← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 86

Sashe 62

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Lamarin mata haƙuri ake yi sai haƙur in ka ce dukan mace zaka din ga yi,to ya zaka yi duk ranar da ka haɗa mata uku ko huɗu?"

" Allah ya kyauta ya kuma tsare ni da tara mata uku,ko ita Juwairiya rabuwa da ita zan yi,zuciyata ba ta son wata Æ´a mace sai Zainab."Dariya A.m ya yi suka fice.

Daddy ya yi faÉ—a kamar zai ari baki yana ta huci ji yake kamar ya rufe shi da duka.
"Saboda baka da hankali sai ka kama mace da duka goto-goto da kai.To wallahi maza ka je ka dawo da Zainab in ba haka ba za ka fuskanci fushina mai tsanani.Kuma duk ranar da ka ƙara dukan musu ƴar mutane wallahi sai na ɓata maka rai."

A.m ya yi shiru yanzu yake tsananin dana sani da ya duke ta.
Ko da ya shiga shashin mahaifiyar sa ranta ya ɓace matuƙa ta yi mishi tatas!Akan ya je ya dawo da Zainab.A.k yake ta bada haƙuri.

Daddy ya yi mishi faɗa sosai ya ƙara masa da hadisan monzon Allah da nasiha,sannan ya ba shi umurnin ya je ya dawo da ita.

Miƙewa suka yi kai tsaye gidan su Zainab suka nufa.A.m gabansa na ta faɗuwa don ya san ba za su kwashe ta daidai ba.

Jefi-jefi yana kallon hanya yana jin matsanancin ɓacin rai,in ya tuna da Juwairiya sai ya ja tsaki da ƙarfi ya kauda kan sa,daga ƙarshe ya ɗauki laifin komai ya ɗora akan Zainab don ita ta bada ƙofa har ta shigo rayuwar su.

Maigadi ya wangale ƙofa da alamun wani zai fita daga cikin gidan don ko hon ba su yi ba,Daddy Zainab ya fito da shiri makullin mota riƙe a hannun sa zai fita,ganin su ya sa ya tsaya yana musu wani irin wulaƙantaccen kallo.

Ya rantse da ace A.m ba É—an amininsa ba ne yau kotu za ta raba su da shi,tun da har ya iya dukan masa Æ´a guda tsoka É—aya a miya.

" Mara mutunci uban mai ya kawo ka gidana ko ka zo ka ƙara dukanta a gabana ne? Ashe dama ba ka da mutunci na ɗauki abu mafi soyuwa na ba ka?"

Masifa yake musu bai bari sun shiga daga ciki ba ya shiga zagin su har da A.k da ya yi rakiyan,sai da ya samu na shi kason saboda mahaifin Zainab ya yi fushi,bakinsa har kumfa yake saboda an bugi shalele.

A.k haƙuri yake badawa har da duƙawa ya kuma janyo hannun A.m,don ya duƙa da ya yi ƙikam ya na tsaye,zuciyar sa na tafarfasa jin rashin mutuncin da yake musu,a gaban ƴan aikin gidan.

Da ƙyar ya basu izinin shiga cikin falon baƙi suka zauna kusan awa babu wanda ya bi ta kan su.

Tsalam mahaifiyar Zainab ta shigo cikin falon tana kallon A.m a wulaƙance.

" Sannu isashshe da za ka kama min Æ´ata da duka,an ce maka jaka na aura maka? Na rantse Zainab ba za ta dawo gidan ka ba,tun da ba ka da mutunci.
Mai take amfana da shi da auren ka sai tsiya da haƙuri na rashin haihuwa da ba ka yi,shine saboda kai mara mutunci ne za ka kama min ita da duka akan wata banza ƴar aiki,to wallahi ba ka isa ba don ba za ta dawo gidan ka ba.
Shekarar ku nawa da aure ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba,dole ka sakin mini ƴata ko kutu ta raba mu."Ta faɗi tana harare-harare.

Duk irin rarrashin da A.k ya yi musu amma sun kafe kan ba za ta koma gidan sa ba,sai nanata maganar haƙurin da take yi saboda rashi haihuwar da baya yi.

Cikin fushi A.m ya miƙe yayin da idanun sa suka kaɗa suka yi jajur.
Ya buɗe baki zai yi magana da sauri A.m ya kama shi suka fice waje.Hannun sa ya ja zuwa mota ba tare da ya ce komai ba,ya shiga motar suka fara tafiya.Ganin yadda yake huci sai ya kunna ƙira'ar alkur'ani.

Suna tafe babu wanda ya yi magana sai zuwa can A.k ya kalli A.m ya ci gaba da tuƙi.Jingina kan shi da kujera tare da lumshe idanun sa.

A lokacin da A.k ya shigo cikin falon A.m riƙe baki ya yi cikin tashin hankali yana kallon yadda falon ya hargitse babu mamora a falon

" Taɓ sai ka tanadar mata wasu ka ije saboda duk ranar da ta san da igiyar auren ka da Juwairiya,wallahi in babu kayan da za ta fasa sai dai wani Abdurrahman ba kai ba,lallai Zainab na da zafin kishi."Ya faɗa cikin tsigar mamaki da tsokana.

A.m da ran sa a ɓace ya kalle sa da takaici ya ce." Fata ma kake min ko so kake na rasa wani shashin na jikina,ni kaina yau na ƙara tsorata da lamarin ta,dole na ɗauki mataki kafin ta san da wannan zancan in dai ba so kake na koma tafiya da ƙafa ɗaya ba."

Dariya A.k ya yi sosai ya ce." Wannan ya rage naka ni dai babu ruwana tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka,kuma wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho."

A.m ya matsa kusa da shi ya gallah masa harara."Ni ba wannan ba yanzu ya zamu yi da waɗannan marasa mutuncin gaskiya bazan iya zama ni kaɗai a cikin gidan nan ba,ni da nake da zuƙa zuƙan ƴan mata biyu yanzu na koma babu ko ɗaya.Gashi yaunwa make ji wunin yau ko ruwa ban saka a bakina,saboda matsalar da damuwata ta saka ni."

" Ya rage naka sai ka san in da zaka je kaci abinci amma ba'a gidana ba,don matata ba kukun ka ba ne,ko da ka ga ada ina baka abinci saboda babu wanda zai baka ne,amma yanzu tun da a kwai Juwairiya sai ka je ka yi biko."Tsaki ya saki take fuskar sa ta canza.

" Na rantse har yanzu ina kan bakana sai na hukunta ta za ta san da wane irin namiji take zama,da na je na kirata gara na kwana banci abinci ba."Ya ce da A.k da ya É—auki makullin motar sa.

" Ok fine ya rage naka da na yi tunanin za ka yi bikon matar wucin gadi,ka huta kafin matar so ta dawo,saboda iyayenta sun yi fushi sosai kuma dole sai ka danne zuciyar ka akan duk abin da iyayenta za su yi maka,Æ´ar su kake aure kuma kai ka dakar musu Æ´a."

" Na ji don Alkah ka tafi babu abin da kake yi sai ƙara tafarfasa min zuciya,da na so na gaya ma mahaifiyarta magana amma kuma na gode da ka hana ni da na yi katoɓara."

" Ok bari na tafi tun da ba za ka dawo da matar wucin gadi ba,sai ka ci gaba da cin abincin Lantana,sannan kar ka yi gigin zuwan min gida mai mata biyu ya zama gwauro."

Ya ce yayin da A.m ya fito don ya raka shi ba tare da ya bashi amsar shaƙiyancin da yake mishi ba.

Ya shiga cikin mota ya zauna tare da riƙe sitiyarin ya kalli A.m da yake riƙe da murfin motar yana jiran ya shiga,ya rufe mishi ƙofar motan.

" Ya kamata ka yi tunani A.m lokaci yana wucewa lamura canzawa,suke yi ka sanar da iyayen Zainab komai ka bayyana Juwairiya a matsayin matar k,tun kafin lamura su kwaɓe maka.Na tabbata da kai ne ba ka haihuwa Zainab ba za ta zauna da kai ba."

Rufe mishi motar ya yi ganin ya shigar da ƙafafunsa ciki,saboda fahimta da ya yi maganar da yake masa ba ta tasiri a zuciyar sa.

" Na riga na yi wa Zainab alƙawari ina sonta ba zan iya haɗata da wata ƴa mace ba.Na san cewa Juwairiya na sona sai dai ba ta san irin namijin da ya kamata ta so ba,duba ga ni ba ajin aurenta ba ne kuma babban goro ai sai magogin ƙarfe!Don haka ina kan baka na."

A.k ya ja motar sa ya fice ba tare da ya ƙara ce masa komai ba.

Zainab zaune a ɗaki ita da ƙawarta Nabila suna hira,wacce ta yi takakkiya ta taho Zariya tun daga Abuja,saboda kiranta da ta yi tana kuka ta gaya mata abin da ya faru.

Nabila da ta gaji ta É—auko gajiyar hanya tana zaune akan gadon Zainab abinci take ci.

Wayar Zainab ta yi ƙara kusan sau goma na kiran ta,amma sai taƙi ɗaga wayar daga ƙarshe kashe wayar ta yi ta wurgata can gefe a fili ta furta.
" Maye kawai mazinaci."

Ko da ba ta gaya mata ba ta san wanda yake kiranta.

" Yanzu kin tabbata abin da na ke gaya miki ko kin yadda namiji buhun ƙaya ne? Wai ki gaya min ta ya akai kika gane suna cin amanarki?"

Zainab ta saki tsaki ta kalle ta da ɓacin rai ta ce." Ni ba wannan ba ina acid ɗin da nace ki taho min da shi?"

" Karki damu tsaƙon ki yana ije a jakata amma don Allah ki gaya mini,ya akai kika gane bayan duk kin ɗana musu tarko sun tsallake?"

"Wani magani na tsinta a cikin drower ta A.m ya na sha na É—aukar ciki da wuri."

Ta ce cikin damuwa yayin da idanunta suka kawo ruwa.

" In yana shan maganin haihuwa to meye hujjarki ko kina tunanin,A.m zai so ya haifi É—ansa ta zina bayan ga matar sa ta sunna?Sannan ni ban ga abin da kika faÉ—a a matsayin shedar suna cin amanar ki ba."

Ta faɗa da tana kallon Zainab da ta yi tsuru-tsuru ta manta cewar,ba ta taɓa gaya ma kowa ba cewar ita ce ba ta haihuwa,sai ta shiga in da in da daga ƙarshe hannunta ta kama tare da fashewa da kuka cikin kuka ta ce

" Yau zan gaya miki wani sirri amma don Allah ko sauran ƙawayen, ba na son ki gaya musu cewar na gaya miki ni ce bana haihuwa ba A.m ba,domin ya yi min alƙawarin ba zai faɗa wa kowa ba kuma ba zai ƙara aure ba."

Gwalalo idanu ta yi cikin mamaki jin abin da ta faÉ—i da gaske ita ce ba ta haihuwa ba A.m ba.
Chapter 62 · 0% Book details