Sashe 49
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannunta biyu ya haɗe da ƙarfi har sai da ta yi ƴar ƙara da hawayen wahala."Ki sa aya a bakin ki kisan irin maganar da za ki yi dani,a gabana kike maganar wani ƙato zai mallake ki koma meye ai ni mijin ki ne kya bari auren ya ƙare kafin nan,ko ba ki san ina kishin mijin da za ki aura ba saboda ki na da baiwar da dole mutum ko ba ya son ki ya yi kishin ki."
Ya ce yayin da idanunsa suka nuna ƙarara abin da yake nufi,hakan sai ya bama Juwairiya mamaki sosai ta saki baki da hanci ta na kallon shi.
"Yes gaskiya ne abin da na faɗa bacin na san wace ce ke sai nace da gaske ne ki na yin abin da Zainab ta faɗa,don haka ina son jikinki da halayen ki matuƙa."
Ya ce da ita tare da lakuce mata hanci ya ƙara rungumeta.Juwairiya ta ji wani iri lokacin da ya furta hakan ta so ace ita ya ce ya na sonta ba jikinta ba,sai ta ji hawaye na sauka a ƙuncinta.
" Ni fa ba ni da lokacin ganin hawayen ki ba kuka na ce ki yi min ba,duk da kwana biyu na yi kewar su ki kawo min abincina ina falo."
Da sauri Juwairiya ta ture shi daga jikinta gani Binta tsaye ta shigo ta na kallon su ta furta." A'uzu billahi minash shaiÉ—anir rajiim."
A.m da ko kaÉ—an bai razana ba ya daka mata tsawa ya ce." Don ubanki aljanu kika gani da za ki yi ta'awizi maza fice daga gurin nan."
Ya kalli Juwairiya da ta kalli ƙofar da Binta ta ruga da gudu ta fice,sai hawayen ta ya ƙaru bai wani damu ba ya ce."Ki kawo min abincina."
Ya fice ya barta cikin tashin hankali da kunyar Binta.
A haka dai abubuwa sukai ta faruwa Juwairiya na jin kunya matuƙa A.m kuwa ya samo hanyar da zai kori Bainta daga gidan,don tun da ta shigo Juwairiya ta dai na sakewa da shi ko son ganin shi ba ta son yi gashi kuma ba haka ta sabar mishi ba.
Ana gobe Zainab za ta dawo Juwairiya sun sha aikin soye-soye ta gaji matuƙar gaske ta na zaune ita da Binta,wanda yanzu suke zanan kurma a tsakanin su.
Da sauri ta tashi ta É—auko kur'ani saboda ta manta yau ba ta yi karatun da take yi ba wanda ta ibar ma kanta kullum.
Binta ta yi zuru ta na kallon yadda take rera ƙira'ar hafsi cikin murya mai zaƙi,sai ta kauda duk wani tsoro ya ce.
"Anty."
Cikin sanyi Juwairiya ta ije kur'anin ta na kallon ta yayin da gabanta yake faÉ—i sosai,don ta san Binta magana za ta yi mata ganin yadda ta natsu.
Ba tare da ta amsa ba ta zura mata ido ta na kallonta.
"Na yi mamaki kasancewarki mace mai addini da hankali kika biyewa mijin Anty Zainab kuna alfasha bayan kin manta duka abin da namiji ya yi ado ne,ita kuwa mace ya na zama tabo da miki a rayuwarta kuma ya ci gaba da bibiyar zuriyarta."
Jikin Juwairiya ya yi sanyi jin abin da ta ce amma ta kasa koda motsi bare ta yi tunanin za ta amsa mata.Ganin haka sai ta É—ora da ce wa.
" Mahaifiyata kafin ta rasu ta ja layi sosai tsakanina da duka wani ɗa namiji wanda ba muharramina ba,saboda suna tsotse zaƙin da ke cikin rake su yada diddiga.kuma koma me ya faru Anty ke ce a ruwa saboda Anty Zainab ta na da kishi kuma ba ta da hali za ta iya komai ga kuɗi,yayin da kike talaka mara ƙarfi sannan kamar kin ci amanar tarbiyar da mahaifiyar ki ta baki ne."
Hawaye suka wanke mata fuska ta kama hannun Binta ta rungume ta na kuka ta ce." Ya zan yi na fahimtar dake har yanzu da ƙuruciya a kan ki,kuma wasu maganar sun yi ma ƙwaƙwalwar ki nauyi ban san yadda zan yi ki fahimci ɗacin da ke zuciyata ba."
Janye jikinta ta yi ta ce."Ina da hankali na san me nake yi,kuma na san ke mai aikin Anty Zainab ce kamar yadda ta gaya a gaban ki,sannan wanda kike kwana a É—akin sa mijinta ne to mai kike so na fahimta in ba zina kuke yi ba?"
Juwairiya ta gwalalo ido jin abin da ta faɗa daidai lokacin da suka ji muryar A.m ya daka tsawa da ƙarfi ya nufo kan Binta ya na faɗin.
"Ke baki da hankali matar ta wa ta sunna kike faɗin muna zina! Allah ya tsare ni ban taɓa ba kuma ba na fatan na yi."
Binta da ba ta fahimci komai ba ta ji dai ya kira Juwairiya,da sunan matar sa wanda ta saka a ranta ta yi kuskuren jin abin da ya faÉ—a ne.
Ganin ya nufo ta ta miƙe tare da saka kuka ta ƙanƙame Juwairiya da ta razana saboda yadda ya canza lokaci guda.
Ga mamakin Juwairiya sai ta ga ya ciro wuƙa a aljihun sa wanda ta tabbata da ita ya shigo,da ma da shirin sa ya zo kenan kuma ya samu hanya.
Hannun Binta ya samu ya karta sai ga jini tar yarinyar ya saki wani irin kukan azaba tamkar numfashinta zai ɗauke ta na roƙon ya yafe mata,amma ina A.m ya yi nisa baya jin kira idanunsa sun kaɗa sun yi jajur baƙin cikin ce wa da ta yi suna zina da matar sa na sunna ya sa shi zai aikata aikin dana sani.
TOFA A.M LAFIYAR KA ÆŠAYA KUWA MAI KE FARUWA KO KASHA WANI ABU NE BARI DAI NA GAMA TARABBABIN WANNAN LAMARI KAFIN NA ÆŠORA BIRONA.
KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.
BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU
JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa
ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 23*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Cikin tashin hankali ta kama shi ta riƙe ta na kuka sosai kamar ranta zai fita ganin hankalin sa ba shi a jikin sa.
"Na shiga uku A.m so kake ka yi kisa?".
Ta faɗa cikin muryar kuka ta na girgiza shi gabaki ɗaya ta ruɗe gani take kamar zai ƙara yankar ta.
Wani mugun kallo ya watsa mata ya sake ta ya na huci."Allah ya sa ki ƙara gigin aibata aurena sai na zama ajalinki."
Binta da ta ji maƙura da gudu ta ruga ɗaki tare da kulle kanta ko kaɗan ba taɓa tunanin mahaukaci ba ne ganin zai illata ta.
A ranta ya zama dole tabar gidan domin ba za ta zauna ba ya kashe ta.
Ta shiga cikin tsananin mamaki da ya ce Juwairiya matar shi ce,to mai hakan yake nufi bayan Anty Zainab ta gaya mata yar aiki ne.
Sam ba ta kawo cewar zai iya ije matar shi a gidan ta zama Æ´ar aiki ba,shi ya sa ta É—auka kawai ya gaya mata hakan ne don ya kawar da tunaninta aka suna zina.
HaÉ—a kayanta ta shiga yi domin dole in Anty Zainab ta dawo za ta bar gidan ba yan ta tsegun ta mata.
Juwairiya kuwa kuka ta saki ta ƙara faɗawa jikin sa." A.m ka na cutar da zuciyata mai kake tunanin zai faru in har ta faɗa ma Anty Zainab abin da yake faruwa,kawai gidan nan zan bari ayau in ya so duk abin da zai faru ya faru,amm na gaji da wahalar da rayuwata da kake yi.
Da ƙarfi ya janyo ta jikin shi ya na huci.
"Juwairaah ki saurare ni ba ni da nufin na cutar dake kawai ki fahimci abin É—aya.."
Juwairiya ta katse shi ta na faɗin cikin kuka da murya mai ƙarfi.
" A.m ya ishe ka ba ka sona ka tsane ni wannan dalilin ya sa kake wahalar da zuciyata da gangar jikina,kullum sai dai ka yi min maganar ka na son jikina halina da kyawuna shin ni bani da zuciyar da za.."
"Juwairiya."
Ya faɗa da ƙarfi tare da girgizata ya na zare idanunsa.
"Karki kawo min maganar banza kin san dalilin aurenki so ban ga dadilin da za ki kawo min maganar banza ba."
Fisge hannunta ta yi ta na kallon sa ta na ja da baya har ta kai bakin ƙofa da gudu ta fice.
Ko da ta shiga ɗaki halin da ta ga Binta sai ta ba ta tausayi karɓar tsummar da ta ga yaga cikin kayanta ta na ƙoƙarin ɗaure gurin yankar.
Hannu ta saka ta karɓi tsummar ta ɗaure mata hannun yayin da hawaye yake kwaranya a fuskokin su duka.
" Ki yi haƙuri haka rayuwa take tafiya a ko da yaushe talaka shi ne a ƙasa ko da shi yake da haskiya."
Ta faɗa ta na kallonta idanunta na ƙara zubar hawaye.
Binta ba ta ce komai ba sai share hawaye da yake gangarowa a ƙuncinta da ta yi.
A ranta ta saka ba za ta ƙara kallon kowa daga cikin su ba balle ta yi magana ta tono ma kanta tsuliyar dodo,ganin abin da ya yi mata ya sa ta fara tunanin ko bashi da imani ne amma har yanzu ba ta amince da faɗin cewar Juwairiya matar shi ce,sai dai in za su yi mata badda kama don kar ta gaya wa Zainab.
Kallonta ta ƙara yi ta na jin tausayinta matuƙa ganin yankan da ya yi mata ya shiga ciki sosai.
"Anya A.m ya na da hankali?"
Tambayar da ta yi ma kanta kenan amma ta rasa amsa sai ta ɗago ta ƙara kallon Binta a karo na biyu.
"Wannan dalilin ya sa na ce miki ba za ki fahimci komai ba."