← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 86

Sashe 45

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A.k ya kalli A.m da ya kasa ce wa komai ya ce da shi." Ka shirya zama da Juwairiya a matsayin yadda ko wace mace take a gidan aurenta ko har yanzu ka na kan bakan ka ku...?"

" Allah ya kyauta na zauna na har abada da gaiyar tsiya ai in wannan mara mutuncin ya na raye ba zan taɓa haɗa zuriya da su ba,kuma mai zan yi da gayyar matsiyata ba na son Juwairiya yaro nake son ta haifa min na saketa,sannan ba zan yi asarar kuɗina ba dole sai ta haifa min baby,wallahi ko dashe ne sai am mata don ba zan yi asarar kuɗina ba."

A.m ya katse A.k da yake magana cikin zafi da kakkausar murya mai hargowa.
" Kuɗin ka ne zai tafi a banza ka maida matsiyata masu kuɗi,dama ta hanyar wani Allah yake azurtawa ɗan ƙaruna,yanzu sai ka ƙaro kuɗi na shekarar ne ko shekara biyu,amma fa ka sani ba zan yadda Juwairiya ta zauna a cikin wannan daular ba,don haka sai ka shirya kawai ka je a farke mahaifarta ayi mata da she ta haihu kowa ma ya huta."

Ya ce ya na kallon A.m da jikin sa ya yi sanyi don yanzu yake nadama ashe tunanin halin sa ya wuce wannan.

Sannan ya ɗora da ce wa "Mahaifiyar Juwairiya ta taso ni kan sauran lokacin da ya rage Juwairiya ta dawo aure za ta yi mata,sosai ta yi min bore har ta na barazanar kai ni kutu ƙila tare za a kai mu ko kuma ka ba ni kuɗin da zan san yadda zan yi na kawar da idanunta kafin wa'adin ya cika."

Har zuwa lokacin shiru suka yi suna kallon juna da mamakon sa.

"A.m ka na jin abin da ya faɗa na fara shakku an ya mutum ne shi ko aljani? Allah ba shi da imani karfa ya zo ya ruguza komai,zan ji kunya sosai domin ni Daddy zai fi ba ma laifi don ban kasance aboki na ƙwarai ba."

A.k ya ce ran shi a ɓace ganin abin da suka yi cikin sirri ya na son ya fasu.

" Kyale matsiyaci ka ba shi kuɗi kawai don ba zan iya sakin Juwairiya ba matuƙar ba ta haifa min yaro ba,don ina son jinina ya fito ta tsatson ta tabbas ubanta mutumim kirki ne don ya ba ƴar sa tarbiya na ƙwarai,amma na san kai yaranka sai dai su ɗauki halin dabbobi don ba su yi dacen uba na ƙwarai ba."

Dariyar jin daÉ—i ya saki ganin ya ci galaba a kan sa ya ce." Allah ya sa karuwai za ka kira su ni na san halin su,kuma na san irin tarbiyar da na basu in dai kawai na ji bayani wato kuÉ—i abokan harka.In baka accourt numba ne ko cash za a bani."

Takaici ya hana A.m magana sai A.k ne ya kalli A.m ya dafa kafaÉ—ar sa ya na faÉ—in "Ka koma ciki kawai zan ji da shi."

Kamar ƙaramin yaro ya juya ya shiga ciki da ƙyar yake ɗaga ƙafafun sa ya na shiga falo ya zauna shaɓar, ya na jin wani ƙunci a ran sa abu ya haɗu ya tarun masa goma da ashirin.

Juwairiya ta fito daga kicin jin shigowar sa wanda ta ɗan ji hayaniya sama-sama,amma ba ta sheda abin da yake faruwa ba,asalima komawa kicin ta yi ta ci gaba da aikin ta don babu kyau laɓe.

Hannu ya miƙa mata ta iso gare shi janyo ta ya yi ta faɗa ƙirjin shi tare da matse ta da ƙarfi har sai da ta yi ƙara ya ce." Juwairiya ina cikin damuwa sosai abu ya yi min yawa.Zainab ba ta son farin cikina wai dama haka ne abin da kake so shi yake wahalar da kai?Tana amfani da son da nake mata ta na azabtar da zuciyata,ga Baba Sani ya zo ya ƙara min zafi."

" Baba Sani ya zo gidan nan na shiga uku."

Ta ce tare da zare jikinta daga gare shi ta zare idanunta don ta san zuwan shi ba alkhairi ba ne.

Kan sa ya ɗaga masa ya riƙe hannunta sosai." Yanzu ta tafi."Ya kwashe duk yadda suka yi ya gaya mata cikin rauni yake maganar.

Juwairiya ta yi shiru ta na kallon sa sai ya ba ta tausayi sosai juya mishi baya ta yi da nufin ta ce mishi ya bayyana auren su kawai,don ta gama kamar ya fara son ta da irin kashe ta da shaukin kala-kala da yake yi,amma sai ta ji muryar sa ya na faÉ—in.

"Juwairiya don kawai ina kwaɗayin na ga ƙwaina a duniya kuma ke ce mace ta biyu bayan Zainab da na ji zan iya rayuwar auren wucin gadi da ita,da ace zan iya zama da wata ba yan ke da zan rabu dake ne kawai saboda tantirin ƙanin mahaifin ki sam ba shi da mutunci,sai dai kamar yadda ba zan iya rabuwa da Zainab ba domin an halicci zuciyata don ita haka ba zan iya rayuwar auren wucin gadi da wata mace ba in ba ke ba."

Tasowa ya yi ya rungume ta ta baya kamar yadada Juwairiya take hawayen jin ya na faÉ—in zai iya rabuwa da ita hak shi ma ya fara hawayen rashin É—a.

Juyo da ita ya yi suka fuskanci juna dukkannin su hawaye na zuba fuskar su ya ce."Kin san na yi miki ƙoƙari Juwairaah don Allah ko da nine ba na haihuwa ki yadda na zuba kuɗaɗena ayi miki dashen mahaifa kin ga Zainab ita an yanke mata mahaifar."

Da yadda yake magana ya ba ta matuƙar tausayi sosai ta ƙara sautin kukan ta ta na ganin an ya ta yi masa halacci kuwa,duba ga irin abin da ya yi mata kuma sai da ta yi masa alƙawari karo na farko ta ji ba ta kyauta masa ba,don har ciki ta zubar wanda bayan ta sha lemun tsamin,amma har wata biyu bai zoba sai da zai zo ta ji ciwo sosai,sai dai shima bai yi ma zuciyarta adalci ba saboda ta na son shi ko idanunta ya isa ya isar mishi da tsaƙon hakan,amma ya yi biris da ita ko tunanin shi bai gane son shi take ba."

A tare suka fara tafiya kowannen su ya shige ɗaki domin samawa junan su maslaha daga halin ƙuncin da suke ciki.

A.k da Baba Sani ya sasha fama kafin Baba Sani ya amince ya karɓi kuɗin da ya ba shi,amma ya rantse in har lokaci ya ƙare zai zo ya ƙara karɓar wani kuɗi,kuma A.m ya sa a ran shi dole ya saki Juwairiya ko da ba ya so.

A.k ya yi shiru kawai ya na kallon sa har ya gama zuba mishi rashin mutunci ya tafi,a ran sa takaicin A.m yake yi sosai don shi ya jawo musi wannnan tashin hankalin,haba!A ce kana auren mace wani yazo ya yi maka iko da ita sai ka ce ya na zaman dadiro.

Ai dama duk abin da aka yi tare da son zuciya a kwai nadama a cikin sa dole mutum ya yi nadama, yanzu in da duniya ta san matar sa ne har wani banza ya zo ya maida su A.t.m É—in sa,to koma mene ne ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ka doka.

Sati biyu da Zainab ba ta nan Juwairiya ta yi amfani da damar ta koya mishi wani kalar kulawarta,wanda shi kan shi mamakin ta yake don yanzu ta cire kunya ta na son ta saka mishi soyayyarta a ciki zuciyar shi,don haka duk abin da ta san zai faranta mishi rai kuma matar sa ta kasa da shi Juwairiya ta cika gurbin sa,shi kan sa mamakin yadda ya saki da ita yake yi.

Sai dai ya kan tuna Juwairiya ba macen da namiji zai iya wulaƙantawa ba ne ko da kuwa ba ya son ta,don Allah ya yi mata abubuwa da dama ga tsananin kula da ibada sosai,sam ba ta wasa da ibada wanda hakan ya na matuƙar ƙara masa ƙimarta a idanun sa.

In ka gan su a gidan zaka É—auka wasu masoya ne ko da yake ya sha gaya mata shi kan sa bai san ya aikai ya sake da ita da yawa ba,amma kawai su rayu tamkar ma'auratan da suka yi auren soyayaya domin ya na jin zai iya mata komai a zaman su in dai zai faranta mata.

A.m ya kai da komai ba ya iya yi sai dai ta yi masa hatta abinci a baki take ba, gabaki ɗaya ya shagwabe ya koma kamar wani ƙaramin yaro ya na fatan ina ma ace Zainab ɗin shi take da wannan hali na kula da shi lailai da ya more.

Juwairiya ta dage sosai ta saka wata irin shaƙuwa a zuciyar A.m ba tare da ya san haka ba,shi ya na danganta hakan da irin kular da take ba shi shi ya sa in ya ji kewarta sai ya ɗauka jikinta da yake matuƙar so yake sa shi jin kewarta.

Amma take zai nemi waya ya kirata su shi hira sosai,ya kuma ɓata lokacin sa ya na waya da ita.

Duk irin kular da take ba shi ta mai da kanta tamkar baiwa a gare shi ta na jiran ta ji ranar da zai rungumeta ya ce mata ina son ki!

Amma bai taɓa faɗin haka ba sai kalaman da suke sakata kuka yake faɗi irin su,kina da wata irin baiwa da ba ko wace mace take da shi ba,in kika riƙe alƙur'ani ki na karatu wani irin ƙarin ƙima kike samu a idanuna,domin Allah ya jarabce ni da son mace mai kula da ibada.

"Juwairiya duk ranar da muka rabu zan yi fama da kewar ki ina kishin mijin da zaki aura nan gaba domin ya yi dacen mace ta gari da baiwar kyau da sura.

Alokacin da nake kallon ki cikin hijabi sai nake jin tsanar ki kamar ba ki waye ba,ashe Juwairaah mata masu saka hijabi wata baiwa suke da shi na kyawun sura kike ɓoyewa.Surar ki abin sha'awa ce ga kowa.

Har lau ina faÉ—a miki zuciya ta da gangar jikina za su yi kewar ki,amma ba komai zan mai da kula ta akan É—an ki sai ya zama wani abu a rayuwa,Allah ya sa ki haifa min baby mai kamar ki."
Chapter 45 · 0% Book details