← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 86

Sashe 34

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juwairiya ta haye mashin jikinta babu karsashi hawayen fuskarta sun ci gaba da kwaranya yayin da É—an mashin É—in ya fara tafiya a kan titi.
Wani ƙarin abin da ya ƙara zubar hawayenta cikin ƙunar rai da ta tuna yau gidan mijinta za ta akan mashin da ƙullin kaya a jaka, ba tare da an kawo mota kamar yadda ko wace mace mai gata wacce mijinta yake son ta ake mata,duk lokacin da ta tuna wannan sai ta ƙara sakin kuka har ɗan mashin ɗin ya juyo ya kalle ta ya na faɗin."
Lafiya Hajiya?"

Amma ba ta kula shi ba kuka sosai take har suka isa gidan Atine,a lokacin da ta isa ba ta nan sai da ta jira ta sannan ta dawo sallah ta yi suka kama hanya.

Wani irin faɗuwar gaba take yi har sai da ta dafe ƙirjinta.Kasancewar a kwai tazara sosai da gidan Atine sai da suka hau nafe.

A lokacin da suka iso ƙofar gidan da Juwairiya ta saka a ranta na A.m ne hankalinta ya yi matuƙar tashi matuƙa gaya.Kawai sai ta ji ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba ta sani A.m suna da kuɗi amma ko kaɗan ba ta taɓa tunanin haka gidan sa yake ba.

" Dole ka ce baka sona kuma ba zaka taɓa sona ba saboda ba mu dace ba ni kai na sheda ne."

Ta furta cikin karayar zuci don ta san ya fi ƙarfinta na har abada.Gaskiya fasalta gidan sa abu ne da zai ɗau lokaci saboda gida ne mai matuƙar girma, da tsari ga shukoki masu kyau waɗanda suka ƙara ƙawata gidan,don haka mai karatu na bar maka aikin tsara fasalta iya tsaruwan gidan,A.m a hannun ka don in na ce zan yi zan ɗauki lokaci ni dai na yi wa gidan suna da aljarnar duniya.

Lokacin da suka shiga cikin falon Juwairiya ku san neman numfashinta ta yi ta rasa, don barazanar shiÉ—ewa yake yi saboda tsaruwar falon da ke É—auke da ku san set huÉ—u na kujeru mabambanta.

Duk lokacin da ta ƙara taku a cikin falon zuciyarta karaya take da son A.m da ya shige zuciyarta saboda ta haƙiƙance ma kanta da yaudarar kanta take yi A.m babu abin da zai yi da ita.

A ƙasar kafet ɗin dake zagaye a tayas ɗin da ya sha guga ya na ta ƙyalli da ɗaukar ido ta zauna tare da rintse idanunta,hakan ta ji ba ta son idanuwarta su yi tozali da matar A.m don ta san zuciyarta za ta buga.

Atine ta zaro wayar ta ta yi kiranta sai dai cikin takaici ta ije wayar ta kalli Juwairiya ta ce." Ba ta dawo aiki ba amma ta ce mi jira ta za ta duba patient ta dawo."

Sai Juwairiya ta sauke idanunta daga kallon Atine saboda kiran sunan ta da ta yi,ta ci gaba da kallon ƙasa yayin da zuciyarta yake bugawa tamkar za ta fito.

Kusan waya biyu suka shafe suna zaune a falon sai kowa shiru jefi-jefi Atine take sakin tsaki,amma Juwairiya iya tsawon lokacin ko tari ba ta yi ba sai sautin bugun zuciyarta da yake ta ƙara tsanantuwa.

Ƙwas!Ƙwas!!Ƙwas!!! Suka ji sautin takalmi wanda Juwairiya ta sadaƙar da matar gidan ce ta dawo,bayan iya tsawon lokacin da ta ɗauka ta shanya su zaman jiran ta kamar wasu dussa.

Bugun takalmin Zainab ya na tafiya tare da bugun zuciyar Juwairiya da take jin tamkar za ta fito,ta rintse idanunta ta na burin a ce ba Zainab ɗin ba ne take ƙoƙarin shigowa,domin tsoro ya bayyana a fuskarta sai take ganin kamar za ta gane dalilin shigowar ta gidan.

Koda ta shigo waya take yi zama ta yi ba tare da ta ce musu komai ba ta ci gaba da wayar ta.

Juwairiya ta kasa ɗago idanunta ta ga matar mijinta na wucin gadi wanda take cikin zuciyar sa yake fifita ta fiye da komai har ya zaɓi ya cutar da rayuwarta duk akan ya farnta mata.

Amma idanuwanta sun kasa haÉ—a ido da ita hasalima ko É—agowa ba ta yi ba, duk da ta fahimci ta gama wayar da take yi bayan ta É—auki rabin awa.

" Am Atine na ɓata miki lokaci ko?"

Tambayar da ta yi mata kenan ta na kallon matar da ta kusa jika da ita a yatsine.
" Ba komai Hajiya dama me aikin ne da muka yi magana da megidan ki na kawo miki."Ta ce mata ta na kallonta.
" Ok."

Abin da tace kenan ta janyo wayarta ta kunna data yayin da tsaƙwanni suke ta shigowa ta na duba wayar har na tsawon lokaci,daga bisani ta kashe ta kalle su duka daidai lokacin da Juwairiya ta yi sa'ar yaƙar idanunta, na tsoron haɗa ido da ita da suke ta kalle ta, don ta ga wannan mace mai ji da kanta da wulaƙan ta mutane.

Karab idanun su duka suka haɗu da juna Juwairiya da ƙyar ta yi nasarar daƙile gangar jikinta da yake shirin tashi da zura da gudu ganin kalar matar da A.m yake aure.
" An ya Æ´ar Nigeriya ce?"

Ta tambayi kanta cikin tsananin mamaki domin yanayin ta da kyanta surar ta gabaki ɗaya ya tsorata ta,saboda hasken ta har wani kashe ido yake yi sosai da ta yi duba ga kalar fatar jikinta sai ta ga ta yi baƙa wuluk kamar gawayi,duk da ya ba kyan fatarta da ƙawayenta suke yi.

Zainab kuwa wani irin tsanar ta ya shiga ranta haka kawai sai ta ji ba ta kwanta mata ba,ba wai kuma kyan da ta gani ba ne ya tsorata ta a'a ita sheda ne akan A.m ko ƴan mata larabawa za ta kawo mishi ba zai yi dubi garesu ba, duba ga yadda ta sha wahala kafin ya amince da ita sannan tun da su kai aure ba ta taɓa jin ya yi maganar wata ko wata ta kira shi ba.

Amma sam Juwairiya ba ta yi mata ba saboda daga ganin ta za ta yi munafunci ganin yadda take duƙar da kanta ƙasa-ƙasa.
" Atine an ya wannan ƴarinyar kina ganin ta yi?Kin san A.m a kwai shi da ƙyanƙyani ji yanayin shigar ta da wani zumbulelen hijabi kin san ya na da tsafta, kar ta zo ta na ma na girki ya na shiga sannan wallahi zubin ta bai yi min ba don ni na daina ɗaukar ƴan aiki gidahumai ƙauyawa,bai gaya miki ɗakin sa da komai na shi ita za ta din ga gyarawa ba?A can zo wata kawai."

Juwairiya ta yi ƙasa da kanta jin abin da ta faɗa duk da ranta ya ɓace,amma ta yi tunanin fiye da hakan a gurin ta saboda ta karance ta tsaf mace ce mai ɗagawa da nuna ta isa,musamman ga talakawa ƙasƙantu irin ta.

Sai kuma ta ji daɗin abin da ta ce ranta ya yi fari ko banza ba za ta zauna agidan wannan mai kama da canis ba sai ya zo ya san yadda zai yi da ita,ai dama abin da ya shirya a yi mata kenan shi ya sa ya aure ta ya kawo ta kuma ita ta sai ma kanta don in da ƙwaɗayi a kwai wulaƙanci!

Atine ta ji jikinta ya yi sanyi sosai har ta fara tunanin in da za ta samu kuÉ—in A.m ta mayar masa don ya na ba ta ta kai ma mai kujeru akan bikin Æ´arta marainiya wanda mijinta ya mutu ya bar mata.

Sai ta ji kamar ta ce ai mijin ta ne ma ya buƙaci ta kawo ta,amma da ta yi tunanin ba ta san dalilin da ya sa ka shi ya buƙaci hakan ba sai ta kama bakinta ta guntse ta ce." Ai Hajiya Juwairiya a kwai aiki da tsafta sosai ta yi aiki da dama shi ya sa na kawo ta,kuma za ki ya ba sosai sai kin gode min,amma ki gwada ta in ba ta yi miki ba sai a kawo wata.Kin sai an gwada akan san na ƙwarai.

" In ko haka ne ta na buƙatar gyara don sai na canza mata tufafi ba za din ga mana girki da shi ba,ni ban san daƙiƙanci da rashin wayewa."

Ta ce ta na kallon Atine da ta yi hamdala a ranta jin ta amince da ita,sai kuma ta kalli Juwairiya ta na mata kallon tsaf irin na ciki da waje har mutum ya gano munin ka.

" Ina yini"

Juwairiya ta ce mata ganin ta na mata kallon ke ba kya gaisuwa ne.

ÆŠauke idanunta ta yi ba tare da ta amsa gaisuwar ba duk da ta tabbata ta ji gaisuwar da ta yi mata.
Sai ta miƙe ta kalli Atine ta ce."Wash na gaji ba ri na shiga ciki."Har ta fara tafiya sai ta tsaya.
" Ina fatan Atine ta yi miki bayanin aikin da za ki din ga yi a gidan nan? Ina da da tsohuwa da take share-share da ƴan abin da ba'a rasa ba.So ke aikin ki kula da ɗakina da na mijina da wankin underwears ɗin mu da girki.Kasancewar ba zama nake ba don yanzu waje zan fara fita na baki amanar gidana, da mijina duk sanda ba na nan ki rinƙa kula da abincin sa ruwan wankan shi kayan sawan shi da wanda ko ina nan ke zaki kula da wannan."

Ta ɗan numfasa ta ɗora da ce wa " Game da kayan sawar shi irin wanda yake so ina fatan ke ba daƙiƙiya ba ce kuma ba' a yi asaran tara ba na yi mishi time table a ɗakin sa na kayan da yake saka wa sai ki din ga dubawa ki na cire masa."

Wani iri Juwairiya ta kanta ya yi mata take wani irin zafin kishin mijinta A.m ya taso ya mamaye zuciyarta,har ya hana ta jin abin da Zainab take ce wa sai kuma tausayin sa ya kamata matuƙa jin irin ballagar mace da yake aure.

Ta ƙara rintse idanunta ta na jin kishin iya adadin masu aikin da Zainab ta yi waɗan da suka gama kallon mata miji,kuma a haka yake iƙirarin ya na sonta lallai ta yadda so halitta ce kuma makaho ne.

" Ki na ji na ina magana kin yi banza da ni!"

Zainab ta daka mata tsawa ganin ta tafi duniyar tunani.
Chapter 34 · 0% Book details