← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 86

Sashe 73

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Wayyo Allah na shiga uku ya zan yi da raina wai yau ɗan da na ba ma tarbiya ne! Yake riƙe da mace maccen da ba muharramin sa ba."

Sai ta fashe da kuka mahaifin sa kuwa tun da ya faɗi,bai ƙara cewa komai ba sai kallon A.m da yake yi tamkar bai san shi ba.

" A.m dawo mu yi musu bayanin ita ɗin matarka ce ba yadda suke tunani ba,mu daina ɓoye ɓoye mu gaya musu gaskiyar komai."

Abba da ke kwance ya miƙe cikin mamaki ya ce." Na lura baku da hankali dukan ku,ta ya ya za'ai ya yi aure ba tare da sani na ba?"
Ya tambaye shi cikin tsananin mamakin sa ya kuma kalli Daddy da ya yi fuska sosai,ganin ana muzanta mi shi shalelen sa.

" Mai ya sa za ka tambaye ni dalilin auren sa bayan ka mallaka min shi halak malak?"

Abba ne ya harzuƙo gani yake kamar Daddy ya raina mi shi wayo,don haka cikin fusata ya cakume shi.

" Ba ka da hankali ne?Kai da shi duk kun zare! Duk da na ba ka shi kyauta,ai kwarmin ido ba ramin ba ne,in ba ka sanar da ni auren sa ba,ka gaya ma mahaifiyar sa da ta yi rainon cikin sa har na tsawon wata tara,ta kuma yi É—awainiyar shi."

Sai Daddy ya din ga kallon sa cikin wani irin kallo yana matsawa,yayin da idanun shi suka fara zubar hawaye,ya kalli A.m da hankalin shi in ya yi dubu to ya tashi,ganin tun da yake bai taɓa ganin iyayen na sa sun yi ko da sai in sa ba.

" Allah na gode maka da ka san da ni a duniyar har ka jarabce ni da rashin haihuwa,yau ga É—an'uwana wanda muka fito ciki É—aya da shi ya yi mini gorin É—a,ya nuna ban isa da É—an shi da ya haifa ba,wanda na yi tunanin yaransa duka mallakina ne."

Da baya baya yake tafiya yana zubar hawaye, duk da ya san abin da A.bba ya ce gaskiya ne,bai kyauta ba da ya biye masa aka yi auren ba tare da sanin su ba,amma ya ji zafin gorin da ya yi mishi sosai ya ji ƙuna a zuciyar sa fiye da tunani.

" Amma ka san ba ku kyauta mana ba,haba ta ya ya zai yi aure ba mu sani ba,sannan ya ije matar sa a gidan sa,kuma ba tare da matar sa ta sani ba?Anya kana ganin ganin kun yi mata adalci kuwa?Sannan ya rasa macen da zai so sai yar talaka mai zai yi da ita"

Ya numfasa ya ja numfashi yana kallon sa sannan ya É—ora da cewa." Yarinyar nan Æ´ar aminin ka ne,kana ganin bai tozarta ka ba ka duba iri tashin hankalin da mahaifinta ya yi maka."Ya ce yana kallon sa.

" Tabbas ƴar aminina ne kuma na san haka,amma ka sani duk abin da ya faru ita ta jawa kanta,da fari da suka zo da maganar korar su na yi na ƙi yadda da maganar su,amma da ga baya A.m ya gaya mini,ita Zainab ɗin ce ba ta haihuwa sannnan kuma ta saka shi dole ya yi mata,alƙawarin kar ya yi mata kishiya,bayan duk abin da ya faru ita ta ja ma kanta,saboda mugun son duniya.

Saboda haka na amince bayan na duba irin ƙuncin da nake shiga sakamakon rashin haihuwa,wanda yau gashi kai ma da kake ɗan'uwana ka goranta mini."Ya tsaya da maganar domin ya huta kaɗan.

Abba da sauran mutanen da ke tsaye cikin mamaki suke kallon Daddy,suna al'ajabin wannan maganar da ya tayar da hankalin su.

" Ganin na ƙi yadda da maganar amma sai A.m ya nuna ya haƙura,wanda ni na ƙi yadda ne kan ya canza haukar maganar da ya yi mata,na ba zai ƙara aure ba,amma sai ya nuna sam shi ba zai ƙara aure ba,saboda haukar so da ya rufe mi shi ido.

"Na amince A.m ya aureta ne saboda in har ba ta hakan ba, a yadda ya nuna ba zai taɓa ƙara aure ba,ni kuma ba na son ya rayu ba tare da ya ga ɗan sa a duniya ba,sanan in na fito fili na nuna kan dole ya ƙara aure ban san ya mahaifin Zainab da ita za su ɗauke ni ba."Ya ƙarashe maganar cikin mutuwar jiki yana ƙara goge sauran hawaye da yake maƙale a fuskar sa.

Ya kama hannun Abba ya riƙe sosai tare da sakin kuka ya ci gaba da cewa." Ka yafe mini amma yau ka nuna min iyaka ta,na san in da zan tsaya akan yaran ka,amma ka sani ba laifi na yi ma Allah ba da ya hana ni haihuwa,kullum ina godiya ga Allah da ya yi mini tarin ni'imomi a rayuwa."

Abba da jikin sa ya yi sanyi sosai ganin ɗan'uwan sa ya yi fushi sosai,shi kan sa ya yi dana sanin maganar da ya gaya masa,wanda hakan ya faru sakamakon ɓacin rai da dokin zuciya,sannan ya yi baƙin cikin abin da su yi haba sai ka ce shi bai fi su hankali ba,amma kuma duk abin da ɗan'uwan sa ya yi masa bai kamata ya yi masa gorin haihuwa ba,duk da cewar bai san lokacin da maganar ta fito ba,don magana zarar bunu ce.

Dukkannin su sun cika da mamaki iya mamaki da gaske A.m yana haihuwa ya yi musu ƙaryar haka,don kawai ya faranta ma mace bayan ya san in da ace shi ne baya haihuwa da ba za ta zauna da shi ba.

Mahaifiyar sa ta zo gaban sa ta din ga kifa masa mari, har sai da ƙanin sa ya janye shi daga gurin.

" Ka cuce mu sam ba ka yi mana adalci ba!Kasan iya tsawon lokacin da na ɗauka ina tashi cikin dare,akan Allah ya sa ka samu ɗa.Kusan kullum sai na yi maka addu'ar ya kauda matsalar da kake da shi,ina tunani da tsoro a kwai ranar da Zainab za ta yi maka tawaye ta rabu da k...."Kawai sai ta ƙara sakin kuka da ƙarfin ta.

Abba ya kalli Juwairiya da ta gaji da tsayuwa ƙafafunta har rawa suke yi,ya kuma juya idanun sa ga Daddy da har yanzu yana jin babu daɗi akan maganar da Abba ya yi masa.

"Ka yi haƙuri ka yafe mini na san na yi kuskure da na gaya maka haka,musamman da na riga na mallaka ma shi duniya da lahira,amma abin da kuka yi kamar ba na masu hankali ba,ga in da abin ya kai ku."

Ya yi shiru ko Daddy zai ce wani abu amma sai ya ga ya É—aure fuska don haka ya ci gaba da cewa.

"Kuma sai ya rasa wacce zai aura sai Æ´ar talaka har da kai ka biye mi shi?Haba ta ya ya za'ai kamar shi ya auri Æ´ar talaka.Ai wannan kamar ya zubar mana da mutunci ne b...."

"Wannan kuma sai ka tuhume sa domin cewa ya yi zai aure ta, su rabu bayan ta haihu ya ba wa Zainab yaron.Wataƙila son ta yake shi ya sa ya yi mini ƙaryar haka."

Da sauri A.m ya kalli Daddy ya ce." Ba sonta na ke yi ba Daddy da gaske nake yi,yaron Zainab zan ba ta riƙe ita kuma za mu rabu bayan ta haihu,saboda mahaifiyar ta ma ba ta san tana auren ba."

" What mene kake cewa Abdul! Anya kana da hankali kuwa."Mahaifiyar sa ta ce cikin tsananin razana.

A.m ya cire tsoro ya gaya musu duk abin da ya faru har ɗauke Mama sai da ya faɗa musu,da yadda Baba Sani ya takura wa rayuwar su,da dalilin da juwairiya ta amshi auren sa,sannan kuma ya yi alƙawarin tana haihuwa zai rabu da ita.

Umma ta din ga mata wani irin kallo na mai kama da tausayi ko akasin haka.
" Sam ba ki yi ma mahaifiyar ki adalci ba,duk da cewar kin yi hakan don ki ce ci rayuwarta,amma ta ya ya za ki yi aure ba tare da sanin mahaifiyarki ba?Gaskiya wannan babban kuskure ne da kika aikata,saboda mahaifiyarki Allah kaɗai ya san halin ƙuncin da take ciki."

Umma ta faɗa cikin tsananin mamaki lallai ɗan yau sai abar su,gabaki ɗaya san mai da mutane shashashu,sun ƙullah hakan ba tare da sanin kowa ba,ita kuwa Zainab wata irin banza ce da har mijin ki zai auri mace ya ije a cikin gidanki ba tare da ta fahimta ba.

" Yarinyar tana da kyau da natsuwa amma mai zai saka,A.m ya je gidan wulaƙantattu takala ya auro ta?"Ta faɗa a zuciyarta tana jin babu daɗi a ranta na haɗa jini da talaka da yake son ya yi.

" Kuma sai ka rasa ƴar wa za ka aura sai yar gidan Malam Shehu Abdul kenan son yarinyar kake yi?Bayan ka ce za ku rabu duk da wannan hauka kake yi,ka taɓa ganin in da ɗan wani ya riƙe ɗan wani?"
Da sauri ya kalli ta jin mahaifin sa ya faÉ—i haka,ya ci gaba da kallonta na É—an wani lokaci,yana son ya gano da gaske ne abin da mahaifin sa ya faÉ—a,kasancewar sa mai saurin gane abin da yake zuciyar mutum.

Taɓe bakin sa ya yi don shi bai ji wani abu na so a zuciyar shi dangane da ita ba,ya san dai yana matuƙar son babyn da za ta haifa.

" Daddy ba na sonta sam ba ta a tsarin matar da nake so,saboda ni ban san mace mai saurin kuka da shiru-shiru,wallahi ban aure ta don ina son ta ba,kawai ni na aure ta don ta haifa mini yaro na ba wa Zainab,kuma in sha Allahu sai na nuna mata na san mahimmancin alƙawari,sannan na fara...."

" Rufe mini baki shashasha! In ba son ta kake ba,mai ya sa ka rasa macen da za ka aura ka je ka aure ta?"

" Saboda ita kawai na ji zan iya zaman aure da ita,amma fa na wucin gadi bayan Zainab."Ya ba Abba amsa da sauri.
Chapter 73 · 0% Book details