← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 86

Sashe 60

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun kafin ta dawo gida take jin wani irin jiri kamar za ta faÉ—i! Ko da ta dawo gida kwantawa ta yi saboda ciwon da mararta take yi,yayin da ciwon yake ci gaba kamar ana tsira mata allura.

A haka ta kwana kamar za ta baƙunci lahira, duk yadda ta so ta ɗauki waya ta kira Hauwa ta gaya mata za ta mutu,saboda Zainab na nan A.m ko kallonta ba zai yi ba,amma ta kasa saboda ciwon mutuwa da take ji.

Washegari ko É—aga É—an yatsarta ba ta iya wa sunan Allah kawai take faÉ—i a bakinta da yake motsawa,tana kukan rabuwa da Mama ba tare da sun yi bankwana ba.

Jinin dake zuba kamar an buÉ—e famfo ya sa ta gane mutuwa za ta yi,sai ta fara maimaita kalmar shahada numfashinta na É—aukewa.

Zainab da duku-duku ta fice asibiti saboda a kwai wani bawon Allah da za ta yi mata aiki da misalin biyar da rabi na safe,tun jiya aka so ayi aikin sai dai an kawo shi ta riga tabar asibitin,kuma ƙa'ida ne in har ta koma gida ba ta dawowa.
A.m dake zaune a falo ya na kallon news mamaki ya kama shi ganin har wannan lokacin ba ta fito ba ta É—aura abin karya.

Miƙewa ya yi tare da saka takalmi ya nufi ɗakinta.

Halin da ya ganta ya yi masifar É—aga mishi hankali,ba tare da wani tunani ba ya taitayeta ya saka a mota ya nufi asibiti da ita.

Da ƙyar aka samu aka tsaida jinin bayan cikin ya fita.Hankalin A.m ya tashi gani yake kamar mutuwa za ta yi wani irin tausayin ta ya kama shi,ya na jin bai yi mata adalci zai barta ta mutu a ɗaki.

Zura mata ido ya yi cikin tausayi ya na shafa kanta.Da sauri ya kamata ya riƙe tare da tallabota ganin ta buɗe ido.

Juwairiya zuciyarta ta buga ganin likita ya shigo riƙe da fayal a hannun sa,tsananin tsoro ya cika mata zuciya don ta san yau a sirinta zai tonu.

A hankali A.m ya maida hankalin shi kan likitan da ya miƙa masa fayal,ya ba masa bayani da harshen turanci duk da cewar Bahaushe ne shi.

" Ina baka haƙuri na zubewar baby don madam ta yi ɓari ne,har sai da muka yi mata wankin ciki.Ga waɗannan maganin za ka siya an sallame ta."
Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi riƙe likitan ya yi tare da jijjiga shi." Mai ya sa ka bari cikina ya zuba ka san shekara nawa na yi ina son na haihu?Wallahi sai kun dawo min da cikina don ba zai yiwu ba!"

A.m ya faÉ—a ya na naÉ—e hannun riga zai yi dabbe gani yake kamar gazawar su ya sa cikin ya fita.

" Am sorry wallahi bamu da hannu a cikin zubewar cikin na nan! Amma na yi mamakin yadda kake son kaga ka haihu matar ka ta iya zubda cikin dake jikinta,don bincike ya nuna mana magani tasha mai ƙarfi har cikin ya fita."

Sai A.m ya kalle shi kamar mahaukaci ko bai fahimci mai yake nufi ba,ya kuma juya ya kalli Juwairiya wacce ta bayyana gaskiyar zargin da yake mata,saboda yadda ta yi tsuru-tsuru na rashin gaskiya.Wani irin shaƙa ya kai mata cikin tashin hankali.

Zainab da ke tafe a cikin motar ta tana tuƙi cikin tsananin nishaɗi,sakamakon ta yi aiki cikin nasara wanda hakan yake saka ta tsananin farin ciki a duk lokacin da ta yi aiki.
Wayarta ta É—auka ta kira layin A.m amma har ta yi masa kira biyar bai É—auka ba.
Ko da ta iso haka kawai sai ta ji gabanta ya faÉ—i.

Maigadi ya wangame mata get ta shiga ta yi parking da sauri ta shige ciki,saboda yunwa take ji matuƙa.Da fari ta so ta fara cin abinci amma sai ta ga rashin dacewar hakan ta shige wanka.

Bayan ta fito tana ɗan dube-dube a cikin dirowar gadonta sai ta ga wani magani an ɓoye shi a cikin dirowar.

Da sauri ta buÉ—e gabanta ne ya buga dam! Sa'ilin da ta ga sunan dake manne a kwalin maganin.

" Maganin É—aukar ciki da wuri."Ta maimaita sunan maganin da Hausa.
" Me A.m yake yi da shi bayan ni ba na haihuwa?"

Tambayar da ta yi ma kanta kenan amma ba ta da amsarta.
Wayarsa ta gani duka uku a gida bai É—auki ko É—aya ba sannan ba shi a gidan.
Juwairiya sunan da ya faɗo mata a rai kenan ta saki wani irin ƙara,da sauri ta sauko har tana faɗi ta mulmulo amma ba ta kula ba.

Wayam babu ita sai wayarta dake yashe a kan gado.Da sauri ta É—auki wayar duk da ta san a halin da take ciki ba za ta iya karanta komai ba.

TO FA ƘARA! ƘARA!! ƘARA !!!

KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI

SAKACINA KO HALIN MAZA

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 27*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Ta na riƙe da wayar cikin tsananin tashin hankali yayin da jiri yake iban ta da ƙyar take iya buɗe ƙwayar idanunta.

Sai dai duk iya iyakan ƙoƙarinta don ta gano pattern ɗin da ta saka wayar,amma ta kasa har ta haƙura za ta kwaɗa wayar da ƙasa sai kuma ta fasa,ta ƙara kwatantawa sau biyu cikin ikon Allah a na biyun wayar ta buɗe.

Bincike ta fara yi a wayar wanda iya yinta ba ta ga wani abu da zai dasa mata zargi ba,saboda Juwairiya ta adana duk wani abin da ya shafi A.m a cikin wayar ta ɓoye shi.

Ta yi nufin ta ije wayar sai kuma wata dubara ta faÉ—o mata ta danna numbobin A.m.

Tana fara danna numbobin sai ga numbar A.m ta fito ɓaro-ɓaro an yi saving ɗinta da rubutun larabci,wanda iya ƙwaƙwanta ta yi ta gane mai sunan yake nufi,amma ta kasa saboda rubutun babu wasulla,ga shi karatun arabin na ta an yi ɗan cikin cokali.

Durƙushewa ta yi a gurin tare da saka wani gigitaccen ƙara,kamar wata mahaukaciya ta fara rotsa,duk wani kayan ƙawa dake cikin gidan tana ƙunduma ashar.

"Wallahi ku dawo gidan nan nice ajalin ku sai na kashe ku duka mundin na gane cin amanata kuke."

Gurin mai gadi ta nufa kasancewa yau Lantana ta na hutun ƙarshen mako da take yi.

"Kai ina A.m ya yi bayan gida a buÉ—e sannan Juwairiya ita ma ba ta nan?"

Jikin sa ya kama rawa dama tun da yaga Am ya fito da Juwairiya a hannun sa,ya sha mamaki ganin tana matsayin mai aiki ya É—auko ta.

Sai ya ƙara kallonta ya ga yadda ta birkice kamar wacce aka kwanto daga turu, tana zare ido ai ba za a ji mutuwar Sarki a bakin sa ba.

" Hajiya ban sani ba da yake na zaga bayi yau na tashi da motsawar ciki."Wani wawan mari ta sakin mishi.

" Banza wawa kawai banga amfanin aikin ka ba."

Ta juya saboda ba ta cikin yanayin da za ta iya wani dogon magana.

******
A.m da ya shaƙe ta tamkar zai kaita lahira yana jin zai iya kashe ta,saboda tsabar tashin hankalin da yake ciki.Ga baki ɗaya idanun shi sun yi jajur tamkar garwashi wuta,ya canza kalar da ba ta taɓa sanin yana komawa ba.

Da ƙyar take kakari saboda wahalar da ta sha,ga kuma A.m yana shirin kaita lahira ba tare da kwananta sun ƙare ba.

" Uban me na yi miki da za ki kashe min yaro?Da kuÉ—ina na siye rayuwarki a she ke kike hana ciki ya shiga jikinki? Na rantse yadda kika salwantar min da yaro sai na kashe ki."

Juwairiya da take jan numfashi da ƙyar idanunta sun yi gulu-gulu,domin A.m ya yi mata shaƙa ba na wasa ba.

Likitan dake tsaye yana kallon A.m da ya zama mahaukacin ƙarfi da yaji,tsoro yake ya matsa kusa da shi kar ya illata shi,amma da ya ga yana shirin kisa,sai ya matsa tare da riƙe shi da ƙarfi ya ce."Ma za ki tashi ki fita don ki ceci rayuwarki."
Duk da ba ta jin ƙarfi a jikinta amma haka nan ta ruga,daidai lokacin da A.m ya ture likitan ya faɗi ƙasa ya bugu da bango,ya ɗauki wani ƙarfe dake gefe ya ɗaga zai maka mata.

Da sauri ta fice daga ɗakin cikin tashin hankali, tana jin kamar ta sume jikinta babu daɗi,amma ya zama dole ta ceci rayuwarta,don yau ta ƙara tsoron A.m sosai a ranta.

A.m da haushi ya ishe shi ganin Juwairiya ta gudu,ya san ko ya duba ta ba zai gan ta ba,saboda asibitin bene ne ga lungunan dake cikin asibitin,ƙarfen da ya yi ninyar maka mata shi ya buga ma likitan,tare da ficewa da sauri yana neman ta.

Sai dai ya nemeta sama da ƙasa bai ganta ba ƙara ya saki cikin ƙaraji, ya rantse yau da ya ganta sai ya raba ta da numfashinta,sannan kuma sai ta gaya masa dalilin ta na zubar masa da ciki.

Ya kai ma iska naushi cikin takaici yana dunƙule hannun sa,ji yake kamar ita yake duka.Allah ne kawai ya taimake ta da ta gudu da yau sai dai wata ba ita ba.

" Wayyo Allah dama ina haihuwa da gaske zan iya haihuwa?"

Ya daɗe a gurin yana ganin kamar za ta fito daga ƙarshe ya shiga motar sa,wanda Allah ne kawai ya sa ya iso gida.

Sai dai yana shiga cikin gidan ya tsaya cikin tsoro ganin an yi ma gidan kaca-kaca,komai na gidan an fasa hatta tv dake manne plasma duk ta yi raga-raga da su.
Chapter 60 · 0% Book details