Sashe 74
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Ai ko baka isa ba tun da ka shigo da ita rayuwarmu dole ka zauna da ita na har abada,Juwairiya za ta ci gaba da zama da mu a matsayin matarka sannan za mu je in da ka ɓoye mahaifiyarta,saboda son zuciyar ka mu dawo da ita,shi kuwa Baba Sani ka barni da shi na san mai zan yi mi shi,saboda ya yi watsi da zumunci Allah sai ya hukunta shi.Sai ku san yadda za ku yi kai da mahaifin kaku dawo da matarka,tun da ku kuka shirya abin ku can ku ƙarata in har ta ga dama ta zauna da kai in ba za ta iya ba,babu dole sai ta zaɓi mai yiwu wa saboda ina son na ga yaran ka,fatana ta haifa maka yara da yawa."
A.m ya ji wani irin saukar abu mai kama da guduma ya sauka a kan sa." Ina sam ba zan iya karya ma Zainab alƙawarin da na yi mata ba,in sha Allahu saina nuna mata ni na san mahimmancin alƙawari ba zan zauna da ita kamar yadda suke tunani ba."
Hamdiyya wacce take cousing É—in A.m ce ,tana zama a gidan sakamakon haÉ—arin mota da iyayenta suka yi.Sai Abba ya É—auko tana karatu a gidan,ta kama hannun Juwairiya da ta ke jin kamar za ta faÉ—i ta zaunar da ita,sai kuma ta kama hannunta ta ce.
" Anty Juwai ta shi muje ciki na ga duk kin gaji da tsayuwa."
A.m ya sauke ajiyar zuciya da ƙarfi yana jin daɗin yadda abin yazo,duk da cewar ya sha mari amma da ɗan sauƙi.
Tun É—azu yake kallonta da ta yi tsaye tsamo kamar wacce ta faÉ—a ruwa,sai hawaye dake turereniya a fuskarata,tana jin irin tarin cin fuskar da suke mata,amam kuma ko mai ya faru ita ta ja ma kanta.
" Alhamdulillah."
Ya faÉ—a a ran sa jin abin da Hamdiya ta ce dama tun É—azu yake kallonta,yana son ya ce ta zauna saboda babyn shi,amma yan jin kunyar idanun iyayen na sa.
Duk yadda Abba ya so Daddy ya saki fuskar shi, amma ya ƙi saboda y ji haushin abin da ya faɗa masa.
Ko da ya rako shi zai tafi sai Abba ya kama hannun sa ya riƙe kamar zai yi kuka ya ce."Ka yi haƙuri da abin da na yi maka raina ne ya ɓace.Abdurrahman haihuwar sa kawai na yi amma kai ka yi duk wata ɗawainiya ta sa,don Allah ka manta komai ba ma shi ba,ka na da iko akan sauran yarana,kawai zafin zuciya na abin da kuka aikata ya sa na faɗi hak.Juwairiya za ta zauna da mu zuwa wani lokaci sannan ta koma ɗakinta ina ka taɓa jin anyi haka! Da yake ɗan na ka mahaukaci ne igiyar kuɗi tana ibar sa,yana tunanin kuɗi zai iya mi shi komai."
" Babu komai Allah ya kauda fitina a tsakaninmu."Ya ce a daƙile kuma ba tare da walwala ba.
Zama ta yi a katafaren falon Umma ta yi tsumu tana kallon dukiyar da aka jera a falon,a ranta tana son ta ga wane gida yafi kyau a tsakanin na A.m da na iyayen sa.
Umma ce ta shigo ta zauna a falon sai gabanta ya faɗi ta ji wani irin banbaraƙwai,ta kasa ko motsi ga miyau da ya cika mata baki kuma yunwa take ji.
" Hamdiya."
Umma ta yi kiranta da ta shiga kicin don ta sama mata abin da za ta ci.
Da sauri ta fito hannunta É—auke da tire na dafaffiyar shinkafa da kayan lambu a sama.
Ta ije kusa da ita tana kallonta haka kawai ta ji ta burgeta." Anty ki ci abinci daga ganin yanayin ki na san yunwa kike ji."Ta faÉ—a da murmushi a fuskarta,burinta ta saki jikinta ganin yadda ta yi.
Juwairiya ta kalli shinkafar sai ta ji sam bai yi mata ba,asalima naman kajin da aka yi girkin da su,take jin ƙarnin su kamar suna ɗanye.
Amai ne ya taso mata da gudu za ta miƙe gashi tana jin kunyar Umma da take zaune tana sanar ma ƴan'uwanta abin al'ajabin da suka ta shi da shi.
Da sauri ta miƙe gabaki ɗaya hankalinta ya tashi ba ta san sadda ta kai hannu ta riƙe ta da take ta shara amai kamar ba za ta daina ba.
A lokacin A.m ya yi sallama ya shigo." Subuhanallahi doctor ya ba mu magani bari na É—auko mata ai lokacin sha ya yi don ba na son babyna ya wahala."
Wata irin uwar harara Momi ta yi mi shi jin abin da ya ce." Kar ka zama mara tausayin mata masu ciki,saboda in ka fara da haka to a haka za ka ci gaba mahaifin ka in har ina da ciki har ije aikin sa yake yi."
" Sorry Momi."
Ya yi mata sannu sannan ya fakaice idanun Momi ya banka mata harara." Ai ke Abba yana son ki ni kuwa ba so tsakaninmu."Ya faÉ—a a zuciyar shi ya fita.
Hamdiya ta ga hararar da ya yi mata sai jikinta ya yi sanyi ta kalli yadda take kwarara aman,sai tausayinta ya cika mata zuciya.
Æaro mata maganin ya yi ya miÆ™a mata tasha amma sai ya dawo.Kwantawa ta yi a kan duguwar kujera gabaki É—aya jikinta ya mutu.
" Momi na ji an ce in mace na da ciki tana yawan amai yunƙurin aman na iya saka yaron cikin ya fita?"
A.m dake kan kujera ya zuba ma cikinta ido shi duk ya ƙosa cikin ya ɗan fito,ta yadda zai din ga shafawa yana jin ɗan sa.
Wintsilowa ya yi tare da zare ido ya ce." Wai haka momi?"
Sai abin ya ba ta dariya ita kanta ba ta burin ɗan ya fita domin ƙila ta fi shi murnar cikin,kawai tana ɗan damuwa ne ɗan zai fito ta gurin ƴar Malam Shehu,amma ya suka iya da ƙaddara.
" Kamar haka na ji malaminmu ya ce lokacin da yake mana bayanin ciki da matankan kula da shi."Ta ce ba tare da ta bari wacce ya tambaya ta ba da amsa ba,a ranta tana jin daɗin yadda maganar ta ƙarɓu.
" Na fa manta ke ma likita kike karanta don Allah Hamdiya ki rubuto min, duk yadda ake kula da mace mai ciki,sai na san yadda zan kula da babyna."Ya ce sannan ya juya yana kallonta da ta yi lamo kamar mai bacci don wahala,a ranta tana jin ta yi Mama ƙaton laifi in dai haka ta sha wuya kafin ta haife ta.
" Ok ba ka da matsala ya A.m.Anty Juwairiya ta so mu je ki gaya min me kike so na dafa miki."Ta maida maganar gurinta tare da kama mata hannu.
Juwairiya tana matuƙar shan wahalar cikin nan,duk abin da ta ci sai ta yi aman shi,in dai ba kalallaɓa ba ko fate,shi ma sai an dafa irin abincin gidan yarin.In kuma ta gama ci ta yi ta amai ko tashin zuciya duk kyawu da ƙibar da ta yi gabaki ɗaya ta rame ta zube ta fita hayyacinta.
Ita abin da ya fi ba ta damuwa shine sam ba ta son duk wani turare da suke shafawa, sai wata humra da Hamdiya ta ba ta tana shafawa.
Tana jin duk lokacin da ya matso gurinta sai ta ji amai,saboda ta gane ba turaren da ya canza ba ne ba ta so,kamshin jikin sa ne ba ta so,tun bai gane ba har ya gane,wanda hakan ya ɓata mishi rai sosai.Ya din ga kumfar baki yana tsiya ya kuma rantse ko mutuwa za ta yi sai ya zo gareta don ya din ga jin lafiyar ɗan shi,rikici sosai suka yi da ƙyar Umma ta sasanta,akan dole ya yi haƙuri ya nisanta kan shi da ita,ya dai ji ta ne amma ya saka a ranshi ko mutuwa za ta yi,sai ya matso ya ji lafiyar baby ɗin sa.
Hamdiya ta yi zuri tana kallonta da ta rintse idanunta kamar bacci take yi,amma tsabar laulayin yake damunta har wani siririn hawaye yake biyo gefen kumatunta.
" Anty Juwairiya ni fa É—azu kin ba ni mamaki sosai ina jin Ya A.m yana gaya miki wai ba son ya matso kusa da ke yake ba,tun da ya samu abin da yake so lafiyar baby É—in shi yake so ya ji,ya kusa dawo da matar so?"
ÆŠan tsaki ta yi tana ganin babu amfanin maganar,da can da take son shi ba ta wani damu ba,balle yanzu da take jin yana mata wari-wari.Ganin ba ta amsa ba sai kallonta take da alama ba ta son maganar.
" Ai wallahi kin ban mamaki sosai haba ina mace kamarki, wani namiji zai din ga nuna wata tafi ni,ina bai isa ba wallahi ya yi kaÉ—an.Ya A.m bai fiki kyau ba sai haske kawai da zai nuna miki saboda shi jan ga fur ne."
Ta ja numfashi tana kallonta ko za ta ce wani abu amma sai ta ga ba ta tanka mata ba,illa lumshe ido ta yi." Kuma da yake cewa ya na da matar so in har ba son ki yake ba mai zai saka ya shigo rayuwarki."
Murmushin dole ta yi ta kalleta ta ce don ta lura ita tana da sauƙin kai ba ruwan ta da ɗagawa,kamar sauran ƴan'uwan A.m da kan su a ɗage yake suna fisgan kai,duk da cewar sun yi murna da jin ɗan'uwan su zai samu baby daga gare ta,amma da suka zo haka suka din ga nuna feeling.
" Kar ki damu da ni Hamdiya a halin yanzu na ƙosa na rabu da cikin nan na koma gurin Mama,saboda kullum sai na yi kuka ashe dama haka ta sha wahala da ni,amma na ha'inceta na yi aure ba tare da sanin ta ba?"
Sai ta fara kuka sosai dama mai shirin kuka ne, aka jefe shi da kashin awaki,tsananin laulayin da take fama da shi ya dame ta.
TO MASU KARATU KU DAI BIYO NI KU JI YADDA ZA TA KAYA A TSAKANIN SU YAU BAN YI TYPIND DA YAWA BA,SABODA BA NA JIN DAƊI KU YI HAƘURI DA WANNAN ANA TARE.
KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.
BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU
JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY
TALLAH!TALLAH!!TALLAH!!!