← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 86

Sashe 36

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 18*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Tun daga wannan ranar Juwairiya ba ta ƙara saka shi a idonta ba wanda hakan ya tabbatar mata da tafiya ya yi tafiya, ita ma kan ta mai gidan ba zama take ba tun safe in ta fita sai dare za ta dawo,ta kwashi abincin da Juwairiya ta dafa,wanda tun daga ranar farko ta yi amanna da abincinta mai shigen daɗin tsiya,don ko A.m da ya ci ya yaba sosai ji ya yi abincinta ya yi kama da wanda yake ci a gidan iyayen sa.

Rashin zaman mutanen gidan haka ya ba Juwairiya damar sakewa a gidan kamar na ta ba ta da wani matsalar takura.

Juwairiya a ɗan zaman da suka yi da Zainab ta gane ko ita wace ce mace mai son hutu da gata,ga shi ta tsani zaman gida ko da ace mijinta na nan ga ta da shegen son ƙwalama kullum ta na yawon siyo kayan daɗi da ciye-ciye.

Juwairiya ta ɗauki tsawon wata ɗaya a gidan a cikin wata ɗaya ta ƙara kyau da kuma irin mai da cimar da take yi,ita kanta in ta kalli kanta a madubi sai ta ƙara juyawa ta kalli kanta cikin jin daɗin yadda ta sauya,wanda har take zolayar kanta da in ta je gida Mama ba za ta gane ta ba.

Juwairiya ba ta da son jiki ku san duk wani aikin gidan ta ɗauke shi shi ya sa kullum gidan ya ke cikin tsananin tsafta da ƙamshi, ita kan ta Zainab kullum yabawa take sai dai tsabar girman kanta ba ta taɓa nunawa ba.

Aiki ɗaya da yake ɓata ranta shi ne gyaran ɗakin A.m wanda kullum ta shiga sai ta yi kuka sosai,musamman da Zainab komai ba ta ɗaukewa sai ita take gyarawa cikin kuka da zafin kishi.

Ganin yadda Juwairiya take da hankali da natsuwa ga shi mijinta ya yaba kuma har ya yi tafiya bai ce komai ba,sai Zainab ta ɗan saki jiki da Juwairiya kaɗan duk da ta san rabuwa za su yi saboda ta isa aure,don haka ta yanke shawarar za ta ɗauko yarinya ta haɗa ta da Juwairiya ta din ga koya mata girki da yadda take gyaran gidan,saboda ko baƙi ta yi sai sun ya ba gidanta.

Ta na tsaye a kicin ta na tunanin abin da za ta dafa sai ta ji Zainab ta ƙwala mata kira,da sauri ta ruga kamar yadda ta buƙata duk lokacin da ta yi kiran ta.

Ba tare da ta kalle ta ba ta na riƙe da jaka ta ci uwar gayu ta ce " Fi ta zan yi yau zauji ya na hanya don haka ina son ki shirya abinci masu daɗi."Fita ta yi ba tare da ta ji mai ta ce ba.

Kwan biyu da dawowar shi da rana ta na shirya abinci a falon cikin sauri take son ta yi ta kammala kafin ya fito,wanda ta yanke shawarar haka ya dace ta din ga kauce mishi ƙila zuciyarta ta huta da raɗaɗin son da take mishi.

Ta na cikin shirya abinci kan dinning ta ji ƙarar kiran waya ya shigo sai ta shiga dube-dube a tunanin ta wayar Zainab ce ta manta fa ita,don sam ba ta kula da A.m da yake bacci ta bayan ta akan doguwar kujera.

Sai dai jin ƙarar wayar ya sa ta gane ba ta Zainab ba ce, wanda kuma haka ya ba ta damar fahimtar a kwai mutum a cikin falon.
Kiran wayar ya sa shi juyawa da nufin ya kashe wayar saboda a gajiye yake matuƙa! Kwanan nan sam bai samu ya huta ba,ya laluba wayar sa da nufin ya janyo wayar ya kashe bai jita in da yake tsammani ba,tunawa ya yi da jifa da ita da ya yi lokacin da ya shigo cikin falon.

Sai ya buɗe idanun sa a wahalce ya na waigen in da yake jin ƙarar ta amma tsabar gajiya ya saka shi kasa motsa jikin sa ya ɗauko wayar.

Ganin haka sai ta nufi in da wayar take ta na neman agaji ta ɗauko masa tare da miƙa masa,yayin da idanunta suke cikin na sa kuma ta kasa ɗauke ƙwayar idanunta ga barin kallon sa.
Idanu suka zuba ma junan su na tsawon lokaci wanda hakan ya sa Juwairiya ta rasa natsuwarta,shi ya fara É—auke idanun sa ya lumshe su.

A hankali Juwairiya ta tako ta miƙa masa wayar da ta ƙara rurin neman agaji.

Idanun shi ya ƙara maida wa kanta ya na mata kallo ƙasa-ƙasa ya na son ya gano halittarta,don shi zai iya rantsewa bai taɓa yi mata kallon cikakke ya san ya take ba,shi dai ya san ya yaba da ita har ya ji zai iya aurenta matsayin matar da zai iya aure na kwangila ta haifa mishi yaro.

Wayar da ta miƙo masa ya kai hannun sa zai ƙarɓa ya haɗa har da hannunta ya na ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa,da sauri Juwairiya ta janye hannun tare da fara tafiya a hankali da nufin tabar gurin don jin wani irin tsau da ta ji jikinta ya yi,yayin da take jin wani ƙarin saƙo daga zuciyarsa ya na aika mata cikin zuciyarta.

" Juwairaah."

Ya kira sunanta ba tare da ya miƙe ba cak tsayawa ta yi ba tare da ta jiyo ba,haka shi ma ya na kwance ya na kallonta kusan tsawon minti biyu,sai ta jiyo gabanta ne ya buga ras!
Da sauri ta ruga zuwa ɗakinta tare da faɗawa kan gado ta saki gwauron numfashi idanunta ta rufe cikin wata irin murya ta ce."Allah na roƙe ka kasa na zama jaruma na gama kwangilata na bar gidan nan kamar yadda na saka ma raina."
Ta nisa tare da ƙara juyawa ta kuma ce wa." Haka kawai ka shigo cikin rayuwata ka hana zuciyata sukuni."

Idanunta ta buɗe suka tsarƙe a na A.m da yake tsaye a gefenta ya na jin abin da take faɗi,ya kai hannu ya fi sau uku da nufin ya riƙe ta amma sai ya kai ma iska nushi don ya na ganin in ya taɓa wata ƴa mace bai yi wa Zainab halacci ba.

Ganin ta buÉ—e ido sai ya ja baya ya haÉ—e rai hakan sai ya É—an tsorata har sai da ta ja da baya ta na kallon shi don ba ta san ya shigo cikin É—akin ba.

" Ji nan Juwairaah! Ko kaÉ—an kar ki saka a ranki zan iya rayuwa dake kin ga matata kuma iya É—an zaman ki a cikin gidan nan,kin ga irin tsananin son da nake mata don bai kamata sai na gaya miki zaki fahimta ba,don na faranta mata na aure ki don haka ki kiyaye duk wani abin da zai sa ki yaudari kan ki,don kin san haka ba mai yuwu wa ba ne sanin kan ki ne ruwa ba tsaran kwando ba ne?"

A hankali ta É—aga mishi kai ganin ya tsare ta da ido ya na son ya ji amsar tambayar sa.
" Sannan kar ki É—auka ko na manta dalilin da ya saka na aure ki ne.".
Ya juyo ya na kallonta ya ce da ita." Wallahi na rasa yadda za' yi na fara ɗaukar ki a matsayin matata don ba mu dace ba,ni sai yanzu nake dana sanin da idona da ya rufe na yadda na aure ki,amma duk da hakan zan daure na aiwatar da shirina da zarar kin sami ciki na kai ki wani gurin ki haihu na karɓi yarona mu shafe babin rayuwarmu."

Ya na kai nan ya fice ba tare da ya lura da kukan da take yi ba na baƙin cikin tsanar ta da ya yi,sai dai kuma daga ba ya ta dai na jin haushin kalaman da ya faɗi saboda duk abin da ya faɗa gaskiya ne,ita ma ta karɓi auren sa ne saboda ta ta ceci ran mahaifiyarta da ɗan'uwanta.

Washegari da safe Juwairiya na kwance hayaniyar masu gidan ya tashe su wanda ta kasa gane ko menene,amma ta tabbata ba lafiya ba jin yadda suke magana sama-sama musamman muryar Zainab wacce har kukanta ta ji.
Matuƙar tsoro ya kamata ji ta yi ta ƙara mugun tsoron A.m don ba ta san haka yake da tsiya ba.

Ta na zaune a É—akinta ta yi tsumu so take ta haÉ—a abin karyawa amma ba zata iya fita ba jin yadda suke ta É—aga murya kamar za su dambace.

Mamaki ya kama ta sosai wai masoya ne suke irin wannan faɗar,ganin sun ƙi yin shiru da sauri ta shige kicin ba tare da sun gan ta ba,ta fara ɗora abinci jikinta na rawa gani take kamar a kanta faɗan zai ƙare.

Ta na shirya a binci a dinning ta ga A.m da ƙatuwar troley ɗin sa ya na ja, ransa kamar an aiko masa da mala'kan mutuwa, ba tare da ya kalle ta ba ya fice daga gidan.

Ba'a jima ba sai ga Zainab da na ta jakar ta na waya bayan ta gama wayar ta kalli Juwairiya ta ce " Ke wai me sunan ki baki gaya min ba?Ko ki na jiran na tambayeki ƙila uwar ki zan ci da sunan."

A hankali Juwairiya ta furta." Juwairiya sunana."Yayin da hawaye suka fara turereniya a fuskarta.

Tsaki ta saki." ko ma mene ne ni tafiya zan yi kuma ƙasar zan bari, ban ce kije ko ina ba kar a kwashi kayana akai gidan matsiyata,ki kula min da gidana duk abin da kike so ga waya ki kira ni in da matsala."

Jefa mata wayar ta yi a jikinta ta fice ba tare da ta yi tunanin za ta iya fashewa ba.

Tsananin mamaki ya kama Juwairiya yanzu ne ta gane musabbabin faɗar su.Da sauri ta leƙa ta windo don idanunta su fita da shakkun kayan da ta saka za ta ƙetare wata ƙasa a matsayin ta na matar aure.

Haka ta wuni sukuku daga kallo sai kwanciya tunna ba masu gidan da za ta yi musu girki.Da daddare sai ta kasa bacci saboda ita kaÉ—ai ne sai masu gadi,Baba in ta gama ayyukanta gida take tafiya saboda ba ta da nisa sosai da gidan.
Chapter 36 · 0% Book details