Sashe 6
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannun Baba Sani ya sauka a ƙirjin Juwairiya tare da wasu tagwayen hawaye masu tsananin zafi da ƙuna a fuska.Ta jin wani irin tsananin tashin hankali a zuciyarta yayin da take ji a cikin zuciyar ta tamkar za ta haɗiye zuciya ta mutu."Da ma burin sa kenan a kai na ya hana rayuwata samun sukuni,kullum ya na bibiyata tare da daƙile farin cikina?Me na yi masa wanda ba zai iya ɗauke mugayen idanunsa a kaina ba,a matsayina na ƴar wansa wanda suka fito ciki ɗaya?Wayyo Allah ina ma ace ranar mutuwa ta ce aka nuna min ba wannan ranar mai baƙin gani da muni a cikin zuciya ta ba.Ihu ya kama ta na yi ya kashe ni kamar yadda yace ko na yi shiru ya ɓata min rayuwa?"Ta tambayi kan ta cikin tsananin ruɗani dai-dai lokacin da ta ji saukar hannun sa a hurumin da ba na shi ba.Sai ta rufe idanunta ta na kiran sunan Allah tare da karanto duk addu'ar ta da fito daga cikin bakin ta. Da sauri Baba Sani ya janye hannun sa daga ƙirjin ta tare da fasa abin da ya yi ninya,jin motsi daga waje."Sannu Malam ka yi a hankali jikin ka babu ƙarfi."Suka ji muryar mahaifiyar Juwairiya ta na magana cikin tausayi. Hankalin Baba Sani ya tashi sosai ya daɗe ya na dakon wannan ranar tun lokacin da Juwairiya ta fara girma ya saka kwaɗayin sa a kanta,gashi ya sami dama amma kuma kamar hakonsa bai cimma ruwa ba. Dai-dai saitin kunninta ya saita tare da raɗa ma ta."In kika yi magana sai na kashe ki."Hakan ya sa Juwairiya kame bakin ta ta yi shuru sai hawaye dake zuba a fuskarta. Ya tsorata iya tsorata ganin sun shige cikin bayin ya buɗe kofar ya fice cikin sanɗa,Juwairiya ta fashe da kuka tare da fita daga cikin ɗakin a ranta ta ƙudirta ba za ta ƙara kwana a cikin sa ba.Fitowar ta ya dai-dai da lokacin da suka fito daga cikin bayin.Faɗawa kan jikin Mama ta yi ta fashe da kuka ta na wani irin kuka mai ƙarfi da ta da hankali ba ta damu da daren da ya tsula ba.Cikin tashin hankali da tsoro Mama ta rungume ta ta na faɗin."Lafiyar ki ɗaya Juwairiya dare ne fa?Ko kin yi gamo ne."Irin tarin tambayoyin da take mata amma ba ta kula ta ba sai kuka da take yi mai ɗaukar hankali,ganin kukan na ta ba na ƙarewa bane Mama ta ja hannunta suka shiga cikin ɗaki lokacin Baba har ya shige ya kwanta,saboda gudawa da yake fama da shi ya kasa tsaya wa ya tambayi abin da ke faruwa. "Mai ya same ki lafiya?"Mama tace don zuwa yanzu kukan ya fara ba ta tsoro ta na ganin kamar Juwairiya gamo ta yi,yayin da ta wani gefen ta fara ba ta haushi bacci ne sosai a idanunta. Juwairiya ta kasa magana sai kuka haka Mama ta yi ta gaji ta koma ta kwanta yayin da ta barta zaune tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu. Washegari da safe Mama duk lallashin da ta yi mata akan ta gaya mata abin da ya faru,amma taƙi ƙarshe sai dai ta yi mata ƙaryar mafarki mara kyau ta yi.Mama ba don ta yadda ba ta ƙyaleta amma zuciyar ta ta na gaya mata a kwai ɓoyayyen lamari,kasancewar Juwairiya ba ta taɓa kasa kwana ita kaɗai ba.Hankalinta ya tashi musamman da Juwairiya tace mata ba za ta ƙara kwana a ɗakin ita kaɗai ba,sai dai a haɗa ta da Ibrahim wanda Mamma bata iya kwana sai da shi saboda ciwon sa,gashi ta na da mugun bacci.Duk da jikin Baba da ya kwana babu daɗi amma haka nan ya shirya ya fita bayan ya sha magani. Wunin ranar Mama ta kasa gane kan Juwairiya duk irin tarin tambayoyin da take mata,don ko ruwan koko da ta dama taƙi sha daga ƙarshe wani ƙarya sake yi mata tace ba ta da lafiya. ****** Gidan cike yake da mutane kai da gani kasan ana farin ciki a dalilin bikin ƴaƴan gata, ga kayan abinci da na tsotse-tsotse da a ke ta fita da shi.Bikin na yaran manya ne waɗanda duniya take hannun su kuma ta yi na'am da zuwan su duniyar,suke rayuwa a yadda suka tsara kuma suke ƙurɓar ruwan daɗi a cikin ta. Naira ta na tsala kuka tare da nai man taimakon agaji da son ɓoyeta domin ta adana kanta ga masu buƙatar ta.Ruwan kuɗi kawai yake tashi da jerin gwanon motoci wanda ba zasu irgu ba.Wannan biki ne wanda ya amsa sunan sa kuma ya buƙaci a buga a jarida,wato bikin Muhammad Dawood Turaki da amaryar sa Zainab Abubakar mai shadda.Waye bai san waɗaɗnan hamshaƙan masu kuɗi da samu rayuwa mafi ƙololuwar daɗi a gare su ba. Muhammad Dawood ɗa ne ga wani hamshaƙin mai kuɗi daga cikin turaki Family,wanda duniya ta san shi har da ƙasashen waje don ma yafi gudanar da harkokin sa a can.Tsarin rayuwar su irin na turawa da zallar boko.Gida ne na ƴanci da rayuwa babu taƙurawa da samun kwanciyar hankali.Suna da matuƙar kyau da asali mahaifin sa haifaffen garin Zariya ne.Ya gina katafaren gidan sa mai kyau a unguwar Zangon shanu,gida mai kyau na bene da tsari.Matan sa biyu Hajiya Khadija wato mahaifiyar A.m sai amarya Hajiya Binta Yaran sa bakwai Muhammad shi ne na farko wanda aka fi sani da A.m,sai kanin sa na miji sauran mata ne guda biyu sai kuma bangaren amarya ta na da uku.Suna zaman su lafiya kuma kan su a haɗe yake. A.m mutum ne mara daɗin sha'ani ga rashin haƙuri ga saurin ƙulewa,ba ka taɓa gane in da ya sa gaba shi kullum mutum a gurin sa bai iya ba kuma ba a yi mishi gwanin ta ba.Kannin sa suna shan faɗa shi ya sa basa ƙaunar ya zauna a gida in kayi magana,yace ka faye surutu in kayi shuru yace ya na magana an raina shi.Shi komai a gurin sa laifi ne sannan ba shi da fara'a ko wasa ba ya yi dasu.Faɗin halin A.m abu ne mai wuya domin ya na da murɗaɗɗen hali baka gane in da yasa gaba,wannan dalilin ne ya sa ba shi da wasu abokan sai A k wanda ya jure halin sa duk da wani lokacin shi ma hutsu ne,amma ya san yadda yake tafiyar da shi.Muhammad ɗan gata ne a gurin mahaifin sa ga shi fari kyakykyawa dogo mai aji da tsafta.Wan mahaifin sa Alhaji Sama'ila ya na matuƙar ji da shi domin a hannun sa,ya tashi ya ma fi Daddy sa kuɗi sai dai shi Allah bai ba shi haihuwa ba. Ya na matuƙar son yaga ya haihu saboda ya samu magaji har ƙasar waje ya kai matan sa uku a ka yi musu dashen kwai,amma Allah bai nufa cikin zai tashi ba,ƙarshe daga baya kan dole ya fauwala ma Allah lamuran sa ya na addu'ar Allah ya sa ya na da rabon haihuwa a duniya. Tun kafin a haifi A.m mahaifin sa ya yi ma Yayan sa alƙawarin ba shi duk abin da ya haifa,saboda haka ana yaye shi aka miƙa ma matarsa Karime.A.m ya taso cikin gata da shagwaba bai san damuwa ko a kasin haka ba.Duk karatun sa a ƙasar waje ya yi in da ya karanci (Economis)bayan ya kammala ya dawo gida Nigeria amma ba ya wata yake fita waje. Family ɗin Turaki mutane ne da ba ruwan su da harkan talaka ba sa hurɗa dasu,kuma ba sa shiga sha'anin su.A.m da ya tashi ɗauko tsanar talaka sai yafi kowa a cikin Family ɗin na su,don shi tunanin sa laifin sa ne da yaƙi tashi ya nema ya tsaya lalaci.Saboda mugun tunanin sa akan talaka ya sa ya tsani ma'aikatan gidan su kullum cikin hantara da mari yake musu laifi kaɗan zai kai duka,musamman masu aikin cikin gida. Zainab Abubakar ƴar gidan wani ɗan majalisa ne da yake tashe a yanzu kuma hamshaƙin ɗan kasuwa.Yarinya mai tashen kyau da ƙuruciya ta na ji da kanta tare da alfahari da kyan da Allah ya yi mata,ga ɗagawa da son nuna ita ma wata ce mai ilmi da kuma nera.Sannan ra'ayin ta yazo ɗaya da A.m na ƙin talaka ba ta da kirki sosai,amma in baka shiga sabgar ta ba ba zaka gane hakan ba.Zainab likita ta karanta a ƙasar indiya.Mahaifinta ya na ji da ita don ita kaɗai ya haifa,sukai hatsarin mota ya samu naƙasa ba zai ƙara haihuwa ba. Saboda haka yake ji da ita ba ya son ya ga ɓacin ranta komai take so shi take yi,gara mahaifinta ya na ɗan jan ido akan lamuran ta musamman shigar ta da ya tsana,amma mahaifiyar ta Hajiya Mariya ba ta barin ya tsawa ta mata a cewar ta in basu ba ta gata ba wa zasu ba. Zainab mace ƴar ƙwalisa da gayu ga ƙamshi a kwai son turare masu tsada da kamshi,ga son kwalliya ta na ɓata lokacin ta akan kwalliya ita rayuwar ta tafi ba ta hamimmanci akan kwalliya da charting,sai ta wuni ta na kalle-kalle a waya ko ɗaukar hoto.Kullum rana na duniya Zainab ta yi wanka sai ta ɗauki hoto ta yi posting ɗin shi ko da wankan kwanciya ta yi.Bayan kwalliya da take so a rayuwar ta sai waya ko da yaushe wayar ta ya na hannun ta. Wani lokacin mahaifin ta ya na tonon ta ya na kiran ta suna mai aljanar hoto ta na son ɗaukar hoto ta tura a Social Media a yi mata comment da liking a na zuzuta kyawun ta,ko ta ɗora a tiktok. Zainab mace ce mai son jiki da hutu duk da ba ta da ƙiba sai dai jiki na mata,amma a kwai son jiki ko waya a kace ta ɗauko sai tace wash!Ta miƙo ta na ya mutsa fuska ko alamar gajiya. A taƙaice ba ta cas ko as ɗakin ta kullum mai aiki za ta shi ga ta share,sannan mai wanki ta kwashi kayan ta hatta innerwears ɗinta,mai aiki take wanke wa ko al'ada ta yi sai dai mai aiki ta kwashe abin a bayi ta zubar sannna ta wanke.Ta na matuƙar alfahari da gatan da iyayen ta suka bata tare da yi musu addu'a.Mace sangartacciya mai son jiki da hutu da zallar wayewa mai ƴanci wacce rayuwarta a cikin fararen