← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 86

Sashe 77

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannunsa ya saka ya É—aga rigarta ya É—ora hannunsa a lafaffen cikinta da bai nuna alamun tana da ciki ba.Tsaki ya yi don shi ya matsu ya ga cikin ya fito.

Juwairiya da take bacci ta ji kamar an taɓa ta kafin ta buɗe ido sai ta ji ƙamshin A.m da ta tsana.

Da sauri ta buɗe ido ta yi ido biyu da shi da yake tsaye yana taɓa cikinta.

Ture shi ta yi tare da miƙewa da gudu ta ruga bayi.Tsabar takaici ya sa A.m tsayuwa kamar an dasa shi har ta gana amai, ta fito ta tsaya can nesa da shi yayin da miyau ya taru a bakinta.

" Na lura iskanci da rashin mutunci yake saka ki kike mini wulaƙanci,kin mai da ƙamshin jikina sai kace warin kashi da na matso kusa dake ki fara amai,to ki sani wallahi ko kayan cikinki za ki mayar sai na din ga gaisawa da babyna,don na lura so kike kawai ya shaƙu dake ke kaɗai saboda in na raba ku,ya ne me ki,don ki sani ba zan zauna dake ba kamar yadda iyayena suka faɗa mini."

Tsaki ta yi ta tofar da miyau sannan ta yi mishi kallon banza ta ce." Na lura ba turaren da ka shafa ba ne na tsana,kaine na tsana kake mini warin da ya fi na kashi ɗoyi,don haka kai ya dama in ka rabu da ni,saboda in zan din ga jin irin wannan warin da nake ji a jikinka,to zan yi fatan Allah ya nisanta ni da kai har ƙarshen rayuwata."

Cikin mamaki ya tsaya yana kallonta a ran sa tunani yake to ko dama yaudarar sa take da take cewa tana son sa,jin irin kalaman da take mi shi,wai yaushe ta zama haka duba ga da ko kallon sa cikin ido ba ta yi,sai hawayen banza da take mi shi,lallai ya yi sake ta raina shi.

" Tun da mun tsani junanmu na ji daɗi sosai kin ga rabuwarmu za ta zo cikin sauƙi,amma wallahi ba ki isa ki hana ni jin ɗumin babyna ba."

Da sauri ya matso tare da ƙanƙame ta kamar zai mai da ta cikinsa.

Juwairiya ta saka kuka da ƙarfi ji take da ya rungume ta kamar ana soka mata allurai,yayin da wani amai ya ƙara ta so mata.

Momi da ta dawo sakamakom mantuwar da ta yi ta ji kukan Juwairiya da ƙarfi,duk da ta ga motar A.m a gidan,amma kukan da ta saka da ƙarfi ba na lafiya ba ne.

Turus! Ta yi tana kallon sa yayin da kunya ya kama dukannin su.

Shafa kan sa ya yi." Momi rashin mutunci take mini wai wari nake yi duk iya gayuna,shi ya sa na murÉ—e mata baki don ni ba na É—aukar raini."

A kunya ce ya faɗa ganin ta gan shi rungume da ita." Ba na son iskanci maza ka tattara ku tafi gidan ku,don ta ce kana wari shi ne za ka mata irin wannan matsar ina falo fa na ke jin ƙarar ta,kaman ta abin da yake cikinta."

" Na sani raina ni ta yi da yawa don kawai ta samu ciki,to ta sani ba zan ɗauki raini da ga gareta ba.Kuma Momi ta zauna a nan kawai har ta haihu "Ya ce da ita saboda sam baya son ta ƙara komawa gidansa,shi burinsa ya san yadda zai yi ya dawo da Zainab.

" Ka san Allah gobe zan tura masu aiki su gayara muku gidanku ku je can ku ƙarata in kun so ku kashe kan ku."Ta juya ta shige ɗakinta don ta ɗauko abin da ta manta.

A.m ya juya ya kalle ta tare da banka mata uwar harara." Kin san Allah ki gaya musu anan za ki zauna in kika bari aka tilasta mini yaga-yaga zan yi da naman jikinki,don kullum ina jikinki ina jin É—umin babyna ina ya so duk abin da zai faru dake ya faru.Bayan nan matar so za ta dawo in ba so kike ta yi miki dukan mutuwa ba."

Kwatankwacin hararar da ya ke masa ta mayar masa ko in ce fiye da haka ta ce." Allah ya ba ka sa a in ka so ka shige cikin jikina ka zauna ba ka raɓe ni ba,amma ina gaya maka wallahi in ka takurani zubar da cikin nan zan yi sai na ga ƙaryar raɓar jikina tun da na gaya maka ba na son ka na tsane ka tsana mai tsanani,sannan matarka ta dake ni ta daɗe kai za ta yi ma illah,kuma wallahi in har ka yadda na koma gidanka sai na hana ka ko shan ruwa a gidan kai da matarka?..."

Da sauri ya kawo mata shaƙa yayin da idanunsa suka yi jajir jin tace za ta zubar da ciki.

Juwiriya ta takura ta tsandara ƙarar saboda hankalinta ya tashi ƙwarai ganin yadda ya canza kammanni,ƙarar ya saka Umma ta yarda abin da ta ɗauka ta rugo ɗakin da gudu,har da ma aikatana gida.

ƘARAR YA SA NI MA NA RUGA A GUJE GANIN A.M ZAI SHAƘE TA BAI JI ABIN DA A.K YA FAƊA MI SHI BA.

TO MASU KARATU KU DAI BIYO NI KU JI YADDA ZA TA KAYA A TSAKANIN SU YAU BAN YI TYPIND DA YAWA BA,SABODA BA NA JIN DAƊI KU YI HAƘURI DA WANNAN ANA TARE.

KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI

SAKACINA KO HALIN MAZA

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY

TALLAH!TALLAH!!TALLAH!!!

INA ƳAN MATA DA MATAN AUREN DA SUKA SHAYAR SUKE SON MARTAR ƘIRJIN SU YA DAWO?

INA MATAN DA SUKE FAMA DA RASHIN ƘIBA KO INA A ƘAME?

MAZA GARZAYO KI SIYA INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO DA ƘIBA,MAGANIN AN RIGA AN GWADA KUMA YA NA DA AKYAU ƘWARAI.BARI IN GAYA MIKI YAR'UWA DUK WADDA TA CE MIKI MARTABAR ƘIRJINKI,ZAI DAWO MATUƘAR JIKINKI BAI MURJE BA,TO GASKIYA KUƊIN KI KAWAI ZA TA CI.

IN HAR KINA SON MAGANIN YA YI AIKI A JIKIN KI SAI KIN DAURE,KIN SHA SAFE DA YAMMA.SANNAN MUNA AIKAWA KO INA SIYAN NAGARI MAIDA KUÆŠI GIDA.

MAGANIN AKAN FARASHI MAI TSAUƘI IN KINA SO MAZA GARZAYO KI KIRA WANAN NUMBAR ( 07088268243) KO (08144072423)

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 34*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

" Abdurrahman!"

Ta kira sunansa cikin tsawa ganin ta'asar da yake son yi.
" A she har hanzu ba ka da hankali wai sai yaushe za ka daina kai hannunka jikin matanka da sunan duka?Ba ka ganin abin da ke cikinta wanda ka daÉ—e ba ka samu ba,so kake ka yi mana asara."

Da muryar tsawa take mi shi magana cikin zafi domin ranta ya ɓace sosai da ta shigo ta ga ya kai mata shaƙa.

" To wai tsaya kisa za ki da za ka shaƙe ta?"

Ta tambaye sa cikin ƙubula saboda ta fahimci ba shi da hankali.

" Momi cikina fa ta ce za ta ƙara zubar wa,ba ki san ta ba ne ba ta da mutunci za ta iya aikata abin da ta ce,shi ya sa zan fara gwada mata sakamakon abin da za ta gani."
Ya kalli Juwairiya da ta yi tsamo-tsamo cikin tashin hankali da tsoro,domin ba ta manta shaƙar da ya yi mata na asibiti.

" Yarinya kin san Allah kika yi wannan gigin tare za ku tafi lahira da shi."

Fakaitar idanun Momi ta yi ta kalle shi ta yatsina baki ta balla mi shi harara,tare da murguɗa baki ta kuma ƙara yatsina fuska.Cikin zafi ya ƙara nufar kanta.

Momi dafe kanta ta yi ta kalle su duka sai suka ƙara ba ta haushi,ta kalli agogon hannunta ta har lokacin da aka ba ta ya wuce.

" Maza kwashe kayanta yau za ta koma É—akinta wallahi ba za ku saka mini ciwon kai ba."Ta faÉ—a tare da fara janyo kayanta.

" Momi don Allah ki bar ni a nan ba na son na koma gidansa."Ta faɗa sai kuma ta kama kuka saboda tana tunanin yadda zaman su zai yi a gidan,sannan wa zai rinƙa tarairayarta kamar yadda su ke mata.

"Momi ba zan ƙara ba don Allah ki bar ta anan yanzu ta zama ƙazamiya ba ta komai zuwa za ta yi ta ɓata mini gida."Ya ce da ita saboda yana tsoron kar Zainab ta ji tana gidan,shi da yake son ta dawo in ta ji komai zai ɓace.

" Oho ko mai za ku ce yau za ku tattara ku bar mini gidana."
Taƙwala ma mai aikinta kira ta ce." Kwaso mata kayan abinta su tafi,sai kun bar gidan nan zan fita."

Da ya fahimci da gaske take yi sai ya ɗauki jakar da Momi ta tilasta mi shi ya ɗauka,yana hararar ta da take ta matsar ƙwalla.

A mota sun yi shiru babu wanda yake tari a cikin su,A.m ya so ya yi mata magana amma da ya ga ta shigo,sai ta zauna a gidan baya ta É—auki É—ankwalinta É—aure hancinta da shi,wato alamun har yanzu warin yake mata.

Kamar kurame babu wanda ya yi magana sai shi da yake ta jan tsaƙi.

Ko da suka shiga falon zaune ta yi a falo ba tare da ta kalle shi ba,ta janyo wayarta ta kunna data ta haye whatsapp da Hamdiya ta buÉ—e mata,don ita da chert kwata-kwata bai dame ta ba.

" A É—akin masu aiki za ki ci gaba da zama kamar da,don har yanzu matsayin ki na nan bai canza ba."Ya ce mata yana mata wani mugun kallo.
Chapter 77 · 0% Book details