Sashe 52
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Duk da wahalar da shi da Zainab take mata har ƙasashe take fita kasuwancinta amma kullum ya na gaya min ita ce matar so ni matar wucin gadi ne,amma abin takaicina sai ya zo ya din ga more ni ya na gaya min irin baiwar da Allah ya yi min bai taɓa kuskuren faɗin ya na sona ba."
Hauwa Tukur ta yi matuƙar tsorata da ganin su kamar wasu larabawa yanzu ta gane dole jikinta ya canza saboda irin daular da take ciki.
Hannunta ta ƙara riƙewa ta ce."A.m ya haɗu irin mazan nan ne masu wayo da dubara sam ba za ki taɓa gane in da ya dosa ba,amma na yi mamakin in da kika samo wannan gayen saboda maƙura ne gurin kyau."
Murmush mai kama da kuka ta saki."Don Allah ki ba ni shawara yadda zan jawo hankalin sa."
Numfashi mai ƙarfi ta."Ikon Allah ita Zainab wata irin banzar mace ce ina tausaya mata ranar nadamarta saboda na ga sakacinta sosai mace sai kace mahaukaciya abubuwan da take yi sam babu tsari aciki kuma ni na fi ganin laifin A.m da ya barta take mishi wannan iskanci.Gaskiya ba na goyon bayanki da kike kare kanki daga ɗaukar ciki, wanda ko ba a faɗa ba na san irin kuskuren da matar sa ta yi kenan kuma na tabbata ta na nadama.Ga kuma in da son duniya ya kaita haba ai ya raina mata wayo ya kawo matar sa cikin gidan ta ya na more abar sa ya maida ita shashasha.
Duk da ita ta na tunanin ba zai taɓa duba gareki ba saboda ba ku dace da juna ba tunaninta bazai kawo mata zai iya ɗaga ido ya kalle ki ba duba ga matsayin sa,ba ta san namiji ba haka yake ba abin da kake ganin yafi ƙarfin sa sai kiga ya mutu akan abin."
Sai ta kwashe da dariya ta duk da ganin halin da take amma rainin wayon ya yi yawa gani take kamar ya na raina musu wayo ne daga ita har Zainab É—in.
" Matsalar ka bayyana damuwarka ga mutumin da ka yadda da shi kenan na yi tunanin za ki ba ni shawara,amma ba ki duba halin da nake ciki ba kin tsaya ki na min dariya."
Ta faÉ—a a zuciye tare da É—aukar wayarta za ta tafi.
Da sauri ta É—auki jakarta ita ma ta kama hannunta."Afuwa lamarin ne a kwai rikitarwa ni dai ina baki shawarar ki kasance a shirye, saboda duk ranar da Zainab ta san abin da ke tsakanin ku Allah kaÉ—ai zai raba ku lafiya yanzu ki É—aga waya ki kira A.m ki sanar mishi da kina son shi mijinki ne fa,wanda yake dawowa ba yan ki ya kwanta mai zai hana ki sanar da shi."
Ta ce mata ta na kallonta a ranta jinjina lamarin take yi."Ba zan iya gaya masa ba kuma ba zai bani damar haka ba haba ya kamata ya ce ya gane irin son da nake masa ko ƙwayar idanuna ya kalla ya kamata ya gane."
"Ai ko dole ki sanar masa meye amfanin dakon son mutumin da bai sani ba kuma ko banza,daga ranar da kika gaya masa irin son da kike masa wallahi ko baya sonki ya kalle ki a matsayin kina son sa zai din ga kallon ki kuma ko banza masoyinka yafi maƙiyinƙa sannan a tunanina a haka wani abu mai girma zai shiga tsakani ba tare da ya sani ba."
Juwairiya jikinta ya yi sanyi matuƙar gaske zuciyarta ta halasto mata irin tarin son da take dakon sa ta ji ya na tasowa nan take ta faɗa kogin zuma har ta ji za ta iya kiran sa ya zo ta sanar mata da damuwar zuciyarta duk da kafin su yi aure sai da suka yi sharaɗin babu wannan wayarta ta zaro domin ta kira shi.
WANI IRIN FIRGITA NA YI SABODA BUGUN ZUCIYAR JUWAIRIYA DA NAKE JI YA SA CIKINA YA MURÆŠA NA TASHI DA NUFIN NA JE BAYI,AMMA KODA NA DAWO TSABAR TASHIN HANKALI BAI SA NA GANE MAI KE FARUWA BA SABODA SAUKAR BUGUN ZUCIYARTA JI NAKE KAMAR ANA BUGAMIN GUDUMA.
TOFA KO YA ZA TA KAYA A M ZAI AMINCE DA SOYAYYARTA?
KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.
BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU
JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 24*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
A tare zuciyarta take bugawa da ringing É—in da wayar take yi.Ta kira sau biyu bai É—auka ba sai jikinta ya yi sanyi ta ije wayar,ta kalli Hauwa da ta kafe ta da ido.
" Na kira shi amma bai É—auki ba ina tunanin wayar ba ta kusa da shi."Ta faÉ—a cikin karayar zuci.
Zama sukai suna jiran kiran wayar ko wannen su zuciyarsa na buguwa tamkar za ta fito.
Sun jima a gurin suna jiran kiran sa har suka gaji.Ita ta fara miƙewa ta kalle ta ta ce." Mai zai hana ki fara nuna masa so misali ki din ga nuna mishi kin yi kewar shi ,da kalamai masu zafi kuma ki din ga tura masa,ai shi ba yaro ba ne dole ya fahimta wataƙila ya san za ki kamu da son sa shi ya sa ya ce kar maganar so ya shiga tsakanin ku."
"Ki na ganin haka shine mafita na riga na ɗaukar wa kaina in har bai ce ya na sona ba ba zan taɓa yadda na bar ciki ya fito a jikina ba."Ta gaya mata cikin sassanyar murya.
" Allah kawai ya san me ya ɓoye a gaba amma ki dage da addu'a kuma ki din ga nuna masa irin yadda kike son sa a aikace ke fa matar sa ce,kuma tun da ya har ya iya haɗa jiki da ke ban ga abin da zai hana ya soki ba,amma ni fa nafi son ki bari ki sami ciki naga irin haukar da zan yi.
Maganar ya gundireta fara tafiya ta yi ba tare da ta ce mata komai ba, a ranta sam ba za ta amince da shawarar ta ba, ta yi alƙawari ba za ta dai na zubar da ciki matuƙar ba zai zauna da ita na har abada ba.
Kamar yadda suka shirya sai ta fara ɗan sakin layi ta na yi masa wasu irin abubuwa saɓanin hankalinsa saboda har mamakin ta yake wai dama haka take!
Duk wani abin da take mishi ya biye mata har ma ya na mata fiye da haka.
Ranar da suka shirya za ta gaya mishi amma a waya don ba za ta iya taran idanun shi ta furta mishi ba.
Da fari text ta ce za ta rubuta mishi sai Hauwa ta ba ta shawarar ta kira shi.
Cikin sa'a ringin É—aya ya É—auka ta na sanar mishi da ta na son ta yi magana da shi kuma maganar is verry important sannan kuma comfidential.
"Ok ba ki da damuwa tun da kina cikin makaranta ki bani É—an lokaci,ina gidan A.k na je gaida matarsa ni da Zainab bari na shigo cikin makarantar,ba sai kin gaya min a waya ba."
Duk yadda ta so ta hana shi zuwa don tafi son su yi a waya amma ya kafe ga shi nan zuwa,daga bisani kashe wayar ya yi ganin za ta yi masa gaddama.
"Ya ce ga shi nan zuwa yaƙi yadda na gaya masa a waya."
Ta faɗa yayin da zuciyarta take bugawa."Gaskiya ya na girmama lamarinki bari na ɓoye yau ina son na ga A.m, a zahirin gaskiya da ya sace zuciyar rabin raina ya hana ma ƙawata sukuni."
Dariya ta yi ta kauda kanta ba ta ce komai ba saboda ƙirjinta yake bugawa.
A lokacin da motarsa ta shigo sai Hauwa ta miƙe da sauri ta laɓe,ta yadda za ta din ga kallon duk abin da ke faruwa ba tare da ya ganta ba.
Har kusan in da take ya ƙaraso da motar sa sannan ya yi parking ya fito ya taho in da take.
Kallonta ya yi lokacin da ya zauna akan É—aya daga cikin kujerun, da suke a gurin tare da sakin wani wawan ajiyar zuciya.
"Kin tsorata ni fa wallahi na É—auka ko babu lafiya,amma tun da na gan ki lafiya lau faÉ—a min matsalar ki."
Ya faɗa ya na kallonta tare da riƙe mata hannu suna kallon juna ido cikin ido.
Sun ɗauki tsawon lokaci suna kallon junan su ba tare da sun ƙifta ba.
Da sauri A.m ya miƙe tare da juya mata baya domin ko ba ta faɗi abin da take son faɗi ba,idanunta sun bayyana tsaƙon su dama ba tun yau ba yake ganin ta na sakin layi,wanda yake biye mata don ya faranta mata.
In ko ta na son ta faɗa masa son shi take, kamar yadda ya gani a ƙwayar idanunta, ya kamata ya yi maza ya dakatar da ita, don ba zai taɓa son wata mace ba bayan Zainab ɗin sa.
Juyo wa ya yi ya kalleta ta da take ta in da inda ta in da za ta fara."Juwairaah kar ki ce ki na sona don ni ba na sonki."
A zabure ta tsaya gaban sa ta fara hawaye kamar an buÉ—e famfo.