← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 86

Sashe 80

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 35*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Zainab zaune a cikin ɗakinta riƙe da wayarta,hawaye ne ke sintiri a fuskarta da ta jiƙe sharkab da hawaye.A ranta tana jin wani irin tsananin baƙin ciki da tashin hankali mai tsanani,duk sadda ta tuna abin da ya faru tsakaninta da A m,wanda har yau ta kasa yarda wai a zahirin gaskiya lamarin ke faruwa.

" Wayyo Allahna! Da gaske A.m ka guje ni saboda wata ƴa mace marar gata a duniya,da gaske jikinka da na ke kishinsa ka mallaka wa wata mace wulaƙantacciya.Me ya sa ka yi mini haka bayan ka yi mini alƙawarin ba za ka taɓa haɗa jikinka da wata ƴa mace ba?"

Sai ruwan hawaye suka ci gaba da turereniya a fuskarta tana jin tsantsar baƙin ciki da kishin Juwairiya a zuciyarta.

Ƙaran tsaƙo da ya shigo a cikin wayarta ya saka ta yi tsaki tare da jefar da wayar,wanda ta san A.m ne ya yi,don kusan a rana sai ya yi mata sun fi goma,amma ba ta taɓa gigin buɗe wa ba.Da wayar a kashe take barin ta sai yanzu da ta ji zuciyarta ta ɗan rage zafi ta kunna ta.

" Ba zan ɗaga wayarka ba macuci azzalumi mayaudari! Ka mai da ni shashasha ka sa ina ta iyayi a cikin ƙawayena mijina ba ruwan shi da mata,ni ce mace kaɗai birnin zuciyarsa a she banza ka mai da ni rainin wayonka ya fi na kowa,yanzu da wace fuskar kake son na kalli ƙawayena suna faɗa musu?Haba ai gara a ce mutuwata na sanar musu."

Sai kuma ta miƙe kamar wata zararriya ta ƙara cewa bayan ta fisge ɗan kwalin kanta ta ya mutsa gashinta da ke ɗaure tare da cilli da ribon ɗin.

"Mai ya sa na rayu don na ga ranar da A.m ya yi wa wata ciki bayan ni ba na haihuwa?"

Kamar wata zararriya sai kuma ta ɗauki wayarta da sauri tare da ƙoƙarin ɓuɗe saƙon da ya yi mata.

" Na rantse sai na koyar da ku hankali sai na shayar da ku ruwan baƙin ciki saboda girman zunubin da kuka aikata mini."
Ta ce sannan ta fara karanta tsaƙon cike da jimami da tashin hankali bayyane a fuskarta.

(Zainab don Allah ki tsaya ki fahimce ni tabbas na san ban yi miki adalci ba,amma in kika fahimce ni za ki gane na yin wannan auren ne saboda ke."Kalar saƙonnin da ya turo mata ranar farko kenan.)

Wata uwar ashar ta danna masa sannan ta buÉ—e na gaba.

(I dan son Juwairiya nake yi ta ya ya za yi na ije ta a gidanki a matsayin mai aikin gidanki,haba ya kamata ki gane na yi hakanne duk saboda ke.Kin san irin yadda nake son yara .Kin ji na rantse miki da zarar ta haihu zan saketa kuma na ba ki yaron da ta haifa, ta fita daga rayuwarmu domin an halicci rayuwata da ke kaÉ—ai.)

Ire iren saƙonnin da yake yi mata kenan waɗanda ba ta dubi zuwa gare su,sai yau ta fara dubawa domin ta gaji da zama ita kaɗai zuciya da gangar jiki sun yi rashin sa,da zarar ta yi shiru muryarsa take mata amsa kuwwa ma kunnenta.

" Ka cuce ni!Da na yanke rabuwa zan yi dakai sai dai na lura ba zan iya yin haka ba,domin kai ne namiji na farko wanda na ji zan iya mutuwa akan sa,amma mai ya sa ka zaɓi ka cutar da ni bayana ka san ina son ka matuƙ...."
" Mijin na ki za ki yi fushi ki bar ma wata! Lallai ba ki da hankali."

Momi da take tsaye ta harɗe hannunta a ƙirji tana jin abin da take cewa,ta tambayeta da mamaki a fuskarta.

"Momi ya kike son na yi A.m ya cuce ni bazan iya yafe masa ba."

Rungumeta ta yi tana rarrashi ta ce." Na yi magana da Hajiya rabi gobe za ku je in da na gaya miki s..."

" No Momi na gaya miki ba zan ɓata aurena da wannan ba in har ba za ki taimaka mini,ta wata hanyar ba to ni zan koma ɗakina na rantse sai na ga bayanta,da kaina zan ɗauki mummunar mataki a kanta.Ita da abin da ke cikin zan bankawa wuta duk su ƙon..."

" Rufe mini baki banza kawai shashasha! Ana nuna miki hanya ki na kaucewa ki je ki yi duk abin da kika ga dama,ai dama da za ki aikata ba ki nemi shawarata ba,wai ke daÉ—i miji ai gayi nan in da ya kaiki,duk abin da kika ga dama ki je ki yi,amma ina tuna miki mundin kika salwantar mi shi da ciki ba zai barki ba.Ita yarinyar kin san ta yadda suka yi har ya aureta kasancewar ta Æ´ar matsiyata."

Fuuuu! Ta fice daga É—akin ranta na zafi sosai saboda gani take ba ta da wayo,da ba zata bi hanyar da ta saka ta ba don ita ce kawai mafita a garesu.

Sai ta kife kan gado tana kuka domin duniyar ta yi mata zafi sosai.

Kusan sau uku yana kiran wayar ba ta É—auka ba,sai a na huÉ—u kamar an saka ta dole ta janyo wayar tare da kanga ta a kunninta.

" Munafiki mayaudari mai za ka ce mini na baro gidanka ba za ka bar zuciyata ta samu sausauci ba."Ta faɗa a zafafe da ɓacin rai.

Ya saki naunauyar ajiyan zuciya mai ƙarfi wace ta taɓa zuciyarta,ya rintse idanunsa yana jin zafin abin da ta ce mi shi,amma sai ya daure ya ce da murya sansanya.

"Zainab please don Allah kar ki kashe waya ki bari ki saurari abin da zan gaya miki don Allah!"

Tsaki ta yi ta yi shiru ba tare da ta tanka masa ba.

Ya cire wayar a kunninsa ya kalli wayar don a tuninsa ta katse wayar,amma sai ya ga ba ta yanke ba,sai ya fara magana da muryar da ya san yana kashe mata zuciya,yake kuma narkar da bargon soyayyarsa ya zagaye duk wata kafa da take jikinta har ta kasa gane girmar laifin da ya yi mata.

" Kin san Allah ya jarabce ni da son yara ko?Sannan ki duba irin tarin dukiyar da nake da shi,amma ba ni da magaji Zey ba kya tausayin rayuwata,ke kan ki ina za ki kai ɗumbin dukiyar da kike da shi?Sannan in muka mutu ba mu da wanda zai rinƙa yi mana addu'a,duniya za ta manta da mu."

Ya numfasa ko za ta ce wani abu amma sai ya ji ta yi shiru don ji take kamar ta shaƙe shi ta wayar.

Wannan dalilin ya sa na ga da in ce miki mu yi adopting yaro a gidam marayu, na ga dacewar kawai na auri mace na siyi É—an da za ta haifa."

Shiru ta yi bayan ta ji duk abin da ya ce zuciyarta ta kasa yadda da lamarin da ya faÉ—a,ba rashin son É—a da ba ta yi bane ya dameta don ba za ta iya wahala da shi ba,amma kuma wannan ba matsala ba ce saboda za ta iya É—aukar mai aiki ta kula da rayuwarsa,to amma ita Juwairiyar za ta iya É—auke idanunta daga gareshi."

Abin da take ta tunani kenan a cikin zuciyarta, sannan kuma mai ya sa bai gaya mata ba tun lokacin,sai kawai ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi.

Kamar ya san abin da ke zuciyarta ya ce." Na ƙi gaya miki ne don ba lallal ba ne ki amince,sannan kuma idanuna sun rufe sosai ina son na ga yarona a haɗa sunana da na sa,idan kika san Juwairiya matsayin matata ba za mu taɓa samun zaman lafiya,ga shi rashin faɗa miki bai yi amfani ba saboda na so ace cikin ƙarya kika yi lokacin da ta samu ciki,sai mu yi ƙaryar ciki har ta haihu."

Jikinta ya ƙara yin sanyi matuƙa kamar wacce ta fito da ga firjin.

" Haba dama na san A.m ba zai taɓa cin amanata ba sai yana da dalili ga shi yanzu baƙin kishina ya saka na je na tona asiri,da yaron ni zan ce na haife shi."Ta ce take wani irin mugun nadama ya shigeta ganin yadda ta kwafsa gefe guda kuma sai ta ba shi laifin ƙin gaya mata da ya yi.

" Ki yi haƙuri ki dawo gareni ji nake kamar zan mutu na yi rashin waɗannan hot kis na ki masu zafi da sanyaya zuciya,yanzu aikina ya ƙare da ita ko kallonta ba zan ƙara ko kallonta ba ke kaɗai ce matata."Ya ce mata da salon muryar shi da yake rikita ta.

" Na ji zan dawo duk da ka zubar da ƙimata a idanun duniya amma ta zauna a gidanku har ta haihu in ya so sai a bani yaron ita ta tafi."

Gaban sa ne ya faÉ—i ras!Amma kuma ba zai iya gaya mata gaskiya ba,gara in ta dawo sa fuskanci wannnan matsalar.

" Ba ki da matsala na zo na É—auke ki?"Ya ce zuciyar sa da fargaba.

" Ba yau ba."

Ɗif ta kashe wayar tana jin haushin sa matuƙar gaske domin ya zubar mata da ƙima a gurin mutane.

A.m ya riƙe waya yana kallonta sororo har yanzu zuciyarsa bugawa take yi,ya san in ta dawo ta ga Juwairiya a kwai dirama,balle ta ga yadda ta koma ta yi wani irin kyau komai na jikinta ya buɗe shi kan sa baya iya ɗauke idanunsa a kanta.

Mai da wayar ya yi cikin aljihunsa ya fesa turaren da ya zamar masa dole,tun ba ya son ƙamshin har ya fara so don babu yadda zai yi,sai ya fara saukowa ƙasa zuciyarsa na ta ɗar ɗar

" A.m!"

Ta kira sunan shi da ƙarfi kuma cikin isa da gadara ba tare da ko ɗan girmamawa ba,ganin yana son ya fita bai kalle ta ba,duk da ya ganta a falon.

Wani irin kallo ya yi mata ganin yadda ta zauna a falon riga daban zani daban sai hular sanyinsa wacce ya ba ta saboda jin sanyi da take yi,tana riƙe da remote a hannunta fuskarta cike da tsiwa,ga kayan ciye-ciye nan a gabanta da ta gama da wannan ta janyo wannan.
Chapter 80 · 0% Book details