Sashe 20
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kawai sai gani ta yi ya saka kuka ya na kallon Juwairiya da ita ma take kuka na tausayin halin da suke ciki." Juwairiya zuciyata za ta shiga cikin wani hali na rashin ki.Ki yi min addu'a Allah ya ba ni mace me irin halin ki,ni na san ke wace ce ko idanunki mutum ya kalla ya san kina da tarbiya da natsuwa.Ina sonki zan haƙura da auren ki saboda umurnin Mama."
Fita ya yi har da gudun sa ya na sharen hawaye Juwairiya ta miƙe da gudu ta shige ɗaki tare da saka kuka.Sam ita ba ta ga dalilin da Mama za ta hana shi ba,ba ta san me Baba Sani yake nufi da ita ba shi ya sa take girmama shi,abin da ya sa taƙi ga ya mata ta san duk ranar fa ta gaya mata ƙudirin sa akan ta, ƙila zuciyarta za ta buga domin abin ya yi muni.
Tun daga wannan ranar ba ta ƙara gani Mas'ud ba ko wayar da ya siya mata Mama ƙwacewa ta yi ta ije,don a yadda ta ga take-taken ta za ta iya kiran shi kuma shi ma haka.Tun ta na saka ran ze dawo har ta cire sai dai ta wahala kafin ta cire son shi a ran ta,sannan da ga baya taci gaba da al'amuranta.
Mariya ta sami miji za ta yi aure anan kusa da layin su za ta yi auren don haka su Juwairiya su ne ƴan mata.Su Juwairiya an sha gayu da lalli an yi kyau sosa,ana ta hidimar biki don ba zama an saci ɗan ɓarawo.
Zaune suke ana hirar Æ´an mata Juwairiya ta kalli Mariya yadda ta sha kyau yace."Su amarsu kin ganki kuwa,dama komai munin amarya ranar bikinta sai ta haska."
Fari ta yi musu ta na dariya tace." Ku zauna kuna rungume filo ni dai Allah ya hutashshe ni na shige daga ciki,ku tsaya kuna ruwan ida kwayi kwantai."
Wani irin dundu Juwairiya ta duma mata ta nafaɗin." Ji min ƴar baƙin fata wato fatan da kike mana kenan tunna kin shige daga ciki ko? To in sha Allah muna bayan ki."Sauran ƴan matan suka taso mata ita dai Mariya dariya take musu,sannan tace." Ai ke Juwairiya Baba Sani ya hana ki aure da tuni kin haihu ma.Amma ba komai Allah ya na tare dake lokacin ki ne kawai ba yi ba."
Shiru ta yi sai hawaye yayin da mutanen É—akin suke ta ba ta baki.
A haka suka sha bikin Mariya aka kaita É—akin ganin Juwairiya za ta tafi ta kama ta tare da saka kuka.Sai kuma ta ba Juwairiya tausayi ta rungumeta ta na share mata hawaye.
Mariya ta share hawaye tace." Maganar da mukai dake akan aikin nan kije Allah za kiji daÉ—i kin ga ni na yi aiki da su."Juwairiya tace." Ke ni raba ni da aikin nan don na yisu amma ban ji da daÉ—i ba."
" Allah ki gwada wannan kin ga yanayin halin da kuke ciki,ga shan maganin Mama dole kina buƙatar kuɗi."
" To zan shawarci Mama duk abin da tace sai na je."Da wannan Juwairiya ta tafi gida cike da kewar ƙawarta wacce ta temaka mata.
Koda ta yi ma Mama magana shiru ta yi zuwa can tace." An ya zan barki kiyi aikin nan nifa tsoro nake yi kina ganin rashin mutuncin da Hajiya Binta ta yi miki,amma tuna kin ce Mariya tace ta na da mutunci sai ki je Allah ya tsare ki."
Numfashi ta saki tace." To bari na gwada mu gani."
Juwairiya ta fara aikin cikin jin daÉ—i ga karatu da take samu ake yi wa yaran lesson da islamiya matar ma ba ruwanta.
Watan ta biyu a gidan ranar ta kammal aikin ta za ta tafi matar tace." Don Allah Juwairiya ki tsaya zamu je gidan biki ni da yarana,zuwa yamma zamu dawo sai ki tafi in kuma na yi dare zan kaiki a mota."
Duk a ranta ba ta so ba amma sai ta amsa da." To." Ta koma ta zauna yayin da ita kuma ta shirya da yaranta suka fita.
Tun da suka tafi har aka kira sallah ba ta dawo ba,ranta ya fara ɓaci don ba ta son ta yi dare kar Baba Sani ya dawo ya kuma ƙara mata wani sharrin.
Jin ƙarar mota sai ta yi maza ta leƙa ta windo ta na tunanin ita ce,sai dai cikin takaici ta koma ta zauna ganin mijinta ne ya dawo.
Ya shigo da sallama ya amsa ya na kallonta." Juwairiya har yanzu ba ki tafi ba?"Ya tambayeta ya na kallonta." Eh tunna ka dawo bari na tafi "
" No ki kira ta nima ƙara fita zan yi."
Don takaici ko amsa mishi ba ta yi ba to me ya dawo da shi koma wa ta yi ta zauna.
Ya shiga cikin ɗakin sa mintina biyar ya fito sai kawai Juwairiya taga ya yi kanta gadan-gadan! Da sauri ta miƙe tare da saka salati dai-dai lokacin da ya fisgota ya haɗa ta da jikin sa da ƙarfi.
Kasancewar shi namiji me jiki da ƙarfi ya yi nasarar kayar da ita ƙasa tare da yi mata rumfa,yayin da dabbe ya kaure ko kaɗan ba ta yi tsammanin ya na da wannan halin ba.Kuka ta saka ta na rokon shi,amma bai kula ta ba yaci gaba da ƙoƙarin ida nufin shi.
" Inna lillahi Faruk!Me zan gani dama amanata kuke ci?"Ta furta cikin ƙaraji! yayin da ta yo kan juwairiya ta hau ta da bugu.
Juwairiya ta yi kuka ta yi ihu ji take kamar numfashinta zai fita domin kanta ta hau ga ta da ƙiba,da ƙyar ya samu ya ɓamɓare Juwairiya ta samu ta gudu.
Da ƙyar ta samu ta isa gida ta na kuka a ranar ta rantse ba za ta ƙara yin aiki ba,ko da mutuwa za su yi yadda ta shigo Mama ta tsorata.
Bayan ta yi mata bayani tana kuka Mama sai da ta zubar mata da hawaye ganin halin da take ciki.A ƙalla sai da ta yi sati ta na jinyar jikinta don har sai da ta kwanta ciwo.
Haka rayuwa take tafiya musu yau baƙi gobe tsummma ga ciwon Mama ya yi tsanani.Wani abin ƙarin tashin hankali Ibrahim da dama can ba lafiyayye bane,saboda sikila ne shi jikin sa da ya yi sauki amma a cikin kwana biyun nan jikin ya tashi.
Ciwon shi sai yake son ya danne na Mama amma duk wanda ya ganta ya san ta na cikin tsananin ciwo.Ga kuma Baba Sani da ya sanar da Juwairiya ya yi mata miji wato Alhaji Tanimu.
A ranar da Baba Sani ya gaya mata sumewa ƙau ta yi don ya tabbata Baba Sani ba ya ƙaunarta,don ita da ya aura mata shi gara ta zauna ba aure ko ace mutuwa ta yi.
Waye a faɗin garin be san Alhaji Tanimu ba wanda ya mai da mace tamkar rigar sawan shi.Mutum ne mara addini ga shi kamar wani hor.Kusan duk shekara yake sakin mace ya ƙara aure bayan ya tabbatar sun sami ciki,don baya son haihuwa a tunanin ta shi kan shi be san iya yawan yaran shi ba,duk da wasu ya na ba ma iyayensu mata kyauta wasu kuma ya kai su almajiranci.
Sannan an sha kama shi ƴara ƙanana ya na musu ya lalata musu rayuwa irin mutumin da Baba Sani yake son ya zama mijinta kenan.Ai Juwairiya ƙaramin hauka ta yi don gara yace ta shiga duniya.
Shiko Alhaji Tanimu se ɗinkirama Baba Sani kuɗi yake yi hankalinsa kwance ganin zai mallaki wannnan zuƙeƙiyar,shi ya sa be damu ba ko sanda ya zo zance taƙi fitowa tallar ta fa aka kawo mishi har gida.
Rayuwa a wannan karan tafi yi wa su Juwairiya illah ga aba abinci sannan dukkanin su ba lafiya,ga Baba Sani da yake ta shirye-shiryen bikin ta don har an kawo kayan sa rana watan gobe biki.
Mama ta shiga tashin hankalin ciwonta ya ninku ga yunwa har takai sai su wuni ba su saka komai a bakin su ba.
Juwairiya ta tsara ma kanta ta gudu amma in ta ga halin da su Mama suke ciki sai ta ji kamar ta kashe kanta ta huta,ita kanta ba lafiya take da shi ba don ta na ganin har tafi su Mama jigatuwa saboda zuciyarta da take ji kamar za ta fashe.
Ganin yunwa zai kashe su sannan duk kuɗin da Baba Sani yake karɓa bai ta ba ba su koda na sabulu ba,ta je gurin Mariya ta ara mata naira dubu biyu ta fara jarin gyada.Da wannan suke samun abinci.
*******
Zaune yake cikin damuwa sai kuma ya miƙe don a yau jin sa yake duk shawarar da amininsa ya ba shi zai iya ɗauka saboda halin da yake ciki.Makullin motar shi ya ɗauka ya nufi gidan A.k.
Sai dai cikin rashin sa'a ba ya nan don haka bayan sun gaisa ya fice daga gidan ya samu wani guri mara hayaniya ya tsaya,tare da ciro waya ya kira A.k.
Ba'a fi minti goma ba sai ga A.k akan mashin ya sauka ya buÉ—e gaban motar ya shiga ya na share zufa."Am sorry aboki motar da ka siya min na kai ta service ba'a gama ba kan dole na baro motar na hawo mashin.Are you under the weather?"Ya tambayi aminnin nasa ganin yanayin sa.
Yace ya na kallonsa bai tanka ba illa ajiyar zuciya da ya yi ya kauda kansa gefe guda,ganin yadda aminin na sa yake ya san yauma ba lafiya to ko dame yazo oho don ya san dai zancen.
Suka É—an yi shiru ba tare sun ce uffan ba na tsawon lokaci sannan A.k ya katse shirun da cewa." Lafiya na gan ka wani iri in ce ba mutuniyar bace ta haÉ—a maka zafi."