← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 86

Sashe 24

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya na shiga ko parking bai yi ba ya fito ya ƙarasa gurin Audi direba dake mishi sannu ya na son ya kulle get ɗin ya ruga bayi,don har lokacin cikin sa bai dai na murɗawa ba.

Mari ya zabga mishi." Kai wane irin banza ne matsiyaci kawai gidan ubanka ne da zan ɗauki lokaci ina hon baka amsa min ba? Ko kuɗin da nake biyan ka da shi haƙo su nake!"

"Allah ya baka haƙuri ina bayi ne cikina ya lalace."

Bai saurare shi ba ya shige cikin gidan falo ya shiga gibbiyar ta na kwance a doguwar kujera me cin mutum uku da remote a hannunta ta na kallo.

Ba tare da kallon in da take ba ya shige cikin É—akinsa ruwa me sanyi ya dinga kwankwaÉ—a har sai da ya cika cikin sa,amma bai ji zuciyar sa ta dai na tafarfasa ba don ji yake kamar za ta fito.

Ya yi cilli da robar ruwan dai-dai lokacin da ta shigo ta na mishi kallon ko ya taɓu ne? Tsaki ta yi kawai ta fice ta san in ta tambaye shi zai iya gaya mata baƙa ita kuma sai ta rama,don haka ba ta tanka mishi ba ta ɗauki wayar ta dake kan gado ta fice a ran ta ta na faɗin." To wa kuma ya taɓo wannan kububuwan?Ba zan yi mishi magana ba ya ƙare a kaina bari na bari ya huce."Ta koma ta yi kwanciyar ta ta na kallo.

Tofa masu karatu kun dai jin yadda ta kaya game da waÉ—annan aminan juna.Ku ci gaba da bibiyata na gode da yaba lintafina da kuke.

ÆŠUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ÆŠIN KU YA NA SAKA NI NISHAÆŠI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha uku.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 13*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

A.k ya na tuki ya na jin zuciyar sa na wani irin tafasa sai dukan sitiyarin yake ya na tsaki ji yake kamar ya je ya shaƙe shi,ya na ji a ran sa ba zai ƙara hulɗa da shi ba don ya tabbata ba shi da mutunci kuma yau zai mayar mishi da motar da ya siya musu a tare da suka je Dubai.

Da sauri ya taka burki ganin ya na son ya buge wani yaro dake sai da rake a tire,ya yi ƙoƙarin janyo natsuwa don ya samu ya isa gida lafiya saboda da ƙyar yake gani.

Matarsa na zaune ita da yaranta suna assigment sai ganin sa ta yi ya shigo kamar an jeho shi,bai amsa sannu da zuwa da suke mishi ba ya shige ɗakinsa wanda ya ɗaga hankalin ta ta miƙe ba shiri ta bi bayan sa.

Ganin yadda ya haɗe kai da gwiwa ta ɗauka rasuwa a kai don haka jikinta a mace ta ƙarasa gun sa tare da dafa shi.

" Lafiya Baban Najwa in ce ba wani abu mummuna ya faru ba?"

Ta faɗa cikin tsoro ganin yadda idanun sa suka canza sannan ta ƙara cewa." Ka yi haƙuri dama haka duniya take ni dai fatana ba mutuwa akai ba,ko wani mummunan lamari ya faru! Don Allah ka yi magana."
Bai amsa mata ko ɗaya ba ya ɗauki ruwa ya na sha.Ganin haka sai ta janyo jikinta bayan ta ƙara A.c ɗakin ta janyo mishi kofa a ran ta ta na addu'ar Allah ya sa lafiya.

Kimanin rabin awa ya É—auka a cikin É—akin sannan ya yi wanka ya fito da duguwar farar jallabiya a jikin sa,gefen ta ya samu guri ya zauna ya na kallon ta da É—an murmushi a fuskarsa.

Sai hakan ya sanyaya zuciyarta da take ta bugawa ta na tunanin ko wani abu me girma ne ya faru.

Ido ya zura mata bai ce mata komai ba hannunsa ta kama tare da É—ora kanta a kafaÉ—an sa." Zuciyata ta ku san bugawa da na ga ka shigo a cikin wannan halin."

Shafa gashin kan ta ya yi yace a hankali da muryar da har yanzu a kwai ɗan ɓacin rai a cikin ta." Mun yi faɗa ne da A.m kuma me zafi don har na bar mishi aikin sa,zan kuma mayar mishi da duk wani abu da ya mallaka min."

Ya faÉ—a ya na furzar da wani irin huci mai zafin gaske.

Kallon sa take da irin ba za ku taɓa canzawa ba duk cewar ta san suna faɗa amma wannan karan da alamar faɗan ya yi tsamari ganin yadda ransa ya ɓace.

" Me kuma ya ƙara haɗa ku?"

Miƙewa ya yi ya ɗauki wayar sa zai koma ɗaki jin tambayar da ta yi mishi wanda ya ɗaukar ma kan sa wargaza shirin,amma kuma bai gaya mata ba sai yace." Wanann kuma sirri ne a tsakaninmu."

Ya ƙarashe shigewa bayan ya riƙe hannun Farha dake ta nacin ya ɗauke ta tun da ya fito daga ɗaki,ya bar ta a tsaye ta na jinjina wane irin rikicine ya faru a tsakanin su har ya yanke barin aikin.

" Ko ma mene ne su suka sani haba! Suna girma suna cin ƙasa." Tace cike da takaicin halin su sai kuma ta yanke shawarar ta kira Zainab ta tambaye ta sai da wayar ta yi ringin sau ku,sannan ta ɗauka tare da sakin wawan ajiyar zuciya.

" Hello sahiba ki yi haƙuri ina falo na bar wayar a cikin na manta da ita,sai da Atine me aiki ta kawo min.Ina yarana?"

Ajiyar zuciya ta yi tace " Ba komai wallahi suna lafiya dama na kira ki na tambaye ki ko A.m ya na nan,na ga aminin na sa ya shigo kamar sun sami saɓani hankalina a tashe yake."

Tsaki ta yi ta taɓe baki." Humh ke kika kula shi ni nawa da ya shigo ko kallon sa ban yi ba,na kyale shi don ba na son ya haɗa min zafi saboda ni ma a cike na ke da wata da ta yi min rashin mutunci a tiktok."Ta ba ta amsa ta yamutsa fuska.

"Zainab!Wai ke ba zaki dai na yin rawa a tiktok ba! A da baki aure amma yanzu ke matar aure ce hakan bai dace dake ba,kin ci sa'a shi A.m sam ba ya yin tiktok amma in Allah ya so ya kama ki sai kiga wani ya tura mishi kuma ba zai ji daÉ—i ba."

" Umh ke ni kyale ni lokacina ne kin san iya yawan adadin mutanen da suke bibiyata,so kike na yi asaran mutanen da suke zuzuta kyawuna?Ai in kika ga na dai na ƙila na mutu ne."

" To Allah ya shirye ki da masu hali irin naki a matsayin ki na matar aure ji je kina bayyana surar ki ɗora waƙa ki nabi don kawai ki yi suna ko burge mutane,ba yan kin san haramun ne a addini kuma bayan haka malamin ahalari yace.Wal mar'atu kulliha aurati ma adal wajha wal kaffaini.Wato ita mace dukkannin ta al'aura ce sai dai fuska da tafukan hannaye. Gaskiya ya..."

" Wash Allah na! Wallahi Maman Najwa kin cika cika mutum wannan dalilin ya sa ban cika zuwa gidan ki ba.Ke kullum sai kin yi ma mutum wa'azi,ke da uztazi kika aura sai kin addabi mutum da wa'azi ina ga ko sallah mutum ya yi zaki ce ba dai-dai bane." Ta É—an numfasa ko za ta ce wani abu sai ta É—ora da cewa jin ta yi shiru ajiyar zuciya ta sauke.

"In kin kira ni ne ki yi min wa'azi ba ni da buƙata matar liman sai kije masallaci ko in da ake buƙata.Ni ya maganar mu na fara yin sana'ar zuwa waje kin yi mishi bayani."Ta canza maganar don ta gundire ta ita ba ta da wani aki sai na yin wa'azi ita kam ba za ta iya ba,ita dai da ta ga za ta iya kashe rayuwar ta da kuruciyar ta sai ta yi Allah ya ba ta sa'a.

Dariya ta yi jin ta canza maganar tace." Na gaya miki tun ranar ni ba zai barni na fita zuwa wata ƙasa saro kaya ba,gara mu dinga basu kuɗin ko mu yi oder kin san yanzu komai a sauƙaƙe yake."

"Taɓ kin yi makaranta amma kamar baki waye ba ok da ma kina jira ya amince miki ne? Dama ba sana'ar kike so ki fara ba,ai koni da kika ji nace zan yi ba zan gaya mishi ba,sai ya ji na fara ke ranar da na ɗan sako mishi maganar Yayyina suna zuwa waje yin business,bai kalle ni ba yace ai da yake mazan na su mahaukata ne basu san mahimancin iyali ba.Shiru na yi bance komai ba ai sai dai ya ga na ɗaware inna dawo koma me zai faru ya faru Am ready for the conseqeuncy."

A ranta ta na girmama irin halin Zainab wacce sab ba ta tsoron miji ga shi Allah ya yi mijinta da son girma,sai dai bai samu macen da za ta ba shi wannan girma ba aiko za'a sha daru don shi ma ba daga baya ba.

" To shike nan Allah ya sa ki gane ni dai ba zan baki kuÉ—ina ba kar mijin ki ya ji na baki,ni ina daraja aurena ke na lalata miki na ki gara na ba shi ya yi min oder hankalina kwance,sannan ki je ki rarrashe shi ki ji abin da ya haÉ—a su ko ma bai gaya miki ba don Allah ki ba shi kula kina sakaci da mijinki fa kar wata ta yi miki kwace."

Ta faɗa da tsigar tsokana duk da ta san Zainab yanzu za ta harzuƙo mata da shegen baƙin kishinta amma ta kasa kula da shi.
Chapter 24 · 0% Book details