← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 86

Sashe 19

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanan ta uku a gurin ranar da Hajiya binta ta shigo ta buƙaci a saki Juwairiya taga sarƙarta,duk da cewa ƙazafi aka yi mata amma ko haƙuri basu bata ba.Ita dai da gudu ta dawo gida tasan yaran Hajiya Binta suka ƙulla mata wannan ƙullalliyar amma Allah ya fisu kuma addu'a takobin mumini.

Ƙarin tashin hankali da ta zo Mama ba ta a gida Ibrahim ne yake sanar da ita ciwon Mama,wani kukan ta saka ta fita zuwa gidan su Mariya domin Mariya bata gaya mata Mama ba lafiya ba.

Yadda ta ga Mama hankalinta ya tashi ƙwarai rungume Mama ta yi ta na kuka sosai.Mama ce ta buɗe ido jin muryar Juwairiya hankalinta ya ɗan kwanta ganin ta fito,don ba ta san halin da take ciki ba shi ya sa jikinta yake rikicewa.

Likita ne ya shigo ya miƙa ma Mariya takadda yace."Gashi ki siyo wannan maganin ya kamata ku din ga kwantar mata da hankali, domin ta na da hawan jini ga ciwon zuciya, matuƙar ana ɓata mata rai to watarana zuciyar za ta buga!"
Wani ƙarin tashin hankali Juwairiya ta shiga jin Mama na da waɗannan ciwuka rungumeta ta yi tana kuka."Mama kema mutuwa za kiyi?Don Allah karki mutu ki barni!Rayuwata za ta shiga cikin garari.Allah na gode maka ka bani ikon cin jarrabawa,amma karka ɗauke min mahaifiyata ka barni da azzalimi."

Mariya ta kama ta ta rungume ta na buga bayanta hawaye ya na kwaranya a fuskarta tsananin tausayi ya cika mata zuciya ganin halin da take ciki."Kin ga ni Mama za ta barni ko!Wai me ya sa rayuwata tazo a baƙin jadawali ne?Nake kurɓar ruwan bakin ciki mafi zafi da ƙuna a zuciya."Tace cikin kuka." A'a Juwairiya karki faɗi haka!Kada ki kasa cinye jarrabawarki kin san Allah ya na jarraba mutum dai-dai imaninsa.Kar zuciya ta sa ki yi saɓo.Ina ji a jikina zaki ji daɗi a rayuwarki.Allah zai ba Mama lafiya."Ta gaya mata ta na shafa bayanta.

Daƙyar Juwairiya ta daina kuka sai ajiyar zuciya hannun Mama ta kama ta riƙe ta na kallonta.Duk wani hidima na asibitin su Mariya da mahaifinta suka yi har kuka ta yi ta na gode musu domin Allah ne zai biya su.

Bayan Mama ta samu sauƙi aka sallame su akan Mama za ta din ga zuwa ganin likita ta na karɓar magani,hankalin Juwairiya ya tashi ta na tunanin ina za ta din ga samun kuɗin da Mama za ta din ga zuwa ganin likita.

Kan dole ta ƙara saka Mariya ta nema mata wani aikin don sana'ar da suke yi sun cinye tsugune kawai suke,da fari Mama taƙi yadda ta ƙara yin wani aikin amma daga ƙarshe dole ta haƙura ganin yunwa na so ta yi musu tabo.

Kwasam ta haɗu da wani matashin saurayi mai suna Mas'ud Allah ya jarabci Juwairiya da son shi yaro ɗan gata da sanyin rai ga kyautatawa.Shigowarsa rayuwarsu ya sa sun samu canji sosai,duk da ya ga ita yar talaka ce amma be saka yaƙi sonta ba don da Allah yake sonta.Mas'ud ya na temaka musu sosai ya na aiki a Jami'ar Ahamdu Bello a library kuma ɗan samaru ne iyayen sa sun rasu sun bar mishi dukiya sosai,sannan ɗan kasuwa ne.

Juwairiya ba ta taɓa jin ta na son mutum ba sai akan sa, gabaki ɗaya ta ji ta na son ta aure shi sai dai tasan hakan ba me yiyuwa bane,don babu yadda za'ai Baba Sani ya barta ta aure shi sai dai akan yadda take jin sonsa, za ta iya fito na fito a tsakanin su ko gidan me unguwa za ta iya kai shi.

Haba tunna ya ga ya na zuwa gurinta ya saka tashin hankali yayin da shi ma Mas'ud ya kafe,ganin shi ma É—an zamani ne sai yace bai tashi uren Juwairiya ba don bashi da kuÉ—i,nan take yace mishi kar ya damu ya amince zai yi mata komai.

Ranar da Mas'ud ya kira Juwairiya ya gaya mata Baba Sani ya amince da auren su har ya ba shi izini ya turo magabatansa,kawai jin sa Juwairiya ta yi amma ba ta yadda da abin da yace mata ba.Ganin haka sai ya ƙyaleta kawai in ta ga zahiri ta yadda.
Da misalin huÉ—u da kwata É—an Baba Sani ya yi sallama ya shigo ya yi kiran Juwairiya taje shashin Baba Sani ya na kiranta a É—akin matarsa.

Gabanta ya faɗi amma sai ta saka hijabinta ta nufi ɗakin ganin a kwai baƙi ya sa ta ji a ranta a kwai abin da ke faruwa sai ta tsaya daga kofa ta na sallama."Yauwa Juwairiya shigo."

Baba Sani ya faÉ—a da murya sanyaya a hankali ta yaye labulen ta shigo tare da tsaya daga nesa ta na kallon mutane jikinta ya bata dangin Mas'ud ne.

Miƙo mata alkur'ani ya yi tare da canza fuska kalar tausayi yace." Dangin yaron nan Mas'ud suka zo neman auren ki,amma ni bazan cuce su ba sun yi min tambayar kina da tarbiya nace gara suji a bakin ki, don nasan ke ƴar mace ce sannan kin yi yawon aiki gidajen masu kuɗi,duk mazan gidan sun sanki a matsayin ƴa mace ga abin kunya na satar da kika yi,har aka kulle amma ga kur'ani ki rantse musu hakan be faru ba "

Taɓ ji ta yi ƙasa ta gaza ɗaukarta ta ji wani irin hajijiya ya kamata." Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un."

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na goma sha ɗaya.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G0J8rS0cxTtCCC38iwA3B9*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA GOMA SHA ÆŠAYA*

Ganin taƙi karɓar kur'anin hawaye ya na zuba ƙuncinta ya yi murmushin mugunta,ya juyo ya na kallonsu sannan ya ƙara saka kuka har da hawaye share-share yace." Kun ga abin da na gaya muku ya zama gaskiya? A matsayina na ƙanin mahaifinta babu yadda ban yi da ita ba akan ta zama macen ƙwarai, amma taƙi jin maganata!"

Juwairiya da take cikin wani yanayi na tashin hankali mara misaltuwa,ta rintse idanunta ta na jin wani irin ƙaton abu ya taso daga ƙirjinta ya tokare mata kirji ya kuma ƙi wucewa.

Tana son ta ji saukar hawaye akan ƙuncinta ko ya rage mata raɗaɗin da zuciyarta take ciki.Kunnuwanta ba za ta iya jure jin kalamai da yake yi ba,ya na aibanta ta ita da mahaifiyarta.

Ta muzanta iya muzanta da ƙyar ta yi nasarar jan jikinta ta fita zuwa shashin su,ta bar shi da bayin Allah da suka yi zuru suna kallon shi,yanayin su bai nuna sun yadda da maganar da yake musu ko akasin haka.

Da gudu ta faɗa ɗakin tare da ƙanƙamre Mama ta na wani irin kuka." Mama duniya ta min zafi! Ina jin wani irin baƙin ciki a cikin zuciyata,wallahi nafi buƙatar mutuwa fiye da rayuwata! Wai me na yi wa Baba Sani ya tsane ni haka!Gara ya kashe ni da ɗacin da yake saka ma rayuwata."

Mama ta rungumeta ta na shafa bayan ta don gani take kamar hauka ta yi." Lafiyar ki É—aya kuwa?Ki yi shiru ki yi min bayanin yadda zan fahimta."

Kusan minti goma ta na kuka ganin ta kasa magana sai ajiyar zuciya take,a ranta ta na jin baƙin cikin rabuwa da masoyinta,don ta san yadda ya aibata ta babu yadda za'ai su yadda ɗan su ya aureta.

Da ƙyar Mama ta samu ta daina kukan sannan ta yi mata bayani.Ran Mama ya ɓace sosai ba ta san sanda ta ji jawaye ya na zuba a ƙuncin ta ba." Na gaji da halin da yake min! Zuciyata ta fara gajiya amma ba komai Allah ya fi shi da ikon Allah sai ya yi nadama,akan halin da yake miki."

Sosai Juwairiya take kuka koda Mas'ud iyayensa suka koma gida suka sanar mishi a abin da ya faru,hankalinsa ya tashi matuƙa duk ƙoƙarinsa na ya fahimtar da su,amma sun ƙi ƙarshe wan mahaifinsa ya gyara zama yace." Ko da a ce yarinyar ba halinta bane,to ƙanin mahaifinta ba ya son ya baka ita ka kyale musu yarinya ga ƴan'uwan ka nan sai ka zaɓa a cikin su."

Ransa ya ɓace matuƙa da ma ya ba shi izinin ya turo dangin sa saboda ya faɗa musu haka.
Motarsa ya É—auka sallama ya yi bai ko tsaya Mama ta amsa ba ya faÉ—a gidan,a yadda ta gan shi ta san ba shi cikin hayyacin sa.

Da sauri Juwairiya ta ruga da gudu don ta saka hijabi ganin ya shigo." Mama ya Baba Sani zai yi haka? Juwairiya ya aiba ta a gaban iyayena. Wai me kuka yi mi shi ya tsane ku?"Ya faÉ—a yayin da idanunsa suka kawo ruwa.

Cikin jimamin lamarin Mama ta share hawaye ta kalli Mas'ud da ya haɗa kansa da gwiya hawaye na zuba a fuskarsa,sai ya ba ta matuƙar tausayi ta san yadda yake son Juawairiya duk da iyayensa suna da shi amma a haka yake son ta.

Ka yi haƙuri ka san matar mutum kabarin sa Allah be nufi Juwairiya matar ka bace,ka bi zaɓin iyayen ka ni na san duk korar mata masoya da yake in har lokacin ta ya yi bai isa ya hana ba."

" Gaskiya Mama ba zan iya jure rashin Juwairiya ba zan je na sami Baba Sani duk abin da za'a yi sai dai ayi haka kawai ya din ga cusgunawa rayuwarku.Ya katse ta da faɗin hakan ransa a ɓace tare da miƙewa.

" Zo Mas'ud don Allah karka je a yadda ranka yake a ɓace za'ayi ɓatatta,ka san halin shi ba shi da haƙuri ni ce na haifi Juwairiya ina me baka haƙuri ka haƙura da ita,shi kaɗai ne wanda take gani a matsayin na ta in har aka ɓata mishi wa za ta riƙe?Ka yi haƙuri Allah be nufa za ka aure ta ba."
Chapter 19 · 0% Book details