← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 86

Sashe 44

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya na isa get ɗin maigadi ya sheƙo da gudu ya na faɗin." Ka yi haƙuri ina bayi na zaga.Wannan wa ne mahaukaci ne yake ƙwanƙwasa ƙofa Allah ya sa lafiya."

A.m bai kalle shi ba ya buɗe kofar sai kuma ya ƙame cikin tsananin mamaki ganin Baba Sani a tsaye ya na ta mazurai.

NI MA NA YI MAMAKIN GANIN SA SABODA NA SAN BA ALKHAIRI YA KAWO SHI BA NA IJE BIRONA DON NA HUTA.

KUCI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN KAR KU GAJI BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN LINTAFIN.

SAKACINA KO HALIN MAZA

TAKU

JAMLA LAWAL ZANGO

TUNATARWA

DON ALLAH ƳAN'UWANA MATA KADA KARATUN LINTAFI YA ƊAUKE HANKULANMU MU MANTA DA BAUTAR UBANGIJI,KU TUNA ALLAH YA HALICCE MU DON MU BAUTA MASA NE.

YAU TAKE JUMA'A KAR A MANTA KARATUN SURATUL KAHAFI ALLAH YA BA MU ALKAIRUN DA KE CIKINTA AMIN

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha shidda.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 21*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

A.m ya tsaya cikin tsananin mamaki ya na kallon Baba Sani da ya ci magani fuskar sa babu walwala ko kaɗan, alamun da rashin mutunci ya zo koma fiye da haka don a wulaƙance yake kallon A.m da yake jin kamar ya kai mishi bugu.

" Uban me ya kawo wannan mara mutuncin gidana ya akai har ya san gidana."

Irin tarin tambayoyin da A.m yake yi ma kan sa wanda ya kasa amsa ko da guda É—aya ne.
" Kai Malam na ga ka na kallona kamar ba ka gane ni ba."
Baba Sani ya ce cikin ɗaurewar fuska ya na ƙarasowa gurin A.m da ya harɗe hannun sa a ƙirji ya na kallon sa a wulaƙance burin sa ya ji mai yake tafe da shi.

"Ba zan kalle ka ba ka san halina ba ni da mutunci mai ya sa ka zo gidana,bayan ka san duk abin da muka yi sirri ne a tsakaninmu,shi ne za ka biyo ni har gida saboda kai tantiri ne."

A.m ya faɗa fuskar sa babu sauran fara'a ji yake kamar ya shaƙe sa,domin baƙin cikin dake cikin zuciyar sa.

"Ban sani ba na ce ban sani ba wallahi kamar yadda kake faÉ—in ba ka da mutunci na fika,don ni yawo nake a tasha da gidan karuwai kai ko ina tunanin iskancin na ka haye ka yi,in ban da iskanci Æ´ar É—an uwana a gidan ka kake tambayata abin da ya kawo ni gidan ka.Ai tushiya mafarin dawa."
A.m ya zare idanun sa ya na kallon shi ganin yadda yake ɗaga murya ya na son kowa ya ji,duk da unguwar ta su ta manya ce kowa ya na cikin gidan sa,amma A.m hankalin sa ya tashi ƙwarai sai ya shiga waige-waige ba yan ya galla ma maigadi harara dake tsaye ya na kallon su.

Sum sum ya wuce sannnan A.m ya taso ma Baba Sani cikin hargowa zai make shi,don yadda yake jin zuciyar sa na tafasa kai dukan shi ne samun sauƙi.

Ganin da gaske dukan shi zai yi sai ya masa da sauri,amma yaƙi wucewa a gurin faɗa yake ya na hargowa tare da nuna A.m,da yake jin zuciyar sa kamar za ta yi bindiga.

A.m ya ƙara kai ma Baba Sani duka daidai lokacin da motar A.k ta sawo kai,da sauri ya yi parking tare da fitowa ya riƙe A.m da yake hargowar dukan Baba Sani.

" Ba ka da hankali ne A.m ka san me kake shirin yi ƙanin mahaifin Juwairiya za ka daka karka manta shi ya ba ka aurenta?"

A.k ya faÉ—a don ya kwantar ma A.m hankali ganin yadda ya zuciya.
"Allah ya sa mahaifinta ne yazo ba shi ba,tunna yaƙi kama kan sa wallahi zan kulle shi igiya ta yi rara."

A.m ya ce cikin zafi yayin da yake jin kamar ya shaƙe shi,shi baƙin cikin sa yadda akai har ya gane gidan sa.
" Bar shi A.k ka bar shi ya yi min rashin mutunci dama na lura ba shi da mutunci,amma tsoratar war sa ba za ta yi tasiri a cikin zuciyata ba.

"Ka gaya mishi in ya na son lafiyar sa, to ya bar nan kar kuma ya ƙara gangancin wucewa ta hanyar gidan,nan ballantana ya yi tunanin ƙwanƙwasa min gida,ka san ba shi da mutunci da ba ni ya samu ba haka zai fasa ƙwan kowa ya ji."
A.m ya ce ya na kallon sa da yake ta karkaÉ—a jikin sa alamun irin da rashin mutunci na zo ko fiye da haka.

" Ka kwantar da hankalin ka bai kyauta ba duba ga irin halaccin da muka yi masa,amma ka tsaya mu ji mai yake tafe da shi."

Ya ce da A.m sannan ya juya ya kalli Baba Sani ya ce."Mai ya sa ka yi haka ba yan mun yi waya da kai na ce maka zan zo."

Baba Sani ya kalle shi tare da kaÉ—a kan sa ya na ce wa."To dussa ne ni da za ka shanya ni kwana biyu na jira ka ba ka zo ba,shi ya sa na yanke shawarar na je gurin wannan É—an mara mutuncin komai zai tafi daidai."

Tsaki A.m ya yi ya ce da shi." Ai ko in ka ƙara gangancin zuwa ƙofar gidan nan ni ne ajalin ka,don na tsane ka tsana mai tsanani mugu kawai wanda ya kasa riƙe ƴaran wan sa."
A.k ya kalli Baba Sani ya ce." To wai tsaya don Allah mene ne ba mu yi maka ba,za ka zo ka dami rayuwar mu?Kuma na gaya maka zan zo har gida aiki ne ya yi min yawa kai kuma mara haƙuri."

"Oho koma me zaku ce kuce amma ni ba ruwana gara ku tsaya ku ji mai yake tafe da ni ba wai ku tsaya ɓaɓatu ba."

Ya ce ya na girgiza jikin shi har da ƴar waƙar shi irin na cikakkun ƴan bariki.

A.m ya watsa mishi mugun kallo ya na jin wani irin tsanar shi mai tsanani ta na zagaye duk ilahirin jikin sa ya ce.

" Ko ma me ya kawo ka ka ɓace min a ƙofar gidana ko na kira ƴan sadda su tafi da kai."

"Sojoji za ka kira ba Æ´an sanda ba kuma abin kunya a gare ka take,ka kulle surukin ka don ko banza na gama da kai tun da Æ´ar wana kake aure shi ya sha nono ya saki na kama."

Ya ba A.m amsa jin abin da ya faÉ—a babu ko É—igon damuwa a zuciyar sa.
A.m ya yi ƙuta ya ce." Allah ya tsare ni na haɗa zuriya da kai dangin matsiyata,ai ko ba mata a duniya gara na zauna ban yi aure ba da na auri zuriyar ka jinin matsiyata dangin talauci."

Ya faɗa cikin ɓacin rai ya na jin kamar ya shaƙo shi ya gama masa aiki,don ya ƙara masa baƙin cikin da ke cikin zuciyar sa.

" Ok to haka kace ko ɗan ƙaruna to sako min ƴar ɗan'uwana wacce kuka yi auren kwangila da ita,dama na zo na tuna maka da yau saura wata biyu da kwana shirin da takwas da yini ɗaya,amma fa ban da kwana auren kwangila ya ƙare ma'ana kuɗin ka sun ƙare shekara ɗaya ka iba,kuma waɗannan watanni biyu da kwanaki suka rage sai a shirya sako min ƴata,don Juwairiya ba ta da uban da ya fini."

A tare suka buɗe baki tsananin mamaki ya kama su ko kaɗan ba su taɓa tunanin haka zai faru ba,lallai Baba Sani ya cika tantiri ɗan duniya ne wanda ya zama lamba ɗaya.

A.m cikin fushi ya taso kan sa ya na faÉ—in." Baka da hankali matar ta wa kake maganar kwanakin rabuwarmu,kai za ka sake ta ni nake da ikon sakinta,kuma babu É—an iskan da ya isa ya sakin min mata.

Ya numfasa ya na jin wani irin tashin hankali da mamakin sa ya ci gaba da ce wa."Kuma da kake maganar haka auren ta na yi don ta haifa min yaro,ammma ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba shi ne har za ka zo ka ce wa'adi ya cika?To na ga uban da ya isa ya sakin min mata."

" Allah ko ɗan zamani hauka kake yi ka yi abu da ƙuruciya ni kuma zan nuna maka da wanda ya riga ka shan iskar duniya,ya girme ka ko da da sakan ne.Bari kaji lokacin da ka zo nai man auren Juwairiya na bi dindigi na gane kai ko ɗan waye da duk wani labarin ka,har da asalin matarka da komai na ta na sani zan iya zuwa gurin aikin ta na kai mata recording ɗin da na yi,lokacin da ka zo neman auren Juwairiya har ma da na ɗaurin auren ku."

Sai suka zare ido jikin A.m ya yi sanyi matuƙa har ya kasa magana don ya cika tantiri na gaske!

Ganin yadda maganar sa ta razana su sai ya yi dariya ya ciro wayar sa ya kunna recording É—in suna ji,babu wanda ya iya ko tari a cikin su sai tsantsar razana da A.m ya ji musamman a ce ya kai ma Daddy kamar yadda ya yi ninya.

A.k ya gyara tsayuwar sa ya na jin wani wani irin tashin hankali ya na ziyartar sa,wani irin gumi yake jiƙa shi don ko kaɗan bai yi tunanin Baba Sani ya na da wannan wayon ba,lallai sun yi boko mai zurfi amma shi ya nuna musu aiki da shi.

" To kun shirya saurara ta ko na tafi don ni ba na son ɓata lokaci."
A.m shiru ya yi ya ɗauke kan sa ji yake kamar ya fisgo shi ya danƙara wayar da ƙasa.
Chapter 44 · 0% Book details