← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 86

Sashe 13

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai fito ba ya na karatun kur'ani har kiran sallar isha ya tafi masallaci,sannan bayan ya yi sallah ya dawo ya zauna a falo shi da yaransa suna kallo shi kuma ya na aiki a laptop É—in sa.
"Abnaj je ka kira min Antyn ka Juwairiya kace ta zo ta bani abinci."Yace mishi ba tare da ya kalle shi ba,burin sa ya ganta ya san ta ɓoye kanta a ɗaki don kar ya ganta.

Yaron ya ruga da gudu zuwa can ya dawo yace."Ga ta nan zuwa."Ya ci gaba da kallon sa bata jima ba ta fito da dogon hijabin ta har ƙasa.Ita sai yanzu dake matuƙar dana sanin gadin mijin wata da yaran ta da take,don a a kwai haramcin haka a cikin addini mace baliga da namiji ba muharramai ba dama na ukun su sheɗan ne.

Nesa da shi ta tsaya kamar za ta yi mishi magana sai kuma ta juya ta shige kicin ta É—auko abincin shi ta ije mishi za ta juya."Ba kiji ba Juwairiya."Yace da ita ganin za ta shige É—akin da take kwana har ta na haÉ—awa da gudu-dugu.

Tsayawa ta yi bata re da ta juyo ba ta na watsa da yatsun hannunta gani take kamar zai haiƙe mata kamar yadda ƙanin mahaifinta ya yi mata,amma sai ta ga ya ƙaraso ya tsaya ɗan nesa da ita ya miƙa mata sabuwar waya mai kyau a kwali ya ɗan daure fuska."Ga shi na ji Antynki tace Abnaj ya saka miki waya a ruwa ta lalace shine na hutar da kuɗin ta,amma fa ki kiyaye ki dai na basu don nan gaba in kika bari suka lalata sai na haɗa da bulala kafin na canza miki wata."Yace ya na kashe mata ido.
Zare ido ta yi ganin wayar da ya siya mata irin wanda take gani a hannun su masu kyau da tsada,ina ita ina wannan wayar ta na Æ´ar gidan Malam Shehu kuma me za ta ce ma Anty Naja."

Kamar ya san me take tunani sai ya kaɗa kansa yace."Karki damu na san me kike tunani zan yi mata bayani.Kuma ba ni da nufin na cutar dake alkhairi ne zuciyata,don Allah ki karɓa kin san babu kyau mai da hannun kyauta baya."Yace da ita ya na wani marairaice fuska sai kace maraya.

"Gaskiya ka bar shi bana so ina gani a matsayina na ƴar aiki bai kama ta na riƙe irin wayar nan ba,don daga ganin ta na san za ta yi tsada kuma in Anty Naja ta gani me zan ce mata?"Sai ta tsinci kanta da furta hakan yayin da takai aya ta tsare shi da ido ta na tambayarsa.

Shi ma ya É—an razana jin tambayar da ta yi mishi kansa ya É—an sosa ya kafe ta da idanunsa yace."Haba Juwairiya kina abu kamar ba mace ba,kice mata saurayin ki ya baki mana."

"Ka yi haƙuri don Allah ba na son kyakykyawar alaƙar mu da matarka ya ɓace,kai sheda ne mace ce na ƙwarai kuma ta yi min halacci."Tace dashi da murya raunanniya yayin da hawaye suka fara turereniya a fuskarta.
Ganin haka sai jikinsa ya yi sanyi ya É—an yi shiru ya na nazarin maganar ta zuwa can ya ja numfashi yace."Laifi ne don nace ina sonki ni fa bani da nufin na cutar dake,kawai ina son ki zamo uwar Æ´aÆ´ana ne."Tsananin tsoron da ta nuna ta na me gwalo ido sai abin ya ba shi dariya.

Tafe take cikin sauri bayan ta tashi daga aikin zuciyarta tunanin sabon halin da mijin madan ɗin ta ya fito dashi,yake damun ta har ta fara tunanin ko ta aje aikin ƙila in Anty Naja ta gane ba lalle-lalle ne ta fahimce ta ba.Kallon tsadaddiyar wayar dake riƙe a hannunta da ya bata take kallo wanda ya rantse ya maya in har ba ta ɗauka ba to zai ba wa Antynna ta da take tsoron sani ta bata da kanta.

Abin mamaki dai-dai za ta shiga gida ta ji an dameta da hon,kamar ba za ta juya ba sai kuma ta juya in da ta ga mijin Anty Naja a cikin mota ya na É—aga mata hannu,wato biyo ta ya yi ba tare da sanin ta ba ya ga gidan su.Tsabar takaici ba ta kula shi ba ta shige cikin gida.

Koda ta gaya ma Mama abin da ke faruwa hankalin Mama ya tashi ƙwarai ta yi shuru kawai ta na jinjina abin a ranta,ta ɗauki tsawon lokaci ba tare da tace komai ba zuwa can ta nisa tace."Ina ga ko haƙura da aikin nan tunna mun sami jari Juwairiya,ni nafi son kiyi aure shine mutuncin ki.Kin san maza basu da ta ido zai iya furtawa hakan ya jawo miki matsala gara mu yi rabuwar mutunci,in ban da shi ma ina ke ina kishi da Anty Naja mace me mutunci."
"Nima haka na gani Mama hankalina ya tashi ƙwarai."Tace da ita ta na juya wayar da ya ba ta."Kinga gobe ki mayar mishi da wayar shi,kice ni na ce ki mayar masa na tabbata ya tsorata ki ne amma ba zai yi gigin bata wayar ta baki ba,in dai ba ya na so ya kira ma kansa ruwa bane."
"To Mama in sha Allahu zan mayar masa,ni ma bana son na riƙe irin wayar nan don Allah kaɗai ya san abin da Baba Sani zai faɗawa jama'a."
"Haka ne Allah ya fishi."Ta bata amsa tare da miƙewa don ɗauro alwalar kiran sallar magariba da ke ta kwaɗawa masallacin kusa dasu.
Washegari da ta je gidan bayan fitar matarsa ya dawo kamar yadda ƴan kwanakin yake mata,ta na ganin shi ta ƙara tamke fuska kamar ba ta ganshi ba ta ji gaba da aikin ta.
Ta yi tunanin zai yi mata magana amma sai ta ji shiru na tsawon lokaci,da sauri ta waigo sai ta ga ita yake kallo kamar bai taɓa ganin ta ba.Miƙa masa wayar ta yi tace."Mahaifiyata tace na dawo dashi,kuma don Allah ka yi min rai ka fita sabgata domin ba za ta amince aci amanar Anty Naja ba."
"Ni kuma sai na shiga wani hali ko?Wannan dalilin ya sa kika ƙi ɗaukar wayata jiya da daddare sai ma kika kashe wayar.Dama masoyi ya na zama maƙiyi Juwairiya?"Ya ƙarashe maganar da sigan tambaya,a yadda ya furta maganar sai ta ji ranta babu daɗi,ganin namiji mai natsuwa ya na mata magiya akan ta so shi.

Wani irin abu ta ji a ranta in da ace matarsa ba ta shiga tsakani ba,babu yadda za'ai taƙi auren shi sai dai ba za ta zama butulu ba.Ganin taƙi kallon sa bare ya saka ran za ta yi magana,sai ma hawaye da ta soma ganin haka ya ɗauki wayar da ta ije mishi ya fice ya san ta na sonshi,amma tsoro ne ya cika mata zuciya in ko haka ne zai je har gida ya nemi aurenta.

Kwana biyu haka suke wasar ƴar ɓuya ganin haka sai ya dena shiga sabgar ta ko dawowa gida ya dai na,ya na shirye-shiryen zuwa gidan su ya nemi auren ta.
Ranar wata yammacin talata ta tashi daga aiki kasancewar an yi rana sosa,da yake lokaci ne na damina garin ya fara haɗa hadari.Juwairiya sauri take ta isa gida saboda ta kauce ma baƙin hadarin da yake tasowa ya na canza garin da yake duhu sosai.
Hon ta ji an danna mata ta waiga sai ta ga Daddyn Abnaj ne ya na mata murmushi yace."Maza shigo na kaiki gida kar ruwa ya zane min masoyiyata."Ta yi kamar ba za ta shiga ba amma ganin har an fara iskar hadari ya sa ta buɗe gidan baya ta shige,tare da haɗe girar sama da ƙasa don karya tambayeta dalili

Hakan sai ya ba shi dariya sosai bai ce komai ba suka fara tafiya, sai ya sai ta madubin motarsa dai-dai in da take zaune."Wato na zama direban ki ko."Ya jefa mata tambaya dai-dai lokacin da ya fara tafiya.
"Ina wuni."Tace ba tare da ta amsa mishi tambayar ba.
"Ba zan amsa ba ina fushi."Yace ya na kallonta ta gilashin motar.
Ba tace mishi komai ganin hakan ya sa ya fara magana da murya mai taushi."Matsalar ƴan mata kenan da kun ga namiji ya na ƙaunarku,shikenan kun samu zaren ja amma babu komai nima lokacina ya na nan zuwa,don na fara hango sona a cikin ƙwayar idanunki."
Ta ɗan saki ranta saboda ta fara sabawa da shi ya wan janta da ɗawainiya da yake musu ta ja numfashi ta sauke ta fara magana da cewa."Ku kuma maza ba amana ka san kusancin dake tsaƙanina da matar ka,amma ka bijiro da wannan lamari haba kai ma ka auna ka gani bai dace ba."

"Kija min aya da ya hana hakan ko hadisi."Ya faɗa a raunane kuma a taƙaice.Babu amma Bahaushe ya na girmama al'adarsa hakan ya saɓa ma al'adar Bahaushe."Sitiyarin motar ya buga da ƙarfi yace "Kin ji ko in da karatun naki ya tafi ina miki zan can addini kina yi min wata magana can,kawai na gane bakya sona ki ce na haƙura kina da wani hakan zai sa na bawa zuciyata haƙuri duk da na san za ta shiga wani hali."

Yanayin da ya yi maganar sai ya bata tausayi amma ta san abin da yake so ba mai yiwuwa ba ne.Murfin motar ta ɓalle za ta fita ganin sun ƙaraso gida ya yi parking,sunan ta ya ƙira da wata irin murya.Ta waigo ba tare da tace ƙala ba,sai ƙasa da kanta da ta yi wato alamun ta na sauraren sa.
"Ki yi tunani zuwa ƙarshen sati nan nake so na turo magabata na,ina ganin za ki dakata da akin nan kafin kizo a matsayin ƙanwa kin ga sai ki ɗora daga in da kika tsaya ki na samun lada rututu!

Ɓalle motar ta yi ta fice dai-dai lokacin da ya miƙa mata ƴan rafar ɗari biyar kusan kimanin dubu ishirin ba tare da ta karɓa ba ta fice,musamman da ta ga Baba Sani tsaye a ƙofar gida shi da wani mutum ya zura mata ido.

Ganin jikinta ya soma rawa ya kalli in da take kallo,sai hakan ya yi mishi daɗi domin faɗuwa tazo dai-dai da zama,ya buɗe murfin motar ya fito ya nufi su Baba Sani dake kallon Juwairiya kamar ya shaƙe ta.
Chapter 13 · 0% Book details