← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 86

Sashe 33

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ƙaryar iskanci kike tunna kin nuna ba za ki canza ta ba sai dai ki zaɓa ko aikin ko ki zauna ki rinƙa dafa min abincin da kanki,tun da na tashi na ga iyayena suna girki a gidammu amma ke saboda sakarci ki ce ba ki iya ba.Ki na ganin ƙannina duk sun iya girki ke na rasa wani irin tarbiya kika samu. "
Ta katse ta hanyar É—aga masa hannu ta ce."Ka dakata kar abin ya zama cin fuska kuma da kake wannan maganar ai ka san wacce kake aure da matsayin ubana."

"Dallah rufe min baki ke ma kin san sai dai ki yi min gori na mahaifin ki ya riƙe muƙami,amma ba wai ko kun fi mu kuɗi ba iya tarbiya ne kawai da muka hora su da shi, saboda arzikin da muke da shi bai saka ya sa mun yi watsi da al'adarmu ta yi ma miji girki."

Tsaki ta saki ta ci gaba da aikinta ta na faɗin." Ai sai ka yi ba ka da aiki ne ni ina da abin yi kamar yadda ka gani."Ta ɗan ƙara sakin ƙaramin tsaƙi a hankali ta ce." Jarababbe kawai."

Ya kalle ta ya na baƙin cikin halin ta don shi bai yi tunanin halinta haka yake ba."Mu zuba da ni dake tunna baki da mutunci kuma da ga yau in kika ƙara zuwa wani guri bayan akin ki Allah y...."

Da sauri ta tashi ta waurgar da ƴar mini system ɗin dake hannunta tare da faɗawa jikin shi ta rufe bakin shi jin zai kafa mata dokar fita,in ta bari hakan ya faru ita kuwa ya za ta yi da zuwa pati da yawaon da suke da ƙawayen ta.

" Haba mai sanyina don Allah ka yi haƙuri karka faɗi haka kai ma ka san wallahi ban saba zaman gida ba,in ka hanani fita ya zan yi kuma ka san kai ma zaka saka Allah ya yi fushi da ni ne,amma na riga na saba da yawo ba zan iya zama guri ɗaya ba ko da ka rantse."

Ya kalleta da mamakin abin da ta ce ba yan Allah ya jarabce shi da sonta ya riga ya rufe mishi ido da sai ya ce bai yi dacen macen ƙwarai ba,amma so makoho har zuciyarsa ta sauko ya kalleta da shauki ya haɗa hannunta duka ya na murxawa da hannunsa don ya na ganin damar sa ne yanzu ya ce.

" Na lura don kin ga ina son ki shi ya sa kike wahalar da zuciyata Zey amma ba komai ina fatan Allah ya saka miki irin son, da nake miki a zuciyarki nawa zaki gane halin da na ke ciki."Ya faÉ—a ga mamakin ta sai ta ga yana hawaye.
Hankalinta ya tashi ta ƙara maƙalƙalewa a jikinsa ta na share masa hawaye saboda jikinta ya mutu murus da son sa.

" Ni ma fa ina sonka hubby kai ɗin ne ka cika faɗa ba ka min uzuri duk da ƙoƙorina da nake kuma ka san yanayin aikina.

Janye hannunta ya yi akan fuskarsa aran sa ya na faÉ—in." Na sani amma kuma hakan bai hana ki fita ba."

A fili kuwa sai ya saki ɗan murmushi kamar ba shi ya gama hawayen baƙin cikin Juwairiya za ta shigo duniyar auren su ba wanda ya ɗora laifin duk akan Zainab amma sai ya ce.
" To ki canza me aiki ni bana son wancan yarinyar k..."

Ta ƙatse shi ta na faɗin ."Na ji zan canza amma kuma Momi ta ce in dai muka kori wannan ba za ta ƙara ne mo mana mai aiki ba tunna ba ni da haƙuri."

" Kar ki damu dama tuntuni nake son na tambaye ki na yi ma Atine mai aikin gidammu ta kawo mana macce matashiya wacce ta iya girki sosai,in kin bani dama sai na gaya mata ta nemo mana kuma ba za'a daÉ—e ba, za ki ga ta kawo mana tunnna ita ma ta na irin kawo su kusan family mu ita take kawo musu masu aiki."

Ya ce tare da rungumeta ya na goga fuskar shi a na ta."Ok ba komai sai ta kawo mana amma ba za mu kore ta ba sai an kawo mana wata."

A.m hamkalinsa ya kwanta ganin bai sha wahalar samun haɗin kanta ba miƙewa ya yi ya shige ɗakin sa,ya gallah wanka ya fice kai tsaye gidan su ya wuce ya sami Atine mai aiki ya ce." Ina son in kika tashi zamu fita da ke zuwa wata unguwa amma ya zama sirri a tsakanimmu in kika yi min hakan zaki samu alkhairi."

"Ka faÉ—i ko mene ne in sha Allahu zan yi maka."

Ta ce cikin mamakin in da za su kuɗi ya zaro masu yawa ya ba ta.Atine jikinta na rawa ta karɓa ta na kallon shi." Wata yarinya nake son na nuna miki ki kaiwa Zainab a matsayin ƴar aiki.Shikenan buƙata ta kuma ba na son kowa ya sani kawai ki bar shi a matsayin ke kika kawota."

Duk da mamakin maganar da ta yi amma tunanin ta bai kai ko ina ba,ta amince masa akan sai ya zo daga ƙarshe watsar da tunanin ta yi don ta san ya wuce ƙarfin ya kula ƴar aiki ,kasancewar yadda ta ga ya na hantarar su bare ma ta yi tunanin wani abin.

********

A ranar da Juwairiya za ta tafi hankalinta ya tashi matuƙa wanda da Mama ta so taƙi kan ta din ga kwana duk da a kwai nisa sosai ta so Juwairiyar ta din ga zuwa ta na kwana har shekara ɗayan ta yi,amma sai Baba Sani ya kafe dole sai dai ta din ga kwana tunna kuɗi ya biya.

TO MASU KARATU GA DAI AMARYA JUWAIRIYA ZA TA TAFI GIDAN ANGONTA KO YA ZAMAN SU ZAI KAYA ?SAI KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN SAKACI KO HALIN MAZA.

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO

ÆŠUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ÆŠIN KU YA NA SAKA NI NISHAÆŠI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha shidda.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 17*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Juwairiya ta yi tsuru da jakarta ta na kallon Mama da ke tsaye a gefen ta riƙe da hijabin ta a hannu ta na ƙoƙarin saka wa a kanta sai ta ji hawaye sun ƙara wanke mata fuska,ta share da sauri domin Mama tun ɗazu take mata ƙorafin kuka yanzu ma da taga ta na hawaye sai ta yi tsaki ta ce." Gaskiya kukan nan na ki ya fara siƙe ni Juwairiya na ga ke da Baba Sani kuka shirya hakan,amma kin bi kin dame ni da kuka in da kin san ba za ki iya ba uban wa ya ce ki amince."

Sai ta rungume Mama ta ƙara fashewa da kuka ta na jin wani irin baƙin ciki da fargaba ga gabanta da yake faɗuwa a kai akai don ji take kamar ta ce a ta fasa.
"Mama akan ki sami lafiya na amince amma ki yafe min in na ɓata miki na ga kamar ran ki ba ya son na tafi."Ta ce da ita cikin hawaye fuskarta ta tura shi a jikinta.

" Ki na ganin in da bai yi wa rayuwarmu halacci ba wallahi Baba Sani bai isa ya saka ki ƙara wani aikatau ba,don kullum na yi sallah sai na roƙi Allah ya raba ki da shi saboda irin cin mutuncin da kika fuskan ta."
Share hawayenta ta yi ba ta ce komai ba ta shafa kan Ibrahim tare da riƙe hannun sa suka fito tare.

" Mama ji nake kamar kar na tafi sai kun tare a sabon gida."Ta faÉ—a tare da fuska.
Mama ta kalle ta ta ce " Gara ki tafi Juwairiya saboda yau aka yi zaki tafi kuma kin ga mutumim nan ya yi ma rayuwarmu hallaci wanda dalilin haka ina matuƙar girmama shi."

" Humh." Ta ce a cikin zuciyarta sannan ta ɗora da ce aranta jin abin da Mama ta ce." Da kin san abin da ya ƙulla da ba ki girmama shi ba,shi ɗin macuci ne sosai ya fiye son kan sa da rayuwar matar sa da kin san dalilin da ya sa ya yi mana wannan abubuwan da kin tsane shi har iya ƙarshen rayuwar ki."

A lokacin da suka yi nisa mama ta kama hannunta ta riƙe sai hawaye ta ce." Juwairiya ki riƙe mutuncin kan ki a duk in da kike kuma, duk abin da ki kai kin san Allah ya na kallon ki mutunci na ƴa mace shi ne zai zama ado a rayuwarki,ba wai ina zargin ki ba ne a' a ina miki nasiha a matsayina na uwa wacce ƴarta za ta yi nesa da ita,sannan ya zama dole na saki a hanyar daidai don kar ki ga mutum zai aikata abu a ɓoye,ya na tunanin ya kauce idon mutane bayan ya manta mahaliccin sa ya na ganin duk abin da ke"

Jikin Juwairiya ya ƙara sanyi kamar ƙanƙara haka kawai sai ta ji ta fara tsarguwa yadda Mama take ta mata wasu irin maganganu, wanda take shan jinin jikinta don in ta yi mata irin waɗannan maganganun ko kallonta ba ta iya wa.
Yanzu haka ta kasance ta yi ƙasa da idanunta ta ce."Mama an ya ba zan."
Katse mata hanzari ta yi tare da taran ɗan mashin ta karɓi jakarta da ta riƙe da ta yi tsumu ta ɗora a kan mashin ɗin sannan ta kalle ta ta ce." Ma za ki tafi Allah ya tsare da kin sami lokaci ki leƙo."
Chapter 33 · 0% Book details