← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 86

Sashe 84

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin cikin wata takwas ya shiga amma duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata,saboda ta yi wata irin ƙatuwa a yadda kamanninta suka canza ina tunanin ko Mama ta ganta sai ta yi da gaske za ta gane ta.

A.m hankalin sa ya tashi ƙwarai tun da ya fara kwana da ita ya shiga tashin hankali,ganin irin wahalar da take ji sam ba ta samun bacci.

Hannunsa ya sa da nufin ya kamata cikin tausaya,amma sai ta ture shi ta riƙe kwankwasonta tare da rintse idanunta,tana jin wani irin azabar raɗaɗin mutuwa yana shigar ta.

" Wayyo Allah na!Mama ki yafe mini dama haka kika ji kika haife ni! Wayyo Mama ba laifina ba ne halin da kike ciki ya sa na amince da abin da mugu azzalimi ya zo mini da ita.Baba Sani Allah sai ya saka wa mahaifina sam baka riƙe maraicin da mahaifinmu ya baka amana ba."

Sai ta cige baki ta miƙe da nufin ta tashi,amma ta kasa da sauri ta koma ta zauna, tare da jingina kanta a kan gadon don ji take kamar ɗan dake cikinta zai fito ta bakinta.

A.m da yake jin wani tashin hankali kusan haka suke kwana duk da sun je asibiti,amma sai a ce musu lokaci bai yi ba,sannan (E.D.D)É—inta bai yi ba balle ayi mata aiki,don haka su jira lokaci.

Duk iya juriyar sa in ya ganta cikin wannan tashin hankalin sai ya ji hawaye da nadama na shigar sa.

Bai san cewa ya shaƙu da ita ba musamamman lokacin da ta fara masa tsiwa, tana nuna ba ta son sa da tsoron sa.

Hunnunsa ta kama ta riƙe ta kalle shi da fararan idanunta wanda yanzu suka koma suka rine saboda ruwan azabar da take kwankwaɗa.

" Bazan yafe maka ba kai da Baba Sani, kai harma da A.k duk da na san ka tilasta shi ne,amma wataƙila da ya jajirce bai amsa ba da ba ku zo gurina tun da kana jin maganar sa b...."

" Juwairiya ki yi shiru za ki haihu lafiya ki koma gurin Mama in sha Allahu Mama za ta ƙara tozal..."

Katse shi da ƙarfi ta yi." Ka yi shiru don Allah mutuwa zan yi! Jikina ya ba ni bazan ƙara ganin Mama ba a rayuwata,ka raba ni da Mama don kawai burinka na ka samu ɗa.Ka tuna ni ma ƴa ce wacce uwa ta haifa take sonta, kamar yadda kake son ɗan da za ka haifa,saboda burinka na haihu ka ba wa matarka ka nisanta ni da Mama A.m ba ka yi mini adalci ba,na tsane ka bana sonka.Dubi irin wahalar da nake sha amma fatan ka na haihu ka rabani da ɗana,saboda ka faranta ma matarka.Wai shin ita ce mace kaɗai a duni..."

Wani irin hajijiya da take yi ya hana ta ƙarashe maganar sai da ta ɗauki tsawon lokaci ta ce a wahale.

" Wayyo Mama na ƙara girmama lamarin uwa a raina,na san haƙƙin ki yake bibiyata tur da irin ƴa kamata wacce za ta aikata wani abu ba tare da sanin mahaifiyarta ba!Tur da ni kaicona da na yi miki butulci na yi aure ba tare da sanin ki ba.
A m ka ɗauki kukana ka tura ma Mama ta yafe mini ko na samu salama a makwancina."Ta ce yayin da idanunta ke rufewa muryarta na ƙasa-ƙasa.

" Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un!"A.m ya faÉ—a cikin tsananin tashin hankali yana jijjigata.
" Da gaske mutuwa za ki yi Juwairiya! Don Allah kar ki mutu wallahi ban aure ki don na kashe ki ba,ki buÉ—e idanunki Juwairiya ki tashi don Allah mai kike so na ce ma Mama da take zaman jiran ki?"

A.m ya ruÉ—e sosai jijjigata yake amma tamkar babu rai a jikinta.
Hawaye yake yi cikin tashin hankali a ransa yana tunanin dama haka mata ke haihuwa.

Yana tsaye a kanta yana jijjigata ya rasa na yi zuwa can sai ta buɗe idanunta, tana wani irin jijjiga kamar wacce ta kamu da tsinƙa-tsinƙa,sai jini ya fara zuba sosai kamar an buɗe famfo.

A.m ya miƙe daga jikinta tare da sakin wani iri ƙara ya ce.

" Juwairaaaaah!"

Kawai ya zube ƙasa babu numfashi.

TO MASU KARATU KU DAI BIYO NI KU JI YADDA ZA TA KAYA A TSAKANIN SU YAU BAN YI TYPIND DA YAWA BA,SABODA BA NA JIN DAƊI KU YI HAƘURI DA WANNAN ANA TARE.

KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI

SAKACINA KO HALIN MAZA

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY

TALLAH!TALLAH!!TALLAH!!!

INA ƳAN MATA DA MATAN AUREN DA SUKA SHAYAR SUKE SON MARTAR ƘIRJIN SU YA DAWO?

INA MATAN DA SUKE FAMA DA RASHIN ƘIBA KO INA A ƘAME?

MAZA GARZAYO KI SIYA INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO DA ƘIBA,MAGANIN AN RIGA AN GWADA KUMA YA NA DA AKYAU ƘWARAI.BARI IN GAYA MIKI YAR'UWA DUK WADDA TA CE MIKI MARTABAR ƘIRJINKI,ZAI DAWO MATUƘAR JIKINKI BAI MURJE BA,TO GASKIYA KUƊIN KI KAWAI ZA TA CI.

IN HAR KINA SON MAGANIN YA YI AIKI A JIKIN KI SAI KIN DAURE,KIN SHA SAFE DA YAMMA.SANNAN MUNA AIKAWA KO INA SIYAN NAGARI MAIDA KUÆŠI GIDA.

MAGANIN AKAN FARASHI MAI TSAUƘI IN KINA SO MAZA GARZAYO KI KIRA WANAN NUMBAR ( 07088268243) KO (08144072423)

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND COMMENT.

SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 37*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Zainab da ke kwance ta miƙe cikin tashin hankali jin ƙarar A.m ta ruga ɗakin da gudu.Abin ta gani ya yi matuƙar razana ta,ɗora hannunta ta yi aka tare da sakin ihu,saboda ta rasa me za ta yi.

Girgiza sa ta fara yi tana faÉ—in." A.m ka tashi don Allah kar ka mutu ka bar ni!Ka san ba zan iya rayuwa babu kai ba."

Ta kalli Juwairiya da take cikin wani hali gani ta yi kamar babu rai a jikinta,sai jikinta ya kama rawa ta rasa baƙin ciki za ta yi?Ko akasin hakan.

Dabara ta faÉ—o mata ta ruga da sauri ta ibo ruwa ta watsa masa.

Buɗe idanunsa ya yi da sauri tare da miƙewa ya kamata kamar zai ɓallata ya ce." Ina Juwairaaah ta mutu ko?"

Zainab da ta kasa magana idanunta ta kai gurin da take kwance rai kwakwai mutu kwakai.

Da sauri ya bi in da ta kalla da idanunsa sai ya miƙe zubbur ya nufe ta ya ɗauke ta zai fita da ita.

" A.m dare ya yi fa yanzu ina zaka kai ta?"

Ta yi masa tambayar da ko kallonta bai yi ba ya fice,ba ta ankara ba sai jin tashin motarsa ta ji ya fice da ga gidan.

A.m da yake tuƙi cikin tashin hankali Allah ne kawai ya kai shi asibitin.

Ba tare da ɓata lokaci ba likitoci suka rufu a kanta,wacce ba ta san halin da take ciki ba.

Jikinsa har rawa yake yi wani irin tashin hankali ya ziyarce shi,ji yake kamar zai yi hauka,domin ya rasa asarar babyn É—insa ne bai so ya yi,ko halin da take ciki ya saka shi cikin wannan halin.

Wayarsa ya zaro a cikin daren ya kira A.k ya fi sau goma sai dai bai É—aga ba,sannan ya kira iyayensa ya sanar musu.

Ya yi shiru yana tsaye a gurin ɗakin da aka kwantar da ita sai leƙe ta windo yake yi,amma duk iya ƙoƙarin da likitocin suke yi ba ta farfaɗo ba,sai ya duƙar da kan sa yana jin tsananin tausayinta,yayin da hawaye yake bin ƙuncinsa.

" Na shiga uku! Yanzu in yarinyar nan ta mutu ya zan yi?"

Ya tambayi kan sa cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa.

Salati ya ji tana yi cikin murya ƙasa-ƙasa sai kawai ya danna cikin ɗakin ya durƙusa a kusa da gadonta ya kama hannunta ya riƙe.

" Juwairiya ina son ki!Ina son ki!! Ina son ki!Kamar yarda kika faɗa mini na maimaita miki,na roƙe ki don Allah kar ki mutu ki bar ni wallahi ina son ki,ban san cewa son ki nake ba sai yau da na ga za ki mutu ki bar ni.Na haƙura da baby kar ki mutu don Allah ki tashi zan rayu da ke ko da ba za ki ba ni baby ba."
Cikin wata irin murya yake maganar yana ji kamar ciwon ya dawo jikinsa,ganin yadda take shan wahala matuƙa.

Juwairiya ta buɗe baki za ta yi magana amma sai wani irin nishi ya hana ta,ta rufe bakin da sauri tana salati a ranta,don ta sadaƙar mutuwa za ta yi,wannan nishin na cire rai ne.

Kawai sai suka ji kukan jariri yana ta tsala kuka sosai duk ya cika asibitin da ihu.

A.m ya saki hannunta da ta rufe idanunta jin wani irin ciwo ya ta so kamar ba ta haihu ba.

Ya kai hannun da sauri zai ɗauki babyn yana faɗin." Alhamdulillahi adada ma khalaƙa."
Da sauri wata nurse ta riga shi ɗaukar babyn,sai ya duƙa ƙasa yana jin kamar an yi masa bishara da gidan aljanna.

" Doctor Marwan ina ga kamar Æ´an biyu ne za ta haifa da wani jariri a cikinta."

Doctor Bilal ya faÉ—a cikin razana ganin ciwo ya koma sabo.

" Anya kuwa ba na tunanin haka saboda scanning É—inta ya nuna mana yaro É—aya."Ya ba shi amsa da shakku a fuskarsa.

Tun suna tunanin cewar mahaifa ce za ta biyo har suka yadda Æ´an biyu a cikin.

Ganin irin wahalar da take sha A.m kuma kamar zai zare kamata ya yi ya riƙe,sai murna ta koma ciki.

Likita ya bada umurnin a fitar da shi saboda yana ɓata musu aiki,duk lokacin da ya ga sun danna cikinta ta saki ƙara mai razanarwa,sai ya ware zai bugi likitan.
Chapter 84 · 0% Book details