Sashe 61
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da ya shiga cikin ɗakin sa sai ya gwammace gara ɓarnar falo da ta yi akan na cikin ɗakin,saboda duk wani takaddu na shi na amfani sai da ta yaga su ta yi mi shi ɓarna sosai.
Tsayawa ya yi da mamaki yana kallon ta tsoro ma ta ba shi,ganin yadda ta wargaza gashin kanta ta zama kamar wata mahaukaciya.
Tashin hankalin da yake ciki yasa ya kasa tambayarta abin da yake faruwa,duk da zargi da yake yi akan ta gane komai.
Zainab ta ƙaraso gurin sa cikin tashin hankali,ta shaƙe shi idanunta sun canza kala,tsabar kishi cike a idanunta ji take kamar ta kashe shi,kawai ta huta domin ya cuce ta.
" Munafuki azzalimi mayaudari yau Allah ya tona asirin ka,dama amanata kuke ci kamar yadda Lantana ta faɗa min ka ƙarya ta?
A.m É—anka kake son ya fito ta zina ?Ba na haihuwa mai ya haÉ—a ka da maganin É—aukar ciki da wuri."
Duk da cewar ya ji maganar ta dake shi amma sai ya sauke ajiyar zuciya da ya tsaya iya nan ta sani.
" Zainab ki fahimce ni wallahi ba na zina kuma ba zan taɓa yi..."
"Rufe min baki mazinaci kawai? Yau Allah ya tona asirin ka na gama yadda da kai.Ni da ba haihuwa nake ba,in fact ba ni da mahaifar da zan ɗau ciki kake shan ƙwayoyin ɗaukar ciki da wuri."
Ta ja numfashi da sauke nauyayyar a jiyar zuciya,tana gumurzun kuka gaba ki É—aya ta fita hankalin ta.
A.m da ya rasa abin yi ƙarasawa kusa da ita ya yi yakai hannu zai taɓa ta,da sauri ta janye jikinta tana mishi wani wulaƙantaccen kallo.
" Ni Allah ya tsare ni na ƙara barin ka taɓa ni da hannun zina ai..."
" Zainab!"
Ya katseta cikin ƙaraji sannan ya nuna ta da ɗan yatsa." Kar ki ƙara kirana da mazinaci in ba haka ba jikinki ne zai gaya miki."Ya ce cikin ɓacin rai.
" To meye kai in ba mazinaci ba ko fasiƙi kake son na ce maka,wallahi na tsane ka ba na son ko kallon mayaudariyar fuskar ka,dole ka sake ni ba zan zauna da mazinaci ba."
Ta ce tare da ƙara cikwikwiye shi sannan ta ɗora da cewa." A.m yar aikina fa kake nema!Na shiga uku Juwairiya ƴar matsiyata mai take da shi wanda ba ni dashi?"
Girgiza hannunta yake yi akan ta sake shi,ya fara magana da muryar sa da yake sace mata zuciya,amma sai ta ɗaga mishi hannu dare da daka mishi tsawa,kamar wani ƙaramin yaro tana masa wani mugun kallo.
"Sake ni na ce ka bani takadda ta kuma na rantse maka,sai na maida Juwairiya kalar da duk wani É—a namiji ya ganta ba zai yi sha'awar ta ba.Ai ni ka gama tsara ni da kalamanka na yaudara matsiyaci kawai."
Ƙwace jikin shi ya yi yana hararar ta ji yake kamar ya kai mata bugu,ganin ta ƙara masa tashin hankali.
" Ki san maganar da za ki gaya mini mijinki ne, ni in har kika ƙara zagina zan miki hukunci,yanzu jikinki zai gaya miki ba tare da na yi nadama ba."
Ƙara cakumo shi ta yi ta kama gaban rigar sa ido cikin ido ta ce."Na faɗa kuma abin da ya fi haka zan faɗa banza mai zan yi dakai sake ni na ƙara faɗi mazinaci ƙazami!"
Mari ya kai mata amma sai ta goce da sauri tare da fisgo rigar shi,ganin ya na son ya fita a ɗakin ta kama ta sai da dire ta har ƙasa.
Duka ya kawo ma hannunta da ƙarfi ta saki jikin shi tare da sakin ƙara,amma kuma sai ta yi kukan kura ta kama shi da dambe.
A.m da yake jin zuciyar shi a wuya ba tare da tunani ba,ya shiga jibgar ta kamar ya samu jaka don iya ƙarfin sa yake dukan ta.
Da fari ta biye mishi tana kokuwa da shi,amma da ta ji kasheta zai yi,da gudu ta ruga É—aki ta É—auko gyale sai gida.
A.m ya durƙushe a gurin cikin nadama tare da kai ma bango naushi." Tabbas na gasganta cewa ke ɗin ba alkhairi ba ne a rayuwata!Juwairiya na tsane ki kuma wallahi sai kin yi nadama sosai,don sai na illata rayuwar ki yadda kika sa na doki matata mafi soyuwa a gare ni."
Juwairiya da take jin rashin ƙarfin a jikinta,amma haka take gudu don ta tseratar da rayuwar ta,saboda yau ta ƙara gasgantawa A.m ba shi da imani kashe ta zai yi.
Hawaye yana zuba a fuskarta da ta tuna irin tashin hankalin da A.m ya shiga,saboda jin ta zubda ciki nan take tsananin nadama ya shige ta sosai.
Tsayawa ta yi cikin tashin hankali ta rasa in da za je,gidan Hauwa ya faÉ—o mata a rai sai ta tari É—an mashin.
Tana shiga ta rungume Hauwa da ta fito daga cikin É—aki jin muryarta tana kuka.
" Juwairiya lafiya mai ya faru?"Ta tambaye ta cikin tashin hankali.
" A.m ya yi fushi da ni na shiga uku! Wallahi ya tsane ni baya sona!"Ta ce tare da sakin wani irin kuka.
" Don Allah ki daina kuka ki yi mini bayani mai ya faru."
Ganin ta kasa magana sai kuka take na fitar hankali.
Zaunar da ita ta yi sannan ta ba ta ruwa tasha sosai ta kama hannunta ta riƙe." Don Allah ki gaya min mai ya faru."
Zubbur ta miƙe tare da ɗaukar hijabinta.Hauwa ta riƙe mata hannu ta ce." Wai mai ke faruwa ina A.m ki sanar da ni."
" Gurin A.m za ni ya yi fushi da ni ya gane na zubda ciki,don Allah ki zo mu je mu bashi haƙuri,wallahi ba zan iya rabuwa babu shi ba,don ina son sa."
Da takaici ya ishi Hauwa tsaki ta yi ta kamata tare da zaunar da ita akan kujera." Ba na son shashanci kin san ba kya son ki rabu da shi,kika zubda cikin da yake so?Babu yadda ban yi da ke ba,amma da yake kunnin ƙashi ne dake kika ji ƙi.Na rasa yadda zan yi ba kya jin magana haba ya kamata ki fahimci mai kike yi."
Share hawayenta ta yi ta ce." Zan je na ba shi haƙuri ba zan ƙara zubda cikin ba,in dai haka zai saka shi farin ciki,amma ki je ki ba shi haƙuri don Allah."
Hauwa ta yi shiru ta na jinjina lamarin domin sam bai yi mata daÉ—i ba,ta san da ma in dai A.m ya sani gakan zai faru,gara da ya sani ya É—auki mataki.
" Hankalina ya tashi sosai baki ga irin fushin da ya yi ba ,na san cewa ba zai taɓa nema na ba,gashi garin neman gira na rasa rasa ido.Na san ayanzu ya tsane ni ba ya son ganin fuskata.
" Rashin É—aukar shawara irin na ki shi ya ja miki,Juwairiya ya kamata ki gane gaskiya.Ni dai yanzu shawarata kar ki ce zaki koma gurin sa saboda ya yi fushi dake mai tsanani."
Ta ce tana kallonta da takaicin abin da ta jawo ma kanta,sannan ta ci gaba da cewa."Yanzu kin ga ba ki da lafiya ki ci abinci kisha magani,ni na san da zarar A.m ya huce zai neme ki don lamarin ku sai ku."
Ta faɗa tare da miƙewa ta nufi kicin bayan ta rufe ƙofarta da key,saboda a take-taken ta za ta iya fita ta je gurinsa.
A.m ya daɗe a ɗakin yana zaune tamkar mutum-mutumi,gaba ki ɗaya ran sa ya ɓace da abin da ya faru,duk sai ya ɗauki laifin komai ya ɗora akan Juwairiya.
Wayar sa ya fara dubawa don ba zai ce ga in da take ba.Sai dai ya gwammace dama faÉ—uwa ta yi kan yadda ya ga Zainab ta mai da wayar.Sai ya É—auki key É—in mota ya fice gidan A.k.
A.k na kwance a falonsa yana ya É—ora yaron sa a kan ruwan cikinsa yana mishi wasa.
A birkice ya shigo fuskar sa babu walwala ji yake kamar ya É—ora hannu aka ya yi ta ihu.
Zama ya yi ba tare da ya tanka ma Matar A.k da ke tsokanar shi ba,ganin haka sai ta ja bakinta ta tsuke.
A.k ya matso kusa da shi tare da dafa kafaɗun sa." Lafiya mai ya faru."Shiru ya yi zuciyarsa kamar za ta ƙone sai tafarfasa.
"Mu je cikin falonka ina cikin matsala A.k wallahi na rantse da zan ga Juwairiya ni ne a jalinta."Ya faɗa da ƙarfi cikin ɓacin rai.
Da sauri ya ja shi suka shige falonsa har da saka key.
A.k da ya yi shiru kamar ruwa ya cinye shi cikin tsananin mamaki yake kallon sa,domin lamarin ya girgiza shi.
" Yanzu kana nufin Juwairiya ba ta gidan,ina ta tafi na san dai ba za ta je gidan Baba Sani ba,sannan Zainab ta yi yaji yanzu lamari ya ɓace."
A.m ya yi ƙuta ya ce." Ina zan san in da take wallahi yarinyar nan ta ɓata min lissafi komai ya rikice,ban san wace hanya zan bi na shawo kan Zey,don ta yi fushi sosai,in da Allah ya taimake ni ba ta gane ta yi ɓari ba,saboda ba ta tuhume ni akan haka ba.Ina ji ina gani ta yi min asarar babyna abin da na daɗe ina nema."
Sai ga hawaye shar a fuskar sa ya na jin tsananin baƙin cikin asarar da tayi masa.
Wayar A.k ya fara ringing da sauri A.k ya kalle shi ya ce." Daddy ne yake kira kuma ina ga kai yake nema tun da kace Zainab ta fasa wayar ka."
Gaban A.m ya faÉ—i da ido ya nuna masa da ya É—aga wayar.
A.k ya danna wurin amsawa tare da saka sifikar wayar.
" Ina abokin ka yake dama ya fara hauka ne?Ƴar mutane zai daka kamar ya samu jaka,maza ka taho da shi zaku gane baku da wayo tun da kai ba za ka iya ba shi shawara na gari ba."
ÆŠif Daddy ya kashe wayar ba tare da ya ji mai A.k zai ce ba,don ya san suna tare da A.m.
Shiru suka yi kamar ruwa ya cinye su ko tari babu wanda ya iya yi.
A.k ya kalle sa da takaici yana gani duk shi ya janyo komai,haba ka auri mace ka ije wa matar ka,amatsayin Æ´ar aiki abin ya yi muni kuma babu tausayi a ciki.