baccin gajiya ita kuwa sai da ta yi ɗan zazzaɓi, shi ya riga ta tashi ya na ƙoƙarin cire kayan jikin sa ya shiga bayi don ya watsa ruwa.
Kallonta ya yi ganin ta tashi suka zuba ma junan su ido,na tsawon lokaci can kuma sai suka kwashe da dariya.
Hannu ya miƙa mata ya na faɗin."Matar wucin gadi zo mu je ki taya ni wanka."
Dariya ta yi tare da noƙe kafaɗarta ta miƙe za ta fita daga ɗakin, ganin ya taho zai kamata kan dole sai ta taya shi wankan.
" Don Allah ka cika ni kunya nake ji."
Ta faɗa ta na ɓoye fuskarta da murya na son jan hankalinsa,shi kan sa bai yi tunanin ta na da irin wannan muryar ba,saboda cikin salo da jan hankali ta furta har da ɗan yi mishi fari.
" Kin san Allah dole yau sai kin taya ni wanka ko da kuwa muryar ƴar baby za ki yi don na gaji matuƙa."
Hannunta ya kama ya na son ya ja ta zuwa bayi amma ta ƙi cikin salo take magana da muryar kuka akan ya ƙyaleta.
Ganin za ta ɓata mishi lokaci cak ya ɗauke ta bai direta ko ina ba,sai cikin bayin ya tsunduma cikin ruwan da ta ji sanyin shi matuƙa.
Saboda tsaɓar shagwaba kuka ta saka mishi da gaske,wanda hakan ya bashi dariya ya watsa mata ruwa a fuskarta.
"Sarkin kuka dama mai hali baya fasa halin sa na manta fa matar wucin gadi ƴar ƙauye ce sam ba ta san soyayyar turawa.Allah sarki Zainab sai na tuna lokacin da muka zo cin amarcinmu mun yi soyayya sosai saboda ita mai aji ce."