Sashe 28
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Yauwa ina motata kuma a ina gidan yake sannan kamar yadda ba ka son matar ka ta sani haka iyayenka kenan ni ne waliyin ku duka ba matsala in ma ka na son a É—aura yanzu ba matsala."
Tsabar takaici ya sa A k yaƙi ce wa komai don ya fahimci jahili ne ku kuma son kuɗin ne ya rufe mishi ido yake faɗin ya zama waliyin su duka,sai shi ma ya miƙe ba tare da ya ce mishi komai ba A.m ne ya miƙa mishi takadda ya ce ga shi duk abin da kake son ka sani ya na ciki.
Zai fita A.k ya kalle shi ya ce " Ai ya kama ta a kira Juwairiya mu gaya mata ko in ce ka yi mata bayani ka san waƙa a bakin me ita tafi daɗi."
A.k ya ce mishi cikin gatsali shi har ya fara jin kunyar ta tun kafin ta fito haka kawai daga haÉ—uwa sau É—aya sai su zo mata da wanann tatsuniyar.
" Baku da matsalar ga ya mata ita É—in banza ai gaba ta kai ta."Ya É—an matso ya na cewa." Dama wannan É—an iskar tsohon ba ya bani wasu kuÉ—in kirki yau zan mayar mishi da kayan tsiyar shi,ana harkar kuÉ—i me za' ayi da tsiya ai ni mutuwar mahaifin ki gaba ta kai ni gobarar Titi a Jos."
" Ga ra dai ka kira ta shi ya sanar mata."A.k ya ce shi dai A.m bai ce komai ba sai dai ya ji wani iri lokacin da Baba Sani ya fita daga É—akin ya na faÉ—in bari na dubo ta shegen yawo ne da ita ai kai da zama za ka yi da ita sai ince baka dace mata ba."
Juwairiya ta na duƙune a murhun gawayi ta hira wutan yafi sau ba adadi amma da ta hura sai ya mutu muɗis,kusan kuka take son ta yi don har ta fara hawaye ganin wutar ta taƙi kamawa ta miƙe tsaye tare da zura mata ido,ji take kamar ta ɗora hannu aka ta yi ta ihu.
Ta takaici ta kalli ledar taliyar da take son ta dafa ma Mama ba ta jima da dawowa daga asibiti ba take son ta É—ora musu abinci da ruwan zafi ta kai musu.
Kawai sai ta ki muryar Baba Sani ya na magana tare da ƙoƙarin shigowa duk da ba ta ji me yake faɗi ba,amma ta tsorata matuƙa gani take kamar zai ce ta dafa taliyar ya ɗaura aurenta.
" Juwairiya ina kike ashe dama ke jarina ne?Oh ikon Allah dare É—aya Allah kan yi bature."Oya maza biyo ni kika abin mamaki aike kin samo mana can jin rayuwa Juwairiya yarinya É—iyar albarka."
Cikin rashin hayyaci ta tsaya ta na kallon shi sam taka sa fahimtar wai yau Baba Sani yake ce mata Æ´ar albarka,sai ta fara shakkun ko ya zare ne jikinta ya fara rawa ta matsa nesa da shi,ta na karanto duk addu'ar da ta fito bakinta.
" Ke ban san hauka maza wuce kina da baƙi a falona kuma wallahi in kai min hauka,zan iya ajalin ki kin san bani da wasa akan kuɗi gara ma ki kiyaye!Maza wuce."
Da sauri ta ruga zuwa shashinsa jikinta na kyarma haka kawai jikinta ya ba ta Alhaji Taminu ne ya zo,sai ta rintse idanunta ba ta son ganin shi a haka ta faÉ—a É—akin tare da sallama wanda na yi tsammanin a zuciya ta yi,don ko ita kanta ba na tunanin ta ji.
Tsayawa ta yi a É—akin ta kasa buÉ—e idanunta sam ba ta son ganin fuskar sa mai kama da biri.
Wani ƙamshi wanda ta shaƙe shi a rayuwarta wanda ba za ta taɓa manta mamallakin ƙamshin, ba har iya tsawon rayuwarta,tun daga ranar da ta shaƙe shi take jin ƙamshin a jikinta har zuwa yau da ta haƙiƙance ma kanta lai-lai wannan mamallakin ƙamshin,mai sanyaya zuciya da kawo nishaɗi ga duk wanda ya shaƙesa ya na kusa da ita,musamman da ta ji sautin da zuciyarta take ta na bugawa da ƙarfi kamar za ta fito fat!Fat!!Har sai da ta dafe gurin.
A hankali ta sauke idanunta da suka kaÉ—a sukai jajur saboda wahalar hura wuta da tasha,duk da taji an kira sunan ta wanda ta gane ba muryar sa ba ne saboda ko tari ya yi za ta gane muryarsa,amma sai ta tsinci kanta da É—ora idanunta a kansa yayin da idanunnata sukai rau-rau sun canza kala suna ba da wani tarwatsi a cikin su.
A.m da ya ji shigowar ta duk da ba ta yi sallama ba amma ya ji an buÉ—e kofa an shigo,sanann kiran sunan ta da A.k ya yi sai ya kasa É—aga idanunsa ya kalleta,duk da ya na son ya kalli wacce yake so ta zamo É—a ga abu É—aya tal mafi soyuwa a gareshi don ko sun rabu aba' a sake ma tuwo suna.
"Ya ilahi! Allah na roƙe ka ka farkar da ni daga mafarkinsa da nake,kuma wanann ya zama na ƙarshe tunna na kusa zama matar wani."Ta faɗa aranta ta na ƙoƙarin mai da hawayen da suke son bayyana ɓoyayyaen lamarin da ke cikin zuciyarta.
" Juwairiya ki zauna mana."
A.k ya ce ganin hankalinta ya tafi wani gurin ga mamakinsa sai ya ga ta nemi ƙasa ta zauna tare da saukar da kanta ƙasa.
Gaishe su take son yi amma ji take kamar babu harshenta a cikin bakinta ta ƙara buɗe bakinta amma ta kasa.
Ganin sun yi shiru duka sai ta ƙara ƙasa da kanta ta na kallon kafen ɗin dake ɗakin tamkar ta na son ta gano ko an maguɗi gurin yin sa.
A.k ya miƙe ya kalli A.m da yake ta danna wayarsa amma a zahirin gaskiya bai san me yake dannawa ba, tunanin sa ta ina zai fara kuma ta fahimce shi,shirun da ya yi ya na son ko A.k zai yi mata bayani amma sai ya ga ya miƙe.
" Bari in jira ka a mota in kun gama tautaunawar ina mota."
Ya fice ya na girmama lamarin da suka zo da shi. " Juwairaah! Babu gaisuwa wataƙila kin manta ni ko."Ya faɗa don rashin sanin ta in da zai fara.
Ta É—ago idanunta ta zuba mishi amma ba ta ce mishi komai ba,sai dai a ranta ta ce." Ta ya ya za'ai na manta da kai bayan ka tafi da zuciya da ruhu gangar jikina kawai ka barmin,amma to mai ya kawo shi gidammu wanda har Baba Sani ya yadda na zo gurin sa.Aurena yake son yi?".
Ta tambayi kanta sai ta yi saurin kawar da wannan bahagon tunanin ta ce " Kai ina wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa."
"Wai ni kurma kika zama bayan rabuwarmu?Ko kina mamakin ganina ne"
Ya É—an tambaye da hasala a ranshi ganin yadda take basar da shi kuma ya tsani hakan.
" A'a ai ba'a mamaki da ikon Allah."
Iya abin da ta ce kenan ta ƙara naɗe bakinta ta yi shiru tanani fal a zuciyarta.
Ganin ta tafi wani tunanin daban sai ya ce " Haka ne ba'a mamaki da ikon Allah don haka kar ki yi mamakin na zo nai man aurenki amma fa na kwangila auren shekara É—aya nake son mu yi dake kuma cikin sirri."
Juwairiya ta É—ago kanta da sauri ta kalle shi a wannan karan ba tare da ta ji nauyin sa ba." Aurena zai yi amma na kwangila mai hakan yake nufi?Sannan kuma cikin sirri to suwa ye ba' a son su san auren?"
Tambayar da ta yi ma kanta kenan a cikin zuciyarta wanda ba ta san maganar ciki ta fito fili ba.Ya gyara gilashin idanun sa ya miƙe tare da juwa mata baya.
" Yes abin da kika ji hakan nake nufi kin san ke ba sa'ar aurena ba ne,na tabbata kina tunanin me ya sa zan aure ki?Kamana É—an gayu kuma É—an masu da shi yayin da ke kina talaka kucaka dake.Ki kalle ni mai aji kama na ban yi kama da wanda zai aure ki ba."
Ya numfasa ya juyo ya na kallonta ganin yadda ta saki baki hanci ido ma'ana ta yi galala ta na jin tatsuniyar da yazo mata da shi.
" Matata Zainab wacce nake so fiye da komai rayuwata mace mai aji yarinya ƴar babban gida,Allah bai nufe ta da haihuwa ba ni kuma bazan iya haɗa ta da wata ƴa ɓace ba don na yi mata alƙawarin bazan yi mata kishiya ba,ga shi ina son na ga ƙwaina a duniya shi ya sa nake son na aure ki a sirri ki haifa min ɗa ɗaya na ba ta amma a gidana zaki zauna amatsayin ƴar aikin ta."
Wani irin hajijiya ta ji ya ibeta sai ga shi a gabansa ta zare ido jin a bin da ya faɗa,take ta ji wani hajijiya zai yarda ita ƙasa ta rintse idanunta,hawaye suka fara turereniya a kan fuskarta da ta shiga da tashin hankali.
" Allah na roƙe ka ka farkar da ni daga wannan mummunar mafarkin na farka ba tare da na gan shi kamar yadda yake tsaye a gabana! Ya Allah ka ɗauke ganina da shi na har abada da kunnuwana su ƙara ji min abin da yake faɗi ba,Ai gara na auri Alhaji Tanimu da na amince na auri mutumin da nake jin,bayan shi babu wani ɗa namiji a duniya shi ne yake son na yi rayuwa a gidan shi a matsayin ƴar aikin matarsa.
Wayyo Alla!gara na ga ranar mutuwata don zan fi samun maslaha a cikin ƙabarina da na amince da buƙatarsa.
Tofa ga dai Baba Sani ya amince shin Juwairiya za ta amince ya auren zai kaya?Ku dai ci gaba da bibiyar lintafin SAKACINA KO HALIN MAZA.
ÆŠUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ÆŠIN KU YA NA SAKA NI NISHAÆŠI.
MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha huɗu.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.