Sashe 51
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna matuƙar shiri sosai komai ma su tare suke yi ga halin su ya zo ɗaya ba ruwan su da hayaniya,musamman ita da take kullum cikin bege da ƙaunar masoyin ta.
Kimanini wata uku da fara karatun Juwairiya wanda Zainab ta ɗauko ƴan aiki har guda uku sai A.m ya yi tsalle ya kawo ƙauli da ba'adi.
Ganin haka sai ta kori Baba in da aka kawo mata mai jini a jika ta na koya mata girkin amma ba ta kwana don ta na da miji sai dai tun safe in ta zo sai magariba take komawa gida.
Ranar wata Juma'a Juwairiya ta tashi da ciwon kai mai zafi da zazzaɓi ko tashi ta yi sallah ta kasa ga wani irin sanyi da yake shiga cikin ƙashin jikinta ya na nuƙurƙusanta.
Abin takaici gashi suna da test don ana gabda yi masu jarrabawa.
Ganin ba zata iya zuwa ba gashi matar gidan ba ta nan kuma yau A.m zai dawo daga tafiyar da ya yi,wayarta ta É—auka tare da duba numbar ta kiran numbar Hauwa Tukur amma wayar ba ta shiga ba sai ta yi tsaki ta jefar da wayar ta kwanta.
Ta na kwance jikinta na ƙara zafi sosai kamar wuta misalin tara sai ga kiran Hauwa Tukur ya shigo,da ƙyar ta janyo wayar da ke kusa da ita ta kanga a kunninta ta na nishi a wahalce.
"Hello Juwairiya ba za ki zo makaranta ba ne lafiya kin san muna da test ga shi Malam D.d ba shi da mutunci."Hauwa Tukur ta faÉ—a a ranta ta na tunanin mai ya hanata zuwa,kasancewar ba ta wasa da karatu.
" Wallahi ba na jin daÉ—i ne kin san sai da lafiya ake komai.Don Allah ki yi min test É—in in zai yi wu."Ta ba ta amsa ta na kyarmar jiki.
Bayan ta yi mata sallama tare da mata alƙawarin in dai ya yadda za ta yi mata ta kashe wayar ta koma ta kwanta.
Sai misalin shidda na yamma A.m ya shigo babu abin da ta yi masa na abinci.
Ganin halin da take ciki ya ruÉ—e sosai kamar zai yi hauka a tunanin sa ciki ta samu,don haka jiki na rawa ya É—aga waya ya kira likita ya zo ya duba ta.
Juwairiya ta ji hankalinta ya yi ƙololuwar tashi jin ya kira likita ita yadda take jin ciwon gani take kamar ciki ne.
Kawai sai ta ji hawaye ya fara sauka a ƙuncinta don ta san lokacin rabuwar su ya yi daga ranar za su fara irga kwanaki.
Bayan likita ya zo ya yi mata gwaje-gwaje ya sa ta yi fitsari ta kawo masa.
A.m da ya yi zugum duk ya ƙosa ya ji abin da likitar zai faɗa,ya na ta addu'ar Allah ya sa likita ya yi mishi kyakykywan albishir.
"Ga wannan maganin za ka siyo maleria ce ke damunta in sha Allahu tasha magani za ta warke."
Hankalin sa ne ya tashi matuƙa kawai sai ya ji hawaye na son ya zubo a ƙuncin sa yayin da zuciyar sa ta karye da tunanin zai samu ɗa.
Jikin sa a sanyaye ya karɓi takaddar ya fice tare da likitan don ya siyo magani ko kallon ta da take zaune bai yi ba.
Wani wawan ajiyar zuciya ta saki wani irin sanyi ya ziyarce ta jin ba ciki ta samu ba.
A ƙalla sai da ta yi kwana uku sannan ta warke sarai ta shirya ta tafi makaranta.
Suna zaune da Hauwa Tukur ba yan sun fito daga lakca Hauwa Tukur da hankalinta yake kan danna wayarta ta kalle ta da ta zuba uban tagumi ta yi nisa gurin karanta wasiƙar jaki.
"Yawan tunani ba shi da amfani ga lafiya kuma ban ga dalilin da zai saka ki zo makaranta ki zuba uban tagumi,ba yan kin baro gwarzon ki a gida nifa da kika ce baki da lafiya na É—auka ciki ne da ke."
Wani irin tashin hankali ya ziyarce ta ta zare idanunta ta na kallonta.
"Subuhanallahi ciki kuma ni fa ba matar aure ba ce."
Ta faÉ—a tare da gwalalo idanu jin abin da ta faÉ—a yayin da take mamakin mai ya saka ta faÉ—i haka.
Sakin dariya mai sauti ta yi ta ɗauki lemun robar da Juwairiya ke sha ta zuƙa tare da kwashewa da dariya.
"To don Allah meye na tsorata haka sai ka ce na ce kin yi kisa."
Ta faɗa ta na mamakin yadda ta razana haka saboda ta haƙiƙance ma kanta ita matar aure ce,sai dai in ba ta son ta ga ya mata amma ko wa ya kalle ta ya san ta na da aure.
"Haba Juwairiya ko wane mutum ya kalle ki ya san kina da aure kin san a kwai matan da dole a gane matan aure,duba ga yanayin jikinta ki kalle kanki kema kin san bakya son ki gaya mini ne,to ki mai da wuƙar ni ban ce zan gan shi ba bare ki yi tunanin ko zan bashi ƙanwata ne."
Ta ce da tsigar wasa saboda ta na son ta kwantar da hankalinta ganin yadda ta birkice lokaci guda.
Jin abin da ta faÉ—a sai hankalinta ya tashi sosai duk da gargaÉ—in da zuciyarta take mata na kar ta faÉ—a mata halin da take ciki,amma ta na jin lokaci ya yi da za ta daina shanye damuwarta ita kaÉ—ai ta sanar da ita ko don ta samu shawarar yadda za ta cire son maso wani a ranta.
Kama hannunta ta yi ta haɗe da na ta ta kalli ta cikin muryar son kuka ta ce."Tabbas tunanin ki haka ne amma ina buƙatar mu samu in da babu mutane ina da damuwa ina son ki ba ni shawara."
Ganin ta fara kuka sai ta riƙe hannunta suka koma in da babu mutane.
"Tabbas tunanin ki gaskiya ne ina da aure amma auren sirri na yi da mijina na shekara É—aya."
Sai ta din ga kallonta irin kin zare kenan ko kuma baki san mai kike faÉ—a ba ta kasa magana sai kallonta take yi.
Ganin ta kasa yadda da abin da ta faɗa mata sai ta ƙara fashewa da kuka ta na jin wani irin zafi a zuciyara ta.
Hauwa Tukur da ta yi shiru ta na jinjina wannan lamarin mai kama da shirin fim ko hikaya a gare ta!A ranta ta na mamakin ta ya ya za'ai wannan aure ba tare da sanin mahaifiyarta ba!Ita ko wani irin so take mishi?An ya ta yi tunani kuwa mai ya kai ta namiji ba É—an goyo ba ne É—an masara ne ana goyon shi ya na kayan gemu."
Maganar zuci take amma ba ta san maganar zuci ya fito fili ba.
Ta riƙe hannunta ta na kuka sosai ta ce ba yan ta yi murmushi mai ciwo."
Dole ki jero min waÉ—annan tarin tambayoin ni ma na san na yi kuskure,kullum cikin dana sani da kukan zuci nake yi."
Ta saki hannunta ta miƙe tare da juya mata baya ta ƙara ce wa da ita."Allah ya jarabce ni da tsananin son shi sosai,amma A.m ya tsane ni baya sona ni ce mace ta farko da ya tsana saboda a koda yaushe cutarwa ce a tsakanin mu ya na ƙara saka min son shi a raina.
Na san ce wa ban yi ma mahaifiyata adalci ba amma babu yadda zan yi ne Baba Sani yaƙi taimakonmu,gashi ba na son na rasa ta,kuma ko banza auren sa ya ceci rayuwata daga auren Alhaji Tanimu,amma kuma yanzu ina tsoron ranar da A.m zai rabu da ni na san ranar ita ce ranar da fitar numfashina zai yi bankwana da gangar jikina."
Hauwa Tukur da take jin tashin hankali ita mamaki take ba ta da har ta yadda za ta iya saida É—anta,amma sai ta danganta shi da don ba ta san son da yake tsananin uwa da É—anta ba ne shi ya sa ta aikata wannan aiki,da kuma zafin talaucin da take ciki uwa uba Baba Sani da ya ke mugu azzalimi.
Ta nisa sannan ta fara magana cikin mamakin mugun hali irin na Baba Sani.
"Gaskiya na ga wauta da ƙuruciyar ki duk da kin yi hakan ne saboda ki taimaki rayuwarku,amma a kwai kuskure a ciki haba ta ya ya zan amince na auri mutum kuma na zauna a matsayin mai aikin matarsa har na iya wanke mata ƙazantarta wallahi hakan ba zai yi wu ba,na tabbata da kin ƙi amincewa in dai idon A.m a rufe yake ya na son yaro dole ya naimi wata hanyar k..."
"Don Allah ki fahimce ni na san na yi kuskure amma kuma abin da ya faru ya riga ya faru!Ki ba ni shawarar yadda zan saka soyayyata a cikin zuciyar sa,yadda dake ya sa na bayyana miki damuwata saboda friend in need is a friend indeed."
Ta katseta jin ta na ta maimaita maganar da wautar da ta yi bayan ta san hannun agogo ba zai taɓa dawowa baya ba.
"Wane shawara zan baki ni fa ina son naga ranar da wannan lamari zai fasu har na zaƙu da na ga kin yi ciki don a kwai turka-turka kina ganin Zainab za ta yadda ta karɓi yaron ne?shi kan sa bai yi tunani ba domin ya ibo ruwan dafa kan sa ala'mura canzawa za su yi saboda man propose but Allah dispose. Sannan babban kuskuren da ya yi na kawo ki gidan sa Zainab ta sanki ina tausaya masa lokacin da maganar ciki za ta fito fili,don Zainab ba ƙaramin hauka za ta yi masa ba.
Ni yanzu shawarar da zan ba ki shi ne ki ƙoƙarta a ki samu ciki za ki ga yadda komai zai canza."
Saka kuka ta yi ta ce."Shawarar da za ki ba ni kenan?ba ki san waye A.m ba kuma ba ki san Zainab ba shi ya sa kike ganin kamar inna samu ciki zai soni wayar ta ta ciro ta nuna mata hoton A.m da Zainab wanda ta É—auke shi na falon su da suka manna..
A duk lokacin da ciwon son shi ya kamata sai ta ciro hoton ta na gani saboda zuciyarta ta sare da soyayyar A.m ganin irin zuƙeƙiyar matar da yake aure,amma haka ba ya canza komai ta na ganin son shi kamar wahayi ake mata.