← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 86

Sashe 83

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zainab ta kalle shi ta fashe da kuka ta ce." In har kana son zamana a gidan,nan ya zama dole ta bar gidan nan don na tsaneta ba na son ƙara kallonta,kuma har wani abinci kake mata A.m tun da nake da kai ka taɓa dafa mini ko ruwan zafi."

Hunnunta ya kama ya galla ma Juwairiya harara ya ce." Saboda babynmu nake yin hakan kin san mai ciki duk abin da ta ce dole ayi mata,kin san Allah da ke kike da cikin nan in da ana yi ma mutum numfashi to zan sauwaƙe miki yin sa,don haka duk abin da nake yi mata saboda baby ne,kuma da zarar ya fita shikenan."

Ya ce mata da murya sanyayya yana kallon Juwairiya a wulaƙance.

" Gaskiya dole ka yi magana da Abba ta koma gidanku na yarda,ko miliyan nawa zan ba da in har za a kula da ita amma ta bar mini gidana."

Ta faÉ—a masa cikin karayar zuci saboda ganin yadda ta koma ya firgita ta.

Tsaki ta saki ta kalle su duka ta ce." Kan ku ake ji ni kaina na ƙosa na bar wannan gidan da baku san haƙƙin kowa ba sai kanku."Ta juya ta koma falo.

"Yanzu da gaske girkin za ka ka yi mata da wannan daren?"Kawai sai ta saka kuka ganin yana saka doguwar riga.

"Yarona zan yi wa girki karki damu cikinta ya shiga na wata huɗu, kin ga mun kusa yarda ƙwallon mangwaro mu huta da ƙuda."Ya ce da muryar rarrashi.

A lokacin da ya fita kifa kanta ta yi ta din ga kuka sosai baƙin ciki cushe a zuciyarta,tana jin wani ɗaci na ganin ta a gidan,wasu irin abu da suka faru dama waɗanda ba su faru ba ta rinƙa hasasowa,sai ta ƙara sakin wani kukan tana buga kanta da gini.

Da ga ƙarshe kasa zama ta yi ganin uku har ta gota ta sauko ƙasan,sai ta ga a wannan lokacin A.m ya kammala ɗanwaken ya kawo mata,amma saboda muguntar da ta saba ta ce sai ya jira ta ta gama.

Da takaici ya ishe ta komawa É—aki ta yi tana ta kuka sosai a yadda ta ga Juwairiya, daga yau ta ije aiki har sai ta haihu ta bar musu gidan,don ba za ta iya barin ta da shi ba a cikin gidan.

Kamar yadda suka saba kwana a falo haka ta kasance yau ita Juwairiya ba ta yi bacci ba,sai shi da yake ta gyangyaɗi daga ƙarshe bacci ya kwashe shi.

Ta gyara zamanta ta ci gaba da kallo tana karanta lintafin Hausa novel mai suna(Burin duniya na Jamila Lawal Zango Jamcy)Wanda Hamdiya ta tura mata saboda ya rage mata kaÉ—aici.Sai dai tsoro da tashin hankalin da yake cikin lintafin da tausayin Khairi da kuma takaicin doctor Garkuwa ya sa ta ije lintafin, da tsananin tsoro ta kashe wayar gabaki É—aya.

A.m da ya ji kiran salla zubbur ya miƙe ya kalle ta wadda tsoro ya sa ta baccin dole.

Ji ya yi kamar ya shaƙeta da sauri ya haye sama ko tashin ta bai yi ba,saboda takaicin gani girkin da ya yi mata ko guda uku ba ta ci ba.

Ya tura É—akin ya shiga har yanzu bacci take yi saboda bayan kukan da ta sha bacci ya É—auke ta ba don ta so ba.

" Zainab ki tashi kiyi sallah."

Sai ta yi tsuru tana kallon sa yayin da hawaye yake bin gefen fuskarta.

" Na rasa ta yadda zan fito na yi miki bayani ki yarda da ni Zainab."Ya faÉ—a muryar kaukausa domin shi yana ganin bai kamata ta É—aga hankali a kan yarinyar da baya jin sonta a cikin ransa ba.

" Na gaya miki ba so a cikin auren nan na yi shi ne don kawai mu samu ɗa,kuma na yi miki alƙawarin da zarar ta haihu zan cika miki alƙawarin da na ɗaukar ma ki ba ta saki uku."

" Zuciya ce take É—ar-É—ar amma tun da haka ka ce shikenan ka yi ma Abba magana ta koma gidanku."Ta ce mishi lokacin da ta yi hanyar bayi.

" Wannan ba zai yiwu ba domin Abba ya ce dole sai na zauna da ita,amma ni ba zan iya zama da wata mace ba bayan ke,ki yi haƙuri har ta haihu sai mu bar garin bayan na saketa mu koma London sai mun ɗauki tsawon shekaru kowa ya manta mu dawo."

Rungume shi ta yi tare da manna mi shi kis ta ce."Na yadda da kai mijina na san duk wannan matsalar ni na kawo shi,domin da ban biye wa son zuciya ta ba,da son gayu da ƙyalƙyali na haihu ko da ɗaya ne, da baka janyo Juwairiya cikin rayuwarmu ba,na yi takaici sosai ban san cewa kana son yara haka ba,sannan ba za ka iya rayuwa dole sai ka so ka ga ɗanka."

Sai kuma ta sake shi ta sa kuka ta ci gaba da cewa." Kaicona da na bi ruɗin duniya na ƙi bari na haihu ko sau ɗaya ne,ina ma matan da suke shan maganin hana haihuwa don wani buri na su,ko mazan suka umurce su za su daina duba ga irin yadda na tsinci kaina cikin nadama.Don Allah A.m karka karya alƙawarin da ka yi mini,saboda kishin ka zan ije aikina har Juwairiya ta haihu na ƙosa ta fita daga cikin rayuwarmu ba zan iya barin ka kai da ita ba,wallahi jiya da na gan ta hauka ne kawai ban yi ba,saboda duk kyan da na ke da shi na tsorata da ganinta.Ashe haka mata suke canzawa in suna da ciki."

Riƙe ta gam ya yi har cikin ran sa yana jin tausayinta don in ya kalli cikin Juwairiya ji yake yi kamar zai sume,to ina ga ranar da ya fito duniya ya ga ɗan mutum ace na shi.

" Na yi miki wannan alƙawarin ba ki da matsala."

Duk wani abun da A.m zai yi ya kwantar da hankalin Zainab yana yi,abu É—aya ne ya ji sam ba zai iya ba yadda ta hana shi ko da kallon Juwairiya,domin ko motsi ya yi idanunta na kan sa.

Gabaki É—aya ta ije duk wani yawonta da take nadamar yin sa da ta yi,tana zaman gida sai ta yi kwanaki ba ta fito ba.

Duk sadda ta ga cikin Juwairiya da yaƙe ƙara girma, sai ta shiga ɗaki ta yi kuka ta yi kuka har ta ji babu daɗi,watarana sai ta yi ta buga kanta a bango tana nadamar riƙon sakainar kashin da ta yi masa.

Ba ta ƙara shiga tashin hankali ba sai da Juwairiya ta fara kubburi duk da alokacin cikinta wata shidda da sati biyu,hankalinsa ya yi dubu ya tashi kamar zai yi hauka,wanda Zainab ta ka sa gane akan baby yake yi ko uwar baby.

Da suka je asibiti likita ya ƙara tura su scanning sannan jini za a ƙara mata,saboda jininta ya yi ƙasa,take A.m ya ce a iba na shi a saka mata.

Zainab ta tada hankalinta matuƙa tsiya sosai suka yi akan ya siya jini a saka.

Sai dai ba ta yi nasara a kan sa ba, don kwana biyu ya yi ana iban jinin sa wanda aka sakawa Juwairiya,da yanzu ta fara raina kanta ganin yadda take komawa har kammanninta sun fara canzawa,ga ƙafafuwanta da suke kubbura.

Bayan an saka mata jini suka dawo gida Allah ya É—auki wani irin tausayin Juwairiya ya saka a zuciyar A.m,wanda ko juya idanunta ta yi sai ya ji wani madarar tausayinta a cikin ransa.

In yana gida sam ba ya iya zama a ko ina sai falon ƙasa,daga baya ƙarya ya yi wa Zainab cewa Momi ta ba shi umurnin ta koma sama,in ya so a ba ta ɗaki ɗaya ta zauna madadin zaman ta a ƙasa.

Zainab hankalinta ya ƙara tashi saboda tun da ta dawo ta ga duk sun canza mata suna wani nan-nan da ita.

Kullum suna sintiri gurin kawo mata abinci na ƙwaɗayi,haka Momi da Abba kullum sai sun kirata sun ji lafiyarta.

Ta raina kanta matuƙar gaske kullum cikin nadamar abin da ta aikata take.Ga tarin dukiyar da take buri ta samu ta samu don yanzu Ƙasar ingila take son ta haɗa hannu da asibinta,kuɗi kam ba ta da matsalar su amma babu kwanciyar hankali,saboda ta lura yanzu sam hankalin A.m ba shi a jikinsa,da ta yi masa magana ya ce zuwan baby ne.

A.m da Zainab suka shirya zuwa waje suka yo siyaryar kayan baby,wanda ita kanta Zainab ba ta san iya yawan kuÉ—in da ta kashe ba.

A.m sai haÉ—a tarin dukiya yake yi ma Juwairiya har da wasu share É—in sa na waje yake son ya bar mata,saboda kar in suka rabuya rage mata jin zafin rabuwa da baby.

Ita kanta Zainab ta yi masa alƙawarin za ta ba ta dukiya masu yawa, ita dai burin ta ta bar mata A.m da babyn da yanzu take jin ta fara son sa a cikin ranta,don son da za ta nuna masa shi kawai zai ƙwato mata martabarta a gurinsa.

Bayan Juwairiya ta dawo sama wata ƙaryar ya shirga ma Zainab akan dole yanzu ya rinƙa kwana da ita saboda cikinta da ya shiga wata na bakwai.

Da fari ƙin amincewa ta yi amma daga baya sai ta yarda akan za su dun ga kwana dukansu tare.

Sai dai A.m yaƙi mata ya ɗan nuna mata hakan ba zai yiwu ba ta amince,don ta san yanzu in dai ba rashin tausayi ba bazai kalle ta ya buƙaci wani abu daga gareta ba,duba ga yadda ta koma.

Juwairiya na ɗanɗana kuɗarta duk wani wahala da take ba ma mutanen gidan,da tsiwa kan dole ta watsar domin yanzu ta kanta take yi,kusan kullum cikin wahala take domin cikin na matuƙar ba ta wahala sosai,kamar za ta mutu ko nishi ta yi sai ta ji wani azaba,ita kam ta sheda mutuwa za ta yi,shi ya sa kullum take kuka sosai akan ya kai ta gurin Mama,saboda ta san mutuwa za ta yi.

Ranar wata daren Alhamis A.m hankalin sa ya tashi matuƙa ganin yadda take sauke numfashi sama-sama.
Chapter 83 · 0% Book details