← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 86

Sashe 69

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Zainab don Allah kar ki mutu ki barni ba zan iya rayuwa ba,in har babu ke a cikin duniyar nan,ki tashi na yi miki bayanin na aure ta ne don ke,don Allah ki buÉ—e ido.

A.m yake faÉ—i ya na jijjigata cikin tashin hankali." Ya kamata a kaita asibiti fa kar ta mutu."

In ji Lantana da take kallon tashin hankali wanda ba' a saka mishi rana.

A.m ya miƙe daidai lokacin da Lantana ta ruga kiran direba,don ya kasa komai sai zare idanu da yake yi.

Zubbur ya ga ta miƙe tare da sakin wani irin ƙara wanda sai da gidan ta girgiza,kawai sai ta saki dariya kamar sabon kamu.
Wani ihun ta saki da ƙarfi ta yi kansa ta na faɗin." Ƙarya kake yi wallahi ni kaɗai na tashi a gidanmu na rayu ni kaɗai ban taɓa sharing ɗin wani abu ba,sai kai abin da nafi so fiye da komai a rayuwa.Ina hakan ba zai taɓa faruwa ba!"

Ta ƙara riƙe shi ƙam ta ci gaba da cewa.Ƙila mafarkinmu duniyar mahaukata ya kawo mu,don na lura kai kanka ba ka san mai kake faɗa ba,don wataƙila baka cikin hayyacin ka."

Mari ta kawo mishi cikin zafin nama ya kauce tare da riƙe hannunta,ya zare idanun sa ya ce."Tabbas bari na ƙara gaya miki ita ɗin matata ce,gaskiya kunninki yake gaya miki,kamar yadda igiyar aurena uku yake a kanki,haka ita ma amma ki tsaya ki sauraare ni,kin san ina sonki ba zan yi abin da zai cutar dake ba. na aureta ne don na..."

"Kai."

Ta daka mishi tsawa da idanunta da suka rine sukai jajur!Saboda tashin hankali.

" Karka gaya min maganar banza ka rabu da ni macuci haƙiƙa ka cuce ni,ka kuma yaudareni.Ka manta ka yi min alƙawarin ba za ka taɓa min kishiya ba,balle ka sanar da ni ce ba na haihuwa shi ne yau ka auri wata mace ban sani ba,kuma saboda cin mutunci ka kawo ta gidana ka na kwana da ita a gadon da iyayena suka siyar mini,wallahi mafi girmar kuskuren da ka yi ka kawo ta gidana,ka maida ni banza shashasha sauna! Ashe in bana nan sakewarka kake da ita?Har kana mini munafucin baka riƙe sunann ta ba.

Wayyo Allah na! A.m ya maida ni banza ya kawo matarsa gidana a matsayin mai aiki!Wace irin banza ne ni har na kasa gane tsakanin su?

Wallahi sai kun yi nadamar abin da kuka yi mini,zan nuna maka cewar da gaske ba a yi ma family ɗinmu kishiya,take yanzu zan kasheka in kashe kaina haka kuma in kasheta!Mutuwar kasko za mu yi daku,ban taɓa sharing ko da wani abu ba balle na haɗa jiki dakai ƙazami kawai."

Da gudu ta ruga kicin kafin ya farga har ta ɗauko wuƙa ta yi kansu ta na faɗin." A yanzu za ayi ta taƙare yanzu zamu yi mutuwar kasko,hisabi akan abin da kuka yi mini zan yi muku tun kafin aje lahira ku haɗu da ubangiji,munafuki mai karya alƙawari."

" Zainab ki ki natsu karki aikata dana sani! Look Zainab kar ki aikata abin da kike son yi,sheɗan ne yake so ya kaiki ya baro,don Allah ki natsu zan yi miki bayani,ina da dalilin da ya sa na ɓoye miki auran."

Kallon mahaukaci take mishi ta tsaita wuƙar daidai gurin Juwairiya tana matsawa kusa da ita.
" Saina nuna miki kuskuren da kika yi mijina za ki aura,kin yi babban kuskure ni kaÉ—ai nake rayuwa a gidan mahaifina,haka dangimmu kaf babu wata mace da aka yi wa kishiya sai ni?Wallahi ba ku isa ba,sai na nuna muku kuskurenku."

Gadan-gadan ta yi kanta data tsorata ganin ta nufo ta da wuƙar,ɓoyewa ta yi a bayan A.m da hankalin sa ya tashi matuƙa,saboda yadda Zainab ta koma za ta iya yin komai.

" Zainab kar ki kashe musu ƴa za ki yi dana sani fa shari'a ba za ta ƙyale ki ba kema kashe ki za'a y."

"Don na kashe ƴar matsiyata uban wa zai taɓa ni na san ko an kulle ni Daddy zai fito dani."Ta bashi amsa idanunta a bushe.

" To ni in kika kashe min É—a wallahi saina kulle duk yan gidanku ba ke ba,saboda ko ba komai zan ga É—ana a duniya na rungume shi iyayena su yi alfahari da hakan."Ya ce mata cikin zafi da É—aga murya.

Kukan kura ta yi taho kan kanta da gudu jin abin da ya faÉ—a,yayin da idanunta suka rufe ba ta ji ba ta gani.

" Yadda ba na haihuwa kai ma ba za ka taɓa ganin ɗanka ba,saboda kai na lalata mahaifata,don na faranta maka shine za ka auri wata,wallahi baka isa ba."

Da sauri ya cakume ta ya riƙe ƙam iya ƙarfinsa ganin abin da take shirin yi.

Juwairiya ta sadaƙar mutuwa za ta yi lokacin da ta yi kanta da wuƙar.Ta rintse idanunta tana salati.

Fuɗuwa suka yi a ƙasa ita da shi ya fara kiciniyar karɓe wuƙar.
Sai kawai ta kai mishi wukar jikin shi Allah ya ba shi sa'a ya kauce,wuƙar ta yanki hannun sa sosai.

Ba Juwairiya kawai ba hatta wanda ta yi yankan sai da ta É—an firgita ganin irin jini da ya fara tsartuwa a hannun sa.

A.m ya kira sunan Allah da ƙarfi ya ji wani irin raɗaɗin azaba yana ziyartar sa,jikin shi ne ya kama rawa ganin duk da yankar da ta yi masa,jini na zuba amma ba ta razana ba,sai ta nufi Juwairiya da ta yi kan sa ta kama hannun sa tana kuka,mai haɗe da salati matuƙar tsoro ya shige ta ganin abin da ta yi.

" Ai na gaya muku wallahi sai kun gane kuskuren ku na cuta ta da kuka yi!"Ta faÉ—a lokacin da ta yi kanta.

Da sauri A.m ya miƙe ya saka ƙafafun sa ya taɗiyeta ta faɗi yarab!Amma da ƙarfin hali duk da buguwar da ta yi,sai da ta ƙara nufo ta da wuƙar.

Ƙara hankaɗe ta ya yi za ta faɗi ya tare ta bayan wuƙar ya faɗi gefe.

Ta saki ihu tana zage-zage kamar wata mahaukaci.

Da ƙarfin tuwo ya riƙe ta tare da yin dubara ya sakata a cikin ɗaki,sannan ya jawo ƙofar ya kulle.

Wayar sa ya É—auka ya kira Mominta don ita kaÉ—ai yake tunanin za ta shawo kanta.

Zuciyar sa a fusace ya ja hannunta suka fita,a cikin mota ya saka ta sannan ya shiga ya ja.

A.m dake tuƙi gabaki ɗaya hankalin sa ya tashi ƙwarai,ko a mafarki bai taɓa tunanin abin da Zainab za ta yi mishi ba,duk da daman ya san zai sha fama da ita.

Ya juyo yana tuƙi da bai san in da za shi ba ya kalle ta,sai ya ga ta dunƙule jikinta hawaye yake turereniya a fuskarta,kamar rawar sanyi take yi ganin yadda ta takure lokaci guda.

Ya sani cewa ya tono ma kan musamman in iyayen sa suka ji abin da ke faruwa,don ya san Zainab sai ta fallasa komai.

Guri ya samu ya samu ya yi parking ba tare da sanin abin da zai yi ba,ya kwantar da kan sa a jikin sitiyarin É—in.

Karo na farko yau ta ga karaya a fuskar shi tun iya rayuwar da suka yi ba ta taɓa ganin abu ya saka jikin shi ya yi sanyi ba,ko da kuwa Baba ne Sani da ta lura ya na matuƙar tsoron shi,amma yana ɓoyewa,sai ya ba ta tausayi sosai.

Ta kalli hannunsa da yake tuƙi jini duk ya ɓata in da ya riƙe kuma ya na ta zuba,kawai sai ta saka kuka tare da cire ɗaukwalin da ta ɗaura,ta kama hannun za ta ɗaure.

" Asirina ya tonu ko kaɗan ban taɓa tsammanin lamarin zai tafi ta haka ba,ina tsoron mahaifina in ya ji abin da na aikata,Daddy zai yi fushi sosai.Dama haka Zainab take da kishi kai mata basu da tunani wallahi!Duk abin da na yi don na faranta mata ne.

" Ina tsoron Daddy in ya jin wanan lamarin ban san abin da zai yi min ba,wataƙila ya tsame ni daga cikin yaran shi."

Kamota ya yi ya riƙe da hawaye a fuskar shi ya ce." Ki ba ni shawara na rasa yadda zan yi zuciyata za ta fashe."

Kawai sai ta fashe da kuka sosai tana tausayin kanta da shi,don ita kanta tana tsoron ranar da za ta koma gurin Mama.

Rungumeta ya yi ƙam yana jin kamar rungumar za ta yi masa maganin damuwar sa.

Wani irin hucin zafi ya ji a jikinta da sauri ya matsa gefe yana kallon ta,daidai lokacin da ƙamshin turaren sa ya ƙara taso mata da amai,ta buɗe motar a guje ta fara sheƙa shi.

A.m hankalin sa ya tashi sosai ya tsaya yana kallonta ya rasa wani tunani zai yi,gashi ko ruwa babu wanda za ta kuskure bakinta da shi.

Sannu yake ta jera mata ya riƙe ta sosai kamar zai mayar da ita jikin shi,sam bai damu da aman da take yi ba.
Da ta gama aman ta miƙe sai ta ji jiri ya kamata za ta zube a ƙasa,da sauri ya tare ta ta faɗa jikin shi,bai damu da jinin da ke zuba ba ya riƙe ta sosai da hannun.

Mota ya mai da ita sannan ya ja suka wuce asibiti.

" Doctor ka fara duba ta da gaske wani cikin ta ƙara samu?"

Ya ce da likitan bayan ya zaunar da ita akan kujera.

Likitan ya kalle shi ya ga irin jinin dake zuba a hannun sa,sannan ya juya ya kalle ta da ta yi sanyi sosai,ciki mai ilinbo gabaki É—aya jin wani iri take a jikinta.

" Ya kamata na fara duba ka kalli bleading hannun ka yake yi.".
"Kar ka damu da ni doctor kawai ka duba ta ina son na sani da gaske na kusa zama uba"A É—okan ce yake magana.Ya faÉ—a jin abin da likitan ya ce.

" Ok to shikenan bari na kira doctor Garkuwa ya duba ka kar ka fara ganin jiri."

" Congratulation ina farin cikin sanar dakai matarka na da ciki sati uku."

Sujjada kawai ya ga ya yi sai ya rungume shi yana murna." Ashe nima zan zama Baba! Allah na gode maka."
Chapter 69 · 0% Book details