← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 86

Sashe 32

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Juwairiya dawo magana zan yi dake."Mama ta faÉ—a tare da lumshe idanunta da su kai mata nauyi.
"Mama don Allah bari na gama girkin kar yunwa ta dame ku ga Ibrahim har ya fara yaushi."
Ta ce cikin in ina ta na son ta kauce ma idanun Mama." Kar ki damu da dawo kawai akan mutumim nan bawon Allah da ya ke taimakonmu,na ke son mu yi magana ni fa kullum tunanin sa nake yi ga shi ya ƙi bayyana kan shi,bare mu yi masa godiya an ya saboda Allah yake mana ni fa na fara shakku a raina.".
Juwairiya ta firgita da maganar da Mama ta yi mata ta san da ma dole ta yi mata waÉ—annan tarin tambayoyin game da kuÉ—in da A.m yake kashe musu ya wuce misali.

Ganin Mama ta fara zargi a zuciyarta sai ta daure ta kauda duk wani tsoro da shakku a ranta,ta kalli Mama da natsuwa ta koma ta zauna ta ce." Mama ki yi masa kyakykyawar fahimta kin san irin tarin kuÉ—in da suke da shi,sannan da zai cuce mu kuÉ—in ba zai biyo ta hannun Baba Sani ba.Don Allah ki kauda komai a ranki kuma in ma sabon gidan da ya gidan da ya siya mana ne ba kya so sai a mayar masa."
Da ƙwarin gwiyarta take magana saboda ta yi tunanin yanzu ita ace za ta din ga buga ƙwallon a raga kuma in ba ta jajirce ba Mama za ta ɗago ta wanda hakan zai ɓata shirin su.

"Lamarin duniya a kwai tsoro ke yarinya ce amma ba zaki gane ba kuma da kike maganar Baba Sani ai duk kanwar ja ce,ke sheda ce akan halin sa kin san irin halaccin da mahaifin ku ya yi mishi amma ya manta ya kasa tallafar rayuwarmu,shirun da kika ga na yi hakan ya samo asali ne saboda alƙawarin da na yi ma mahaifin ki wanda ya tilasta min na yi masa daga baya na zo ina dana sani,amma wallahi kin ji na rantse da ban yi ma mahaifin ki alƙawari ba da na ɗauki mataki akan yadda ya hana rayuwarmu saƙat."

Ta ce ta na kallon Juwairiya da ta firfito da idanunta ganin yadda Mama take magana, saboda tsawon rayuwarta fa ita ba ta taɓa jin ta ɗaga harshe ba,sai yau lamarin ya matuƙar razana ta har ta fara dana sanin amincewarta don da wuya shirin su ya tafi ga shi A.m ya kashe kuɗin sa.
Mama ce taci gaba da magana ganin ta yi shiru ta na zare ido sai ta ce." Wa ya sani ko kuÉ—in kammu muke ci."
Yayin da tsoro ya ƙara kamata tuna yanzu duniya ba gaskiya.

" Da ma Baba Sani zai yi miki bayani Mama ni ne na ce ya bari ki ƙara samun sauƙi Wato shi mutumim da yake taimaka mana ya auri matarsa wacce ƴar majalisa ce. To gabaki ɗaya rayuwarta ƙasar waje ta yi karatu,ta samu gata sosai wanda hakan yake saka suna samun saɓani ga shi ba ta iya girki ba komai ba ta yi."

Ta yi shiru ta na son ta ji ko me Mama za ta ce amma sai ta ga ta tsaya ta harɗe hannunta a ƙirjinta ta na sauraren wannan tatsuniyar ita tunanin ta to meye haɗin ta da wannan dogon labarin wanda take ganin ina ruwan ta da labarin sa.

Juwairiya ta rasa in da za ta kama ta ci gaba da zancen a wannan lokacin ji take kamar ta É—ora hannu ta yi ta kuka ganin yadda Mama ta kafe ta da ido.

" To saboda wannan ne ya na son a koya mata abubuwa da girki yake son ya s..."Juwairiya da ta ci gaba da magana sai kuma ta tsaya tare da sakin kuka wanda hakan ya ta da hankalin Mama, amma sai ta yi shiru ta na kallonta yadda take kuka mai sauti.

" Shi ne yake son mace wacce za ta zauna a gidan shi na shekara ɗaya ta koya ma matarsa girki da yadda ake kula da gida,na tsawon shekara ɗaya kuma duk wacce ta amince za ta yi zai tallafa ma rayuwar su,ban san tsinannen da ya gaya masa halin da kuke ciki ba har ya zaɓi Juwairiya a matsayin wacce za ta yi,don wallahi da na sani ba zan bari ba ai gara na saka ƴata."Muryar Baba Sani suka ji ya na magana a bakin ƙofa.

Mama ta ji wani irin juwa ya kamata murna za ta yi ko farin ciki amma kuma Juwairiya ta din ga yawon aikatau kenan?Juwairiya a yanzu ya kama ta ace ta na É—akinta,sai dai kuma mutumim ya yi hidima ga rayuwar su wanda wani É—an'uwan ka ba zai iya haka ba.

Ta buɗe baki da nufin ta nuna rashin amincewarta amma sai ta kasa saboda ya yi musu halacci haka kawai sai ta ji ba za ta iya musawa ba,amma ranta ta saka dole in Juwairiya ta gama aikin ta za ta yi aure da irin mijin da take so ko da hakan zai saka ta karya alƙawarin da ta yi ma marigayin mijinta ne don za su raba abin faɗi ƙila kutu za ta raba su,saboda haƙurin abin da yake mata wanda sakamakon hakan ya sa zuciyarta ta buga.

Juwairiya ta shiga tsananin mamaki gani Mama ba ta ƙara ce mata komai ba ta takure gefe zuciyarta cike da tashin hankali,wani irin zazzaɓi ya rufe ta sai makyarkyata take hawaye ya na zuba a ƙuncin ta.

Mama ta yi jim da kofi a hannunta bayan ta ba ta magani tasha." Ni fa hankalina ya tashi Juwairiya ke ma kin yi gangancin karɓar wannan kwangilar duk da hakan ya tseratar da ke da ga auren wannan tsohon,amma kin manta irin wulaƙancin da dukan da kika sha a dalilin aikatau."

Juwairiya ba ta ce komai ba sai hawaye da suke shatata fuskarta.
Mama tace ta rasa wani irin tunani za ta yi akan maganar aikin Juwairiyar da za ta yi,kuma da ta nemi sanin waye hatta ita Juwairiyar ba ta gaya mata ba sai wani lulluɓin biri suke yi wa kare an ya? Akwa lauje cikin naɗi!Ta faɗi a zuciyarta cike da shakku.
Ta zauna a gefen gadon da take kwance tare da janyo mata bargo." Allah ya baki lafiya."Ta ce tare da zabga tagumi.

Wa su irin zafafan hawaye suka wanke mata fuska sai ta canza kwanciyarta saboda ta juya ma Mama baya." Ki yafe min Mama na san ban yi miki adalci ba,amma na yi hakan ne saboda na ceci rayuwar ku duk da hakan ni zai kai ni kushewata saboda ƙara kusanci da na yi da shi,shi zai jagoranci ruhina zuwa mutuwa.Allah na roƙe ka ka cire min son sa a cikin zuciyata."

*****

A.m zaune a tanƙamemen falon sa da remote a hannun sa gefe kuma Zainab ce take aiki da computa da ta ɗora a cinyarta,saboda gwanancewa da aiki da ita da ta yi ba tare da ta kalle abin da take daddannawa ba take aikin ta,yayin da hankalinta ya na kan A.m da yake ta jan tsaki ya na juyi a kujerar.

Talatu mai aiki wacce take sabuwar ƴar aikin da Mominta ta kawo mata saboda halinta sam ba ta daɗewa da me aiki.Ita ce ta yi sallama ta shigo idanunta akan A.m saura ƙiris ta yi ɓari amma sai ta ije ta ci gaba da kallon shi.

A.m wanda da ma hanya yake jira miƙewa ya yi ya kwasa mata mari ya ce." Wai ke wace irin mayyar yarinya ce ba na hanaki kallona ba!Banza ƙatuwa da ke maza fice min daga falo! Kuma yau zaki bar gidan nan."

Da sauri ta ruga ta na shafa gurin da ya mare ta don ta ji zafi sosai jikinta har rawa yake saboda ita duk ta gan shi,sai ta ji ta na son ya kula ta duk da ta san shi ba san ta bane amma ya na da kyan da duk mace za ta yi mafarkin samun shi.
Zainab kuwa tsaki ta yi a ranta ta ce." Haka kawai duk ka tsani ƴan aiki kullum cikin canza masu aiki muke wannan karan sai dai ka yi haƙuri amma ba zan canza ba."
Juya wa ya yi ya kalli Zey da ta daina aikin da take yi ta na kallon shi ya ce." Allah na tsani yarinyar nan ke duk masu aikin ki dangin mayu kike É—auko wa,gaskiya ki sallame ta ni sam ma abincin ta ba ya min daÉ—i."

"To ni ya kake son na yi ko ni kake son na dun ga yi maka girkin?"Ta ɗan saki dariya ta ci gaba da magana ta na ce wa." In haka kake tunani gara ma ka cire har na yi aure ban taɓa shiga kicin da nufin na yi girki kai ko ruwan zafi ban iya dafawa ba,ka ga ya zama dole ka ci na ta in ba so kake ka ɗauko kuku namiji ba wanda da ma kafiyarka na tsiya da baƙin kishi ya hana ka,amma ni ban ga dalilin da ya sa ka za ka ƙi ɗaukar kuku namiji ba a gidammu su suke girki ni kai na na gaji da cin abincin masu aiki."

Wani kallo ya watsa mata ya ce." Zainab ki kiyaye ni da maganar kuku a haka yadda kike zama kusan naked ne zan ɗauko kuku,matan ma da suke kallon ki ni na san baƙin cikin halin da nake shiga sai dai na lura shashasha ce ke kin ɗauki rayuwar yahudu da nasara ba ki san darajar kan ki ba."

"To aiko ka na ruwa wallahi tunna duk yawon duniya da ka yi baka waye ba ni ban ga dalilin da zai saka kasa na din ga ɓoye kai na ba kamar wata ƙonannniya."
Ta ba shi amsa cike da gatsali ta na girgiza ƙafa.
Chapter 32 · 0% Book details