Sashe 7
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
fata ta yi. Zainab ta na da kyua na nuna wa tare da mannata a hoton irin matan nanne waɗanda ka na ganin su kaga hutu,ko kai mace in ka hansu sai ka yaba.Doguwa fara ga gashi da kyan diri sannan ta na ƙara zuzuta kyanta da mayuka na gyara gashi da fata da kuma sabulai masu tsada.Ita dai ta yadda ta bautawa jikinta ko da za ta karar da wunin ranar ne,shi yasa in ka kalleta dole ka ƙara. Ta na da girman kai a gurin samari ga ta da farin jini,amma duk saurayin da yazo za tace bai yi mata ba.Mahaifinta ya na matuƙar son yaga ya yi mata aure don ta haifa mishi jikoki,shi yasa kullum yake lallashin ta akan ta fidda miji daga cikin yaran masu da shi da alhazawan da suke neman ta,amma taƙi ita ganin ta aure taƙurawa rayuwar tane.Tafi son rayuwar hutu da jin daɗi sannan ba ta son taƙura da shishshigi ga lamarin ta. Abin da ƙara tsoratar da ita ganin ƙawarta Nihal da ta yi aure shekara ɗaya da ya wuce.Ta na da kyau da gayu,amma tun da ta yi aure ta haihu ta zama ƙatuwa ga tumbi da ta yi,sannan ƙirjinta ya zube,kullum cikin aikin yara ko a gurin aiki ta rage ƙokari,ga takurawa ɗan tiktok ɗin da take yi mijinta ya hana. Wannan dalilin yasa ta ƙara tsanar aure ta na gani kamar koma baya ne a rayuwar ta,ganin mahaifinta na da kuɗi kuma ita ma ta tara kuɗin da za ta ɗauki nauyin kanta.Ta saka ma ranta ba za ta yi aure ba,in ma dole sai ta yi aure to ba za ta yadda ta haihu ba kawai za ta yi rayuwar hutu ne don gani take kamar tara yara wahala ce gata likita kuma bata son jikin ta ya canza. Duk mazan da suke zuwa gun ta kullum cikin kushe su take yi ta na yi musu wulakanci,kuma in auren za ta yi tana son namji mai kyau wanda ya fita gayu da tsafta.Ba ta taɓa jin soyayyar wani a cikin zuciyar ta ba,shi ya sa take wulaƙanta duk wanda ya zo gurin ta. Kwasam!Ta haɗu A.m a ranar wata daren alhamis da misalin ƙarfe shidda saura kwata agogon birnin a ƙasar London,ta raka yar gidan ƙanwar mahaifiyar ta siyo kaya.Suna zaune a cikin jirgin za su dawo A.m ya shigo hannunsa riƙe da waya da cingam a bakinsa ya na taunawa a yangace.A.m na son cin cingam kamar mace hakan ya samo asali ga matar Alhaji Sama'ila da ta rike shi ta na son cin cingam.Hausawa sun ce zama da maɗaukin ƙanwa shi ke kawo farin kai.Aiko haka ta kasance A.m ya koya cin cingam a gurin ta duk lokacin da ya ci abinci ko ransa yake a ɓace,sai ya huce a kan cingam ɗin. Ran shi a ɓace yake akan taron da suka yi da safe a companin su,sam yadda yaso taron ba haka ya kasance ba,wannna dalilin ya saka shi baro London bai kammalla abin da ya kawo shi ba. Ya shigo cikin jirgin fuskar sa kamar an yi mishi mutuwa,bai kalli kowa ba sai kujerar sa da ya nufa ya na murza tafin hannun sa tare da tauna cingam ɗin da ƙarfi saboda fushin sa ya ragu. Wani irin kallo ya watsa mata ganin ta zauna masa a kujerar sa,da fari ya ɗauka makauniya ce saboda kowa da numbar kujerar sa amma ganin ta na riƙe da waya sai ya daka mata tsawa da ƙarfi yace."Za ki iya tashi a ƙujerata ki nemi taƙi tunna baki je makaranta balle kin san yadda ake irga numbobi." A hatsale ta miƙe tare da faɗin."What."Ita sai yanzu ta kula ba'a gurin ta ta zauna ba,saboda hankalin ta na kan wayar ta sanda ta shigo.Ranta ya ɓace jin kalaman sa sai kawai ta ɗaga hannunta da nufin ta wanka ma mutumim da ya kira ta jahila mari,sai ya banbance waye ke da jahilcin atsakanin shi da tunna idanunsa sun kasa gane mishi wayayya mace mai a aji da class,wacce take tashe a tiktok.