Sashe 71
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Matar kawuna ta yi mini hanyar wani malami ya ta kaini gurin sa,don ya janye hankalin sa daga gareta,amma sai dai in na yadda da sauran ƙwayayen haihuwana za'a yi asirin,in da za'a bar ɗaya kawai wato ɗa ɗaya zan haifa a duniya.Ba tare da damuwa ba na amince.A lokacin har an saka ranar auren su biki ya rage kwanaki aka fasa auren,in da ya zo gidammu da fari iyayena sun ƙi,amma ganin zai haukace dole aka ɗaura aurenmu wanda dalilin haka ta aikata suicide. ta mutu.
Sai dai na fara nadama bayan aurenmu duk lokacin da hankalin sa ya dawo jikin sa,sai ya kasance ina yawan zuwa a juyar masa da hankali,a haka muka rayu har na haife ki bayan na haife ki sai Allah ya saka mi shi tsananin sonki,domin yana son yara sosai ya sha gaya min zan haifa masa yara da yawa."
Momi ta yi nisa tana kallon Zainab da ta yi zuru ta zuba mata ido tana kallonta cikin al'ajabin labarin da take gaya mata.
" Na yi matuƙar dana sani sosai da na yadda aka yi amfani da sauran ƙwaina,saboda dangin sa sun takura mi shi akan ya ƙara aure,sai dai na yi ruwa na yi tsaki har yau ya kasa ƙara auren.Don haka ki share hawayen ki A.m bai isa ya zauna da wata mace ba bayan ke,ke kaɗai ce za ki zauna da shi har abada,na yi miki wannan alƙawarin in...."
" No Momi don Allah kar ki saka wani abu daban a cikin aurena! Ina son A.m ina burin na rayu da shi har abada,kuma kin san ni ba na son waɗannan halayen da kike yi,don haka in ba za ki taimaka min ba,kawai ni zan watsa mata acid ko na ɗauketa a garin."Ta ce da Momi cikin shagwaɓa tana kallonta yayin da hawaye suke ƙara turereniya a fuskarata.
" Banza shashasha! Ita kin san abin da ta yi har A.m ya kula ta? Ki zauna garin kallon ruwa kwaɗo ya yi miki ƙafa,kuma Allah kin ji na rantse miki ko ke baki yadda da hakan ba,dole mu zamu ɗauki mataki."
"Haka ne Momi ki yi haƙuri amma gaskiya ba zan amince da abin da kike so ba,zan kira Anty Lubna na san za ta ba ni shawara."
Gabaki É—aya kayan sawarta suka kwashe ita da Momi,bayan ta kira mahaifinta ta sanar masa take ya buga ma Daddy A.m waya saka yi kaca-kaca.
Jikin Daddy ya yi sanyi to fa asiri ya tonu ya san cewa a kwai daru saboda shi ya saka hannu aka É—aura auren.
Jikin shi ya kama rawa saboda irin zagin da mahaifin Zainab ya din ga yi mi shi,ya san dole ya kira ainihin mahaifin shi ya gaya mi shi.
Wani irin zufa take tsefo masa don ya san Allah kawai zai fidda shi,sai yanzu yake ganin mugun wauta da ya yi har suka yi galaba ya amince da aure.
Wayar sa ya zaro ya don ya kira A.m cikin fushi.A ran sa yana baƙin cikin halin dukan mata da A.m ya ɗaukar wa kan sa.
**********
" Wai mene ne haka ne A m ka san mai kake yi kuwa a asibiti muke,kuma ka duba idanun mutane a kan ka suke sam ba ka da kunya."
A.k da ya yi wa Juwairiya rumfa da take kwance kan gado,ya kuma tura hannun sa a cikinta wai zai ji in da yaron yake.
Juwairiya da wani irin kasala ya rufe ta zuciyarta tashi take yi,kamar wani aman yake son ya zubo mata.
Da sauri ta ture hannun sa ji ta yi kamar an É—ora mata wuta a in da ya É—ora mata hannu a cikin.
Ita ji ta yi da ya matso ta kamar wani irin wari za ta ce ko ƙamshi mara daɗi yake mata.
Hannunta ta saka ta toshe hancinta da jin wani amai zai taso." Don Allah ka matsa kusa da ni sam ba na son jin ƙamshin ka kusa da ni."Ta faɗa da muryar kuka tana jin wani ƙunci a tare da ita.
A.m ya yi turus kamar zai saka kuka ya juya ya kalli A.k da ya zuba masa ido sosai cikin son dariya.
" To fa baban baby ka ce kai ma ka shiga daga ciki kenan."
Ya faɗa a ransa yana tunanin kamar Juwairiya tana daga cikin jinsin matan da Allah ya halitta,a lokacin da suka samu ciki sai Allah ya jarabce su da tsanar miji tsana mai tsanani,yayin da suke ƙaurace ma mazajen su wasu har suna cutar da kan su.
Don matar sa tana daga cikin irin masu wannan halittar,duk sanda ta samu ciki shikenan zaman lafiya ya yi ƙaura a gidan su har ta haihu.
" Humh ka na ji fa wannan yar rainin wayon take faÉ—in na matsa,ai ita ta san in da ba babyna da yake jikinta ba babu abin da zai saka na matso kusa da ita,bayan ta san babu macen da nake so irin matar so."Ya faÉ—a yana hararar ta sosai ganin ta hana shi jin motsin baby.
Ga mamakin sa sai ya ga ta mayar masa da hararan da ya yi mata,don ita har ga Allah ta ji wani irin tsanar shi a cikin ranta,ba wai don abin da ya faru ba,sai dai wani canji da ta ji a jikinta,saboda in ya matso wani irin wari take ji har da ƙarni-ƙarni a jikin sa,wanda yake tado mata da hararwa.
A.k da ya yi tsuru yana kallon abin al'ajabi ganin yadda suka ɗauki fushi,bai taɓa tsammanin Juwairiya tana da tsiwa ba.
" Ikon Allah yau kuma irin murnar da za ku nuna kenan,bayan yau Allah ya kusan cika muku burin ku.Kai zaka samu magaji,ita kuma za ta koma gurin Mama kamata ya yi ku nuna ma Allah godiyar ku."
A tare suka harari junan su sai ta ji wani irin kewar Mama da son ganin ta ya kamata.
Hawaye ta soma zubarwa wanda ya É—aga hankalin A.m,cikin É—aga murya ya daka mata tsawa.
" Ki yi ma mutane shiru so kike É—ana ya gado shegen kukan ki na rashin dalili."
A.k da yake kallon dirama dafa kafaÉ—an sa ya yi ganin yadda ya daka mata tsawa.
" Haba A.m be a man. Baka ka san ba'a É—aga ma mata masu ciki murya,irin shi ne suke haihuwar É—a motsi kaÉ—an sai ya birkice."
Da sauri ya kalli A.k cikin razana ya kama hannun sa ya riƙe sosai." Da gaske kake?Ina ga zan duba duba google akan yadda zan kula da cikin saboda kar a samu matsala, ina son yarona ya fi ɗan kowa a duniya,kuma ba na son ya yi kama da waccan abar mai emotionally fence."Ya ce yana nuna ta da bakin sa tare da galla mata harara.
Tura bakinta ta yi ba ta ce masa komai ba,don ita yanzu haushin sa take ji na rashin dalili
A.m ya ƙara hassala don ya tsani raini, karfa don ta ga ta samu ciki tace za ta yi mi shi rashin kunya,da kuma ya tuna abin da A.m ya gaya masa sai ya duƙa kusa da ita.
" Kin san fa yanzu bake kaɗai ba ce,don haka duk kulawar da zan ba ki babyna nake ma wa,ki kwantar da hankalin ki yarona ya sakata ya wahala ya yi ƙatoto."
Ya ƙara sausauta muryar da ba ta taɓa sanin yana da shi ba." Baby mai kake son ci?Ka faɗi duk abin da kake so zan kawo maka shi."
Ture hannun sa ta yi ganin ya ƙara kawo wa "Don Allah ka ƙyale ni ba na son cin komai."
" Ba ke na tambata ba babyna nake magana da shi don na san dole yana buƙatar abinci."
Ya faÉ—a a kausashe don shi jin yake anya zai iya É—aukar raini daga gare ta.
" Ka dai kula da abin da na ce maka, in ka din ga daka mata tsawa ta haifi yaron matsoraci, kai ka sani ka san dai wannan shikenan babu ƙari."A.k ya ce da shi.
Sosa kan shi ya yi." Na ji kuma zan kiyaye in sha Allah.Dole na samu babban likita wanda zai dinga É—orani a kan yadda ake rainon ciki."
Juwairiya ta miƙe ta tana wani yatsina irin na masu ciki gabaki ɗaya ta ji wani canji a jikinta.Dambu da kalallaɓa ta ji kawai tana son ta ci,amma ta san ko ta faɗa masa ƙila ba zai nemo mata ba.
Amma kuma da ta ji son cin abincin zai saka mata amai,in dai ba ta ci ba kallon sa ta yi ta ce." Ni fa dambu zan ci da kalallaɓa kuma yanzu nake so."
A.m ya zare ido ya ce." To yar rainin wayo gara dambu na san shi matar A.k tana yi,amma kuma mene ne kalallaɓa?Ni fa kar ki raina mini wayo ƙila ba baby ba ne zai ci."
" Ko ma waye zai ci dole ka nemo ai wallahi tausayinka nake ji,don yanzu ka shiga hannu dole ka zama ɗan siyayya."A.k ya ce mishi yana kallon doctor da ya turo ƙofa ya shigo.
" Yauwa doctor yau she zan dawo ka ba ni shawarar yadda zan kula da babyna."
Dariya ya yi suka tafa da A.k." Abinka da sabon shiga."Hararar A.k ya yi jin abin da ya faÉ—a.
Wayar sa da take da can gefen Juwairiya ta É—auki ruri sosai.Gaban sa ne ya faÉ—i don ya san kiran bai wuce daga gidan su.
" Please A.k É—aga wayar ba zan iya ba na san bai wuce Daddy."Ya faÉ—a yayin da fara'ar shi ta kau.
Shi kan sa A.m a tsorace yake ya san ayau Allah kawai zai raba su da shi.
Da ya É—aga wayar sai ya saka ta a hands pree.
" Kaicona Abdurrahman! Yau na yi dana sani da na ɗora yaƙinina akan ka.Abin da ka aikata kenan?A she baka da hankali wallahi ban taɓa sanin mahaukaci ba ne kai sai yau.Maza ka taho gida ina neman ka duk in da kake, da kuma yarinyar da Zainab ta ce ka dake ta saboda ita,don ni bazan ce matar ka ba ce sai dai kuma in ka canza iyaye bayan ni da Daddy ɗinka.Minti biyar na baka."
Mahaifin A.m ya faÉ—a yana huci ya kashe wayar,yana kallon Daddy da ya yi tsuru-tsuru.