← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 86

Sashe 70

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gurin da take kwance ya nufa ba tare da ya ji kunyar doctor dake tsaye yana kallon sa yana dariya ba,ya bata hot kis bayan ya rungume ta.
" Da gaske za ki haifa min Baby?"

Dariya doctor ya sannan ya kalle shi ya ce."Aman da ta yi ya É—an galabaitar da ita so yanzu za mu ba ta rest bed zuwa an jima sai ku tafi,na rubuta muku maganin da zai dakatar da aman."

" No doctor a ƙara mata ruwa kawai saboda jikinta ya yi weak ina son yarona ya samu kuzari,kasa ka mata drip kawai ba na son abin da zai cutar da shi,kaga in ba ta da ƙarfi ba zai samu damar ya juya yadda yake so ba."

Dariya ya yi sosai ya bugi bayan sa." To fa yau Allah ya haÉ—ani da patient sabon shiga to Allah ya sa madam ta haifi Æ´an biyu,amma jikinta ba sai an saka mata ruwa ba,ka ba ta maganin nan da zarar kun je gida.

Duk yadda doctor ya yi da shi amma ya kafe sai an yi mata ƙarin ruwa,don kar yaron sa ya wahala,dariya sosai yake masa ganin yaushe akai daren da har gari ya waye yaron da ko gudan jini bai zama.

A.m ya ruÉ—e duk da tashin hankalin da yake ciki amma in ya tuna zai sami baby,sai ya ji ya É—an rage damuwar shi.

Wayar sa ya zaro ya kira A.m akan ya zo asibiti ya same shi.

*********
Zainab ta sa saki wani gigintaccen kuka lokacin da Momi ta shigo gidan tana sallama.
Ƙofa ta shiga bugawa tana faɗin." Momi ki buɗe ni ina ɗaki ya kulle ni."

Jikin Momi ya kama rawa sosai ganin jinin da ya zuba a hannun A.m face-face a falon.
" Mai ya saka ya kulle ki lafiya wai mai ke faruwa ne jinin waye a ƙasa?"

Ta jero mata tarin tambayoyi cikin tashin hankali.

" FaÉ—awa jikinta ta yi ta saka gigitaccen kuka.
" Momi tun da na taso na taɓa neman wani a bu na rasa?Kuma kin taɓa ganin na yi sharing ɗin wani a bu a gidammu,ko da mota ce?"

Da sauri ta girgiza mata kai alaman
" a'a."

To wai Momi A.m yake tare da Juwairiya mai aikina da Lantana ta ba ni labarin suna tare, kuma wai auren ta ya yi har tana da ciki,ya ije ta a gidana suna rayuwar aure."

Sai ta saki razanannen kuka tana girgiza kanta.

" Ni wallahi gani nake kamar mafarki nake yi! Komai ya canza cikin ƙanƙanin lokaci.Wayyo Allah na!Na shiga uku."
Da sauri ta miƙe a zabure." What impossible! Amma wasa kike mini ko?Haba ina ta ya ya za'ai A m ya aikata wannan ɗanyan aikin, bayan ya san ba'a yi wa family ɗinmu kishiya,sannan kika ce ta samu ciki wa ya yi mata,bayan shi baya haihuwa ku..."

" Momi ki tsaya ki fahimce ni na san na yi miki laifi ban taɓa gaya ma kowa ba,amma ki yi mini uziri don Allah!"

Ƙara miƙewa ta yi a zabure bayan ta gama gaya mata abin da ta ɓoye mata tsawon shekaru.

Zaro idanunta ta yi da ƙarfi ta furta." Innalillahi wa inna ilaihir raju'un! Zainab.

"Da gaske ne ke ce ba kya haihuwa ba A.m ba?"

TSANANIN FIRGITAR DA TA NUNA YA TADA HANKALINA NA IJE RUBUTUN DON NA SAMU NATSUWA.

KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI

SAKACINA KO HALIN MAZA

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 31*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

" Momi da gaske ne duk abin da na gaya miki na aikata,tabbas na sha maganin hana haihuwa don kar na haihu in tsufa A.m ya guje ni.Amma duk abin da na yi saboda shi ne ina..."

Wani irin gigitaccen mari Momi ta kwasa mata sai da ta wuntsila.
" Zainab are you stupid! Kin san abin da kika aikata kuwa kin san irin tashin hankalin da kika saka kan ki? Inna lillahi na shiga uku! Mai ya sa kika ɓoye min ina matsayin mahaifiyarki? Da duk haka ba ta faru ba."

Zainab da ta ji saukar marin Momi sai da ta yi suman wucin gadi,ta dafe ƙuncinta cikin tashin hankali,saboda tun da take Momi ba ta taɓa kai koda ɗan yatsarta jikinta ba.

" Momi marina fa kika yi?Bayan ba ki taɓa ko yin ihu mai ƙarfi gare ni ba,balle ki ɗora hannunki a jikina."

Momi da take cikin tashin hankali saboda abin da ta aikata,kallonta ta yi ji take kamar ta rufe ta da duka.

" Wallahi Zainab ji nake kamar na rufe ki da duka! Kin yi kuskure sosai in har kika yi wasa sai zaman duniya ya gundure ki,saboda girmar laifin da kika aikata.
Maihaifinki na matuƙar son ya ga kin haihu haka nima, dangin A.m suna nan suna tsananin damuwar su akan rashin haihuwa da ba ku yi,ina kallon sa a matsayin azzalumi baya haihuwa ya kuma ƙi rabuwa da ke,ashe tawa ƴar ne ba ta haihuwa."

Ta faÉ—a cikin kuka sosai wanda ya É—aga hankalinta sosai.

Hannunta ta riƙe tare da fashewa da kuka ta ce." Idan har za ki yi irin kukan nan, ya kamata ni na yi hawayen jini Momi,amma har yanzu ban ji tashin hankali ba sosai don ba na haihuwa,asalima ni yara sam ba su dame ni ba saboda wahala kawai suke baka, kuma kin san Momi na tsani ƙazanta sam ba na son na wahalar da rayuwa."

Momi ta fisge hannunta ta juya mata baya,ta na kallon windo cikin wata irin murya,mai nuna tsantsar damuwa ga mamallakin muryar ya shiga.

" Har yanzu ke yarinya ce ba ki gane komai ba,amma na tabbata za ki yi nadama in har ba ki É—auki mataki ba,na rantse miki duk ranar da ki ka yi sake A.m ya haihu,daga ranar za ki fara son yaran duniya ba ki É—aya."

Ta juyo da ita suna fuskantar juna cikin murya mai sanyi ta ce."Duk da cewa Allah ya mallaka mini ke,amma mahaifinki har yau yana kukan rashin É—a,ba za ki gane mai nake nufi ba sai ranar da kika yi hankali gurin tunanin wa zai gaji dukiyarki.Ki duba irin dukiyar da kike da shi in kika mutu wa za ki bar mawa?Ko so kike duniya suci.
A.m yana da kuÉ—i da ahalin sa mene nufin ki akan dukiyar babu rabon ki a ciki?"

" Haba Momi mai zan yi da wata dukiya iya abin da Allah ya mallaka mini ya ishe ni, ba sai na nemi agajin kowa ba,ga kuma dukiyar mahaifina, da ni ce kaÉ—ai mallakin sa."

Ta ce da Momi cikin jin ƙosawar maganar ta, don ita ba ta yi tunanin za ta ɗauko mata wannan shirmen ba,saboda damuwarta ta fi gaban wannan.Abu ne na zuciya da Allah ya ke halittar so a ciki,sam ba za ta yadda wata ta ƙwace mata shi ba.

" Ba za ki gane ba ne Zainab dole ki É—auki mataki na san mai kike nufi,kuma magana ta tana kan hanyar damuwarki,kin ga in kika yi gigin barin abin da kike faÉ—i ya faru,wallahi sai kin raina kan ki."

" Wannan dalilin ya sa na ce tuntuni mu watsa mata acid amma Momi kika ƙi,da yanzu matsalata ta kau yanzu gashi kin sakani a cikin matsala,don ko kaɗan ban yi tunanin tana cikin gidana ba."Ta ce da ita tana ganin kamar Momi ta ja mata duk abin da ya faru.

" Na hana ki ne saboda watsa mata ba shine mafita ba,in har yana sonta to zai yi komai don ya ceci rayuwarta.Na bari ki dawo hankalinki ya kwanta sai mu ɓullo ma abin ta ruwan sanyi,ba tare da ya yi tunanin da saka hannunmu a ciki."

" To yanzu Momi ya zan yi?Ba zan iya barin ma wata kucaka ƙazama yar talaka mijina ba,ina son sa shi kan sa ya san irin son da nake masa.Ki taimake ni mijina ya dawo gareni Juwairiya ta fita daga rayuwar sa,in har ba so kike ki rasa ni ba,don na yi rantsuwar ba zan taɓa barin wata ta raɓe shi ba,ko da ace ba ni tare da shi! In ko hakan ta kasance mutuwa zan yi,sai dai ku nemi wata ƴar."

Jijjiga ta da ƙarfi take yi ganin yadda ta fita hayyacinta tana watsi da kayan ɗakinta.

" Ya isa ki natsu ki gane wace ce mahaifiyarki sam ba zan bari hakan ta faru ba,ko da ace zan yi yawo tsirara ne! Kin san wace ce mahaifiyarki ya kamata ki zama jaruma.Irin zuciyata ya kamata ki ɗauka,ba in aka yi miki abu ki ce za ki rama ta kisa.Sab ba haka jarumi yake cin nasarar sa ba,dagewa za ki yi ki saka makamanki ki yaƙi duk wanda ya zama garnaƙaƙi a cikin rayuwarki."

Ta faɗa yayin da ta yi shiru tana kallonta don ba ta fahimci mai take cewa ba." Bari na baki labarina wanda baki taɓa sani ba Zainab.Mahaifin ki yaso wata mace kamar ransa yana jin zai iya mutuwa in bai same ta ba,ita kuma ƙawatace da muka haɗu a makaranta.
Mun shaƙu sosai muna shiri da ita,duk ƴan'uwanta na san su,don har zuwa nake na kwana a gidan su.Mahaifinta hamshaƙin mai kuɗi ne sosai suna da kuɗi,yayin da ni ina karatu a gidan kawuna shi ya ɗauko ni ya sani a makaranta iyayena talaka.

Tun da na fara mahaifinki na ɗauki son duniya na ɗora mishi sosai,sannan ina son na canza rayuwata daga ƙangin talauci.
Chapter 70 · 0% Book details