← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 86

Sashe 64

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juwairiya riƙe da waya a hannunta suna kokuwa da Hauwa da ta rantse ba za ta kira shi ba.

" Hauwa ki taimake ni don Allah kada ki sa zuciyata ta fashe! Na san har yanzu A.m yana fushi da ni ne haƙurin zan ba shi."

Wani mugun kallo ta sakin mata ta ce." Wai ke ba ki da aji ne? Shi ya sa ya raina ki ya ke wulaƙantaki,Allah ya halicci mace da daraja mai girma a gurin ɗa namiji in kika ba shi lokaci da kan sa zai kira ki,don haka ba zan ba da wayata ba."

" Wayata tana gidan sa babu ta in da zai kira shi kuma na san cewa ba zai taɓa kirana ba,ko sau ɗaya ki bani na kira shi don Allah."

Ta faɗa tare da marairaice fuska hawaye a kan ƙuncinta.
" Bari na tura masa da tsaƙon haƙuri daga gareki in har yana buƙatar ya kira ki zai neme ki,amma ba zan bari ki kira shi ba nuna son da kike masa ya yi yawa shi yasa yake gasa miki gyaɗa a hannu.

Sai ta koma ta zauna ta zabga tagumi da kalar tausayi har hanzu hawaye na turereniya a fuskarata.

Yanayin da ta yi sai ya ba Hauwa dariya da takaici.

Wayar ta ɗauka ganin taƙi cin abincin da ta ije musu ta faɗa kogon tunani.

Tsaƙon haƙuri ta tura masa da basu wuce kalmomi biyar ba ta ije wayar.

A.m dake kwance a kan makeken gadon sa da yake jin faÉ—in sa ya kai faÉ—in duniya.Filo ya jawo ya rungume da tare da jan tsaki.

Tsananin ɓacin rai yake ɗauke da shi saboda ya ya je gidan su Zainab ta bar ƙasar.

Da ƙyar ya iya dawowa gida ya kwanta yana jin wani irin zafi a ran sa.Tun ranar da tsaƙon ban haƙuri ya shigo daga Juwairiya wanda yau kwana biyar da shigowa, bai ko karanta da kyau ba balle ya tura reply wani irin haushinta yake ji da yanzu ya fara irga ranakun da zai zama Daddy.

Wayar sa ta yi ringing har sau uku sai a na huÉ—un ya É—auka a kasalance ba tare da ya tanka ba.
" Ban yi tunanin za ka amsa kirana ba balle ka É—auka."Muryar Baba Sani ta daki kunnin sa.
Da hargowa ya ja tsaki da takaicin ƙin duba wayar da bai yi ba ya ɗauka,wanda hakan ya kasance ne saboda baya son ya kalli wayar lokacin da kiran ya shigo.

" Ban san kai ba ne da babu abin da zai saka na amsa wayar,mara mutunci mai ya sa ka kira wayata?"

" Na kan yi mamaki in ka yi min wannan tambayar Juwairiya da take gidan ka irin mangwaro ce ka samo ka shuka ta fito,da kake tambaya ta dalilin kiran ka."

Shiru A m ya yi masa a yanayin da yake baya buƙatar tashin hankalin Baba Sani don yana shakkun shi sosai.
" Na so na zo da kaina amma dana tuna baka da mutunci,kuma ka yi min gargaɗi sai na dana tsufana,gudun kar na mutu da ƙafa ɗaya sanin baka da mutunci,kuma sam baka girmama na gaba da kai.

"Fine gara da ka yi ma kanka ƙiyamullaini ƙaƙi zuwa in da nake da sai ka raina kan ka wallahi."A.m ya ce ran shi a ɓace.
" Ƴar ɗan'uwana na biyo naji ba'asi A k ya zo nemanta jiya."Gabansa ne ya faɗi ya yi shiru bai tanka ba,amma tsoro fal a zuciyar sa ya manta Mama ba ta gari,kwata-kwata bai yi tunanin in da za ta je ba,saboda haushin da ta ba shi ko tunanin halin da take ciki bai yi ba.

" Na ji ka yi shiru ne ko ka ɓatar mini da ita ka san fa ita ɗin dukiya ta ce,so ka kiyaye don wallahi zan iya shuka rashin mutuncin da baka taɓa tunanin in da shi ba."

" Har a kwai wani rashin mutuncin da za ka yi min da zai firgita ni bayan san baka da mutunci gabaki ɗaya rayuwarka,a tsiya za ka ƙare don baka gaji arzikiba garyar matsiyata."

Dariya Baba Sani ya saki jin abin da ya faÉ—a sai ya ba shi amsa da.

" Ashe masu arziki zasu zama matsiyata don in ka yi gigin ɓatar da ita saina zaman maka ƙadangaren baƙin tulu,don haka ka kula ba ni da mutunci kai ma sheda ne."

A.m da ran shi ya ƙara ɓaci matuka kaɗa kan sa ya yi sannan ya ba shi amsa" Kama ta ya yi na zo na kamaka in ji dalilin da ya sa take zubar min da ciki,don na san wataƙila kai kake saka ta kuma wallahi in har na gane da saka hannun ka sai na saka kaf zuriyarku an ɗaure ku."Ya ce da shi ciin ɗaga murya .

" To shikenan ɗan Ƙaruna ina jiran ka amma ƙila ni zan fara ɗaure ka,matuƙar ka salwantar min da ƴar ɗan'uwa kuma jarina,wai yaushe kuɗin da ka ba ni zai gama aiki?"Ya canza maganar da sigar tambaya.

Da takaici ya kama shi jifa fa wayar ya yi ba tare da ya kashe ba,yana jin dariyar Baba Sani can kuma ya kashe wayar.

" Ina ga Juwairiya da tsinannen Babanta Sani su za su yi ajalina."

Ko me ya tuna da sauri ya É—auko wayar da ya yi jifa da ita.

Numbar da ta turo masa da tsaƙon haƙuri ya fara bincika duk da bai wani karanta tsaƙon sosai ba.

Wayar na ringing tana ƙara tayar masa da zafin dake cikin zuciyar sa.

Sau uku ya kira amma ba'a ɗaga ba har ya yanke shawarar ba zai ƙara kira ba,sai kuma ya ji muryar wata mace ta yi sallama.

" Ina Juwairiya take."

Ya faÉ—a a gundure da takaicin kiran da ya yi." Ban sani ba kuma in ga wrong number ka yi saboda ban san mai wannan sunnan ba "

Ta faɗa da ɗan daga murya dama abin da ta yi ninyar ta yi masa kenan,saboda yanzu matuƙar haushi yake ba ta yana can yana wahalar da kan shi,ga in da ake masa son mutuwa.

" Ko da ban san ke wace ce ba kar ki raina min wayo kin san dai abin da ke tsakaninmu ,ba kiran ta na yi don ina so ba,a'a saboda ta ɓata mini kuma sai na nuna mata kuren ta."Ya ce da Hauwa ran sa a ɓace.

" Ok kai da ka santa kake wannan maganar amma na yi maka bayanin ban san ta ba balle na sa abin da ya haÉ—a ku."

Hauwa haushi yake ba ta ji take kamar ta kama shi ta yi masa shegen duka saboda irin mutanen nan masu gatsali.

Ta buÉ—e baki za ta yi magana ji ta yi an fisge wayar Juwairiya ce daga bayan ta wacce ta shiga bayi a she ba ta san ta fito ba.

Jikinta har rawa yake lokacin da ta kanga wayar a kunninta tare da fashewa da kuka.

" Hello don Allah ka yi haƙuri ka yafe min wallahi ba zan ƙara ba zuciyata za ta fashe na rashin ka a kusa da ita k..."Wata uwar tsawa ya daka mata.

" Ban kira ki don ki gaya min tsoki buruku ba kin ji na rantse kar ki bari mu haɗe dake don sai kin raina kanki.Gidan uban wa kike Baba Sani ya kira ni ya ce min ba ki a gidan sa?Da auren kike gantali ni dama na san ƴan iskan ƙawaye kika yi da su suke zuga ki,to makarantar ma na daƙile tun da baki san mutunci ba kuma na rantse miki za ki fuskanci fushina mai tsanani."

" Don Allah ka yi haƙuri ka yafe min na yi kuskure ba zan ƙara ba."

Hauwa ce ta fara kiciniyar fisge wayar da ta yi mata kyakykyawar riƙo.
"Dole A.m ya din ga wulaƙanta ki haba kamar ba mace ba duk kin zubar da ajin ki ya raina ki an faɗa miki so hauka ne haka ake nuna ma masoyi ?"

Duk yadda ta so ta karɓe wayar ta ƙi bata,har duƙawa ta yi tana ba shi haƙuri yayin da idanunta ke zubar da hawaye.

" Gidan ƙawata Hauwa Tukur."

Ta bashi amsa har tana in ina garin saurin ta faÉ—a masa." Minti goma na baki ki dawo gida in ba haka ba za ki fuskanci hushina."

A wannan lokacin Hauwa ta ƙarɓe wayar."A.m duk abin da kake yi Allah yana kallon ka,don Allah ya jarabce ka da ƙaunarka sai ka din ga wahalar da ita?Ina jiye maka ranar da Allah zai kama ka a kanta...."

" Ke karki kawo min maganar banza matata ce fa kin san irin maƙudan kuɗin da na saka na aure ta?In har na gane ke kike zugata saina ɗaure ki igiya tai rara.Maza ta dawo cikin mitinan da na bata."

" Juwairiya ba za ta dawo ba saboda ba ta da lafiya sosai in har ka matsu da ta dawo to ka zo ka É—auke ta."

Ɗif ta kashe wayar cikin ɓacin rai saboda tunanin da take mishi ya wuce wannan.

" Haba Hauwa kina gani har sallar dare nake yi don ya kira ni shine za ki ce ba zan koma ba,kin san wannan batsa kika yi don tafiya zan yi."Ta ce cikin murna.

"Ki ce dabbe za'a yi a gidan nan na ga wanda zai kada wani ko da ganina kin san ba za ki ibi komai a jikina.Wallahi mugun haushin sa nake ji ya faye son kan da da yawa na, yi baƙin cikin ɗauke Mama da ya yi ita ce kawai za ta iya ƙwatar miki ƴancin ki,don ke baki maida kanki mace ba shi yasa yake gara ki ya na amfani da son da kike masa.

A.m da yake jin haushin kiran da ya yi mata yana ta zagaye kamar mai É—awafi.

Ya fi kusan minti talatin yana jiran ta dawo ko ba komai ya rage damuwar abinci da kullum yake fama da yunwa,don ko gidan su ya je babu wanda yake masa tayin abinci,ya san ana yin hakan ne don a hora shi.

Wayarsa ya ɗauka yana tsaki ya tura tsaƙo kamar haka.

" Turo min da adireshin gidan."
Chapter 64 · 0% Book details