← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 86

Sashe 47

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya ishe ka a gaban wata banza daƙiƙiya kake gaya min wannna maganar?Ya zama dole Juwairiya ta bar gidan nan duk da ba na tunanin ko kallon ta za ka iya kuma na yadda da kai A.m,amma ai ta isa aure kawai zan ɗauko yarinya ƙarama in ya so ta koya mata aiki ta bar min gidana."

Am ya kalle ta ya ɗaga kafaɗunsa alamun bai dame shi ba ya ce." Ya rage na ki Zainab mijinki na ke matuƙar ba za ki zauna ki kula da ni ba,ni kuma ina da damar da zan hana duk wata mai aki shigowa gidan nan sai wanda na ya ba da abincin ta tun da ni ake girka ma wa,in kuma za ki canza ta fine amma kece za ki zama makwafinta ba ki ba fita gantali sai kin girka min abinci."

" Kalle ni da kyau ai wallahi ƙarya ka ke don ba ka nemi aure in da matar ka za ta dafa maka abinci ba."

Ta faɗa ta na juya jikinta tare da takun girma sannan ta ɗora da ce wa." Kuma kan ka ake ji ni ƙara fita zan yi saboda kaya ake so da yawa,amma kafin na tafi dole na kawo yariyar da Juwairiya za ta koya ma aiki."

Ta wuce zuwa da sauri bayan ta harari Juwairiya ta ce "Kuma da ga yau na hana yin girki tare da na ku ki yi mana na mu daban kuma daban."

" Allah ya sa bangon duniya za ki ba wata ƙasa ba mu zuba ni da ke shege ka fasa."

A.m ya faÉ—a mata lokacin da ta haye sama ya juyo ya kalli Juwairiya da ta bushe a tsaye ta na kallon dirama,girar sa ya É—aga mata tare da kashe mata ido É—aya ya ganin ta firgice ya manna mata kiss a kumatu.
"Abinci ya yi daɗi ƙwarai "

"A kwai tukwici an jima."

Zare idanunta ta yi ta zuba mishi ido lokacin da ya haye sama ya na sakin mata murmushi mai tsada wanda ya saukar mata da kasala har sai da ta zauna.

A hankali Juwairiya ta ja jikinta ta shige cikin É—aki ta na mamakin A.m da kullum saka ta yake a cikin shakku.

Ranar wata safiyar talata Juwairiya ta shirya za ta gurin Mama.Ko da ta isa gidan Mama ba ta nan sai da ta jira ta sannan ta dawo daga moƙota da ta shiga.

Cikin mamaki Mama ta tsaya ta na kallonta tare da riƙe bakinta don ta rabu da zuwa gidan kwana biyu.

"Juwairiya kin gan ki kuwa haka kika dawo sai kace amaryar da take ganiyar cin amarci!Gaskiya kin yi kyau sosai."

Gaban Juwairiya ya yanke ya faÉ—i gani take kamar Mama na zargin wani abu,irin yadda take kollonta cikin mamaki.

" Kai Mama hutu ne fa kawai saboda kuÉ—i suke da shi sosai."

Mama ta matsa kusa da ita ta zauna tare da riƙe hannunta ta na shafawa.
"Gaskiya kin yi kyau matuƙa ki na sane da saura wata biyu da kwanaki ki gama aikin ki ko?"

Ta tambaye ta da ƙosawa sannan ta ɗora da ce wa." Na matsu ƙwarai na ga kin yi aure ji nake kamar rai na ya na jiran wannan ranar ne kawai."

Mama ta faɗa ta na ƙarewa Juwairiya kallo tare da tunani barkatai a zuciyarta.

" Mama aure lokaci ne ai zan yi in lokacina ya yi kuma ni yanzu aure tsoro yake bani,ji fa Mariya har sun rabu da mijinta.Na matuƙar tsorata Mama ina tsoron kar na yi aure na dawo ina zawarci."

Ta faÉ—a yayin da idanunta suka yi rau-rau tuna maganar da A.m yake gaya mata a kullum.

" Ko wa da ƙaddarar sa Juwairiya kuma mutum ba zai iya tsallake ta ba,wataƙila zaman su ya ƙare da mijinta a kwai rabon wani a gaba shi ua sa suka rabu,amma kar ki saka wannan a ranki ki saka a ranki za ki yi aure da zuciya ɗaya."

Ta faɗa ta na kallonta sannan ta miƙe tare da juya ma Juwairiya baya ta ɗauko kuɗi ta ce."Kin ga wannan kuɗin nan,ina adana su ne in kika gama aikin nan kamar yadda aka iba sheƙara ɗaya,in dai Sani bai amince ki yi aure ba to za a haifi ɗa mara ido tsakanina da shi."

"Mama hakan ma ba zai faru ba in sha Allahu aure zan yi kar ki ta da hankali Mama."

Juwairiya ta faɗa jin abin da Mama ta ce ma ta sai hankalinta ya tashi matuƙa, ta shiga zubar hawayen da ta kasa gane dalilin yin sa saboda tarin damuwar da yake ranta.
A ranar Juwairiya ta je da nufin ta ba Mama irin tarin kuÉ—in da A.m yake ba ta saboda hannun sa a sake yake,amma jin irin maganganun da take yi mata mai kama da wanka da ruwan jurwaye, sai hankalinta ya tashi ta koma ba tare da ta iya ba ta kuÉ—in ba,saboda ta na tsoron kar Mama ta tuhume ta.

Koda ta fito za ta tafi Mama ta É—auki tsawon lokaci ta na mata nasihar da ta kula da mutuncin kanta,a haka suka rabu jikinta kamar an yi mata dukan tsiya.

Zaune suke a falo Zainab ta na gefen A.m da hankalin sa,ya ɗauku akan labarai da ake yi tashar aljazira.Zainab ta na riƙe da filet da ta yanka apple ƙananata na ci.
Zainab ta kalli A.m da ya É—an juyo ya na kallon ta ta ce." Ka san me wannan shashashan yaron ya ce?"
Ya É—auke kan sa ga barin kallon ta tare da É—aukar remote da ke gefen kujerar da ta ke,ya canza tasha ganin an gama labarai ya ce.
" Wa kenan."

"Amir ma na."

Ta na nufin cousing É—inta sai ta ci gaba da ce wa." Kirana ya yi wai don Allah ya na son Juwairiya."

A.m da maganar ta dake shi ya kalle ta zabure ya na faÉ—in." Amir É—in ne ya ce ya na son ta kai amma ya fara shaye-shaye."

Zainab ta kalle shi ganin yadda ya razana a tunaninta,ta ɗauka ta ɗauka ya na mamakin kamar shi ya na ɗan manya zai ce ya na son ta,don haka ta gyara zama ta na ƙara shige masa ta ce."Kai ma ka razana ni kaina hankalina ya tashi sai da na yi mishi tatas! Saboda ba shi da hankali mai zai ci da Juwairiya ƴar matsiyata!"

Miƙewa ya yi ya na faɗin." Amma zan koya mishi hankali matuƙa sai ya yi nadamar faɗin sonta da ya ke yi ke ba ma ita ba ko wani ne ba zai ƙara faɗin ya na son ta ba."

" Ai gara ka yi mishi magana mahaukacin ƙila ya taɓu ne,amma na ƙalubance ka da ka ce ko wani ne ya ce ya na sonta zai sani,kamar maigadi da direba Bala in suka ce su na sonta ai faɗuwa ta zo da zama."
"Ko ma dai waye ya faÉ—a ki tsawatar masa don ko da hauka kar su yi gigin faÉ—a mata."

Ya ce ya na ƙoƙarin barin gurin amma sai ta ƙira sunan shi ya tsaya ya na kallonta.
" Juwairiya fa dole ta bar gidan nan don aure za ta yi duk jin daɗin girkin ta da kake yi haka za ka haƙura ka bar shi,kuma na yi magana da Anty Fati za a kawo min yarinya ƙarama kafin Juwairiya ta tafi ta saba da gidan kuma ta koya mata girki."

Dubara ce ta faÉ—o masa sai ya dawo ya zauna ya na fuskantar ta ya ce."Haka ne na san dole ta yi aure,amma kafin nan mai zai hana mu saka Juwairiya a makaranta ko da part time ta din ga zuwa,kin ga sai ta karanta abin da ya shafi girki da yadda za ta koya ma yarinyar da za ki É—auko ko ba komai mun taimaki rayuwar ta,ke kan ki ba kya son zama da jahila marasa ilimi."

Zainab ta É—an yi nisa ta na tunani domin ita sam ba ta ga amfanin saka ta a makaranta ba,saboda iya girkin da ta iya ya isa ba sai ta koyo ba.

" Meye alfanun haka a gare mu Juwairiya gwana ce gurin girki ba sai mun kai ta makaranta ba."Ta ce ta na kallon sa." Ok tun da haka kika ce fine ni tunani kawai na yi ya kamata mu taimake ta,amma na fahimci ranki ba so ba a bar maganar."

Ya faɗa ya na ƙoƙarin hayewa sama shi ya yi tunanin hakan ne don kawai ya ragewa Juwairiya,zafin raɗaɗin rabuwa da shi fahimtar da ya yi ta na son karatu sannan ya shirya zuwa ƙasar waje yi mata dashen ƙwai na haihuwa don shi ya sadaƙar shi ne ba ya haihuwa duna ga rashin samun cikin da ba ta yi ba.

A ran sa ya saka bai wuce su ƙara wata tara a tare ba saboda ya huta da ɗan iskan nan Baba Sani ya tabbata zai ƙara neman sa.

Kwana biyu da maganar mai aiki sai ga shi an kawo wata yarinya wace ba ta wuce shekara sha uku ba,sannan ta na da hankali matuƙa ga natsuwa ba ta da hayaniya.

A ranar da aka kawo Binta mai aiki yarinyar ta shiga cikin ran Juwairiya matuƙar gaske,don komai Juwairiya ta ɗauka za ta karɓa ta ce ita za ta yi,sai yarinyar ta shiga ranta matuƙa musamman da ta gaya mata labarin mahaifiyarta ta rasu,kishiyar Babar ta take gallaza mata har ta kawo ta aikatau.

Da fari Zainab ta ƙi amincewa na su saka Juwairiya a makaranta,amma daga bisani ita da kanta ta nuna masa amincewarta don tun ranar da ya yi mata magana bai ƙara ta da maganar ba.

Cikin ɗoki ya gaya ma Juwairiya da ta kawo takaddunta na shedar kammala sakandiri zai saka ta a makaranta,hakan ya yi mata daɗi ƙwarai sai dai da ta sanar ma Mama sai taƙi rashin amincewa,ita a ganin ta a wanan shekarun aure ya da ce ta yi, amma da ta ga Juwairiya ta nace kuma ta san alfanun karatun sai ta amince,da sharaɗin in har ta samu miji za ta yi aure kuma koda ya ce bai amince da karatun ba.
Chapter 47 · 0% Book details