Sashe 9
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Dakin sa ya nufa cikin sauri ya ajiye briefcase ɗin ya cire kayan sa ya saka jallabiya ya nufi toilet yayi alwala.yana fitowa yayi sauri ya sakko daga sama ya fice daga parlon ya nufi get ya buɗe ya fita daga gidan . masallacin a kusa da gidan yake,yana shiga ya tarar har an idar da sallar magrib.nan da nan ya yi kabbara ya tada sallah.bayan ya idar da sallar ne ya zauna yana jan carbi har aka kirawo sallar isha'i.
Bayan sun idar da sallar sai da ya tsaya yayi addu'a sannan ya fito daga masallacin ya kamo hanyar gida.ya na shigowa ya iske ta zaune a parking.yanda ya fita ya barta haka ya dawo ya tadda ita ko wanka batayi ba.tana zaune ta mi'ke ƙafa tana sana'ar tata ta chatting.
Ya samu waje ya zauna a gefen ta,ya d'ago ya kalle ta yace"ina fatan dai kinyi sallah dai ko??" ya faɗa yana ƙara duban ta,dan yasan zeyi wuya idan tayi sallar .ta dubeshi ranta a b'ace "tace wai kai mai yasa ka fiya takura ne?? Kullum baka da wata magana sai wannan,naga dai sallar nan idan na gama abin da nake yi ina harhad'awa in yita,idan har kaga banyi ba to gaskiya gajiya nayi.sabo da haka ni bana son takura,ka ƙyaleni mana idan na gama abin da nake yi zanyi".
Tsananin mamaki ne akan fuskar sa,ko da yake idan da sabo ai yaci ace ya saba.ya rasa yanda zai yi da rufaida, sabo da kullum abin nata ƙara ci-gaba yake yi,kuma yana yin iya bakin ƙoƙarin sa domin ganin ta gyara halayyar ta,amma ina kullum ita abin nata ƙara gaba yake yi.
Ita baga kula da miji ba,baga tsafta ba,babu gyaran gida balle na jikin ta,gashi bata kula da yaran ta,bugu da ƙari girki ma kwata kwata bata iya ba.bama wannan ba shi abin da yafi damun sa rashin ibadar ta, tun da sai ta ga dama take yin Sallah,idan bata ga dama ba bayi take ba.
Ya sauke b'oyayyiyar ajiyar zuciya tare da ƙara duban ta yace"dole ne na takura miki indai akan ibada ne domin ganin kin rabauta.kuma bazan dena ba har sai kin gyara halayyar ki.duk in da naga kin kauce hanya dole ne inyi ƙoƙarin dai dai taki akan hanya,ko kina so ko ba kya so, sabo da haka tun kafin In yi mummunan saɓa miki wallahi maza ki ajiye duk abin da kike yi kije kiyi sallah"
Ya ƙarasa maganar ransa a b'ace, yasan muddin ba haka yayi mata ba da wuya ta tashi ta yi sallar nan.sanin halin sa da tayi baya ɗaukan raini yasa ta tashi fuuuuuuu ta wuce zuwa sama,ya bita da kallo yana girgiza kai.
Jin da yayi cikin sa na ƙugi ne yasa ya tashi ya nufi dining table,yaja kujera ya zauna tare da buɗe warmers ɗin da suke ajiye a wajen.ta farko ya fara buɗewa ya ga shinkafa ce fara tas a ciki,ta biyu kuma stew ne a cikin ta, ɗayar kuma fried chicken ne a cikin ta
Ba tare da b'ata lokaci ba ya ɗauki plate yayi saving ɗin kansa ya yi bismillah ya fara cin abincin.cin abincin kawai yake yi badan yana jin daɗin sa ba, Sabo da kwata kwata babu wani tes da abincin yake da shi.
Bayan ya gama ne ya tashi ya kama hannun yaran sa ya kashe kayan kallon suka haura sama,ya kai su d'akin su yayi musu wanka ya saka musu kayan baccin su,yayi musu addu'a ya kwantar da su.kashe musu ƙwan d'akin yayi tare da jawo musu ƙofar.
Kai tsaye d'akin sa ya nufa ya faɗa toilet ya sakarwa kan sa shower.brush yayi sannan ya fito d'aure da towel a ƙugun sa,hannu sa riƙe da ƙaramin towel yana goge lallausar sumar kansa.tsayawa ya yi a gaban mirror ya shafa had'ad'd'en lotion ɗin sa mai mutuƙar ƙamshi.
Closet ɗin sa ya buɗe, ya ɗauki wasu haɗad'd'un pajmas white colour ya saka.ya ɗauki laptop ɗinsa ya zauna a katafaren gadon sa, ya jin gina bayan sa da fillow, ya kuma ɗakko wani fillow ɗin ya mi'ke ƙafarsa ya ɗora akai , sannan ya ɗora laptop ɗinsa ya fara aiki.
wannan kenan...............
A ɓangaren su HALIMATU kuwa bayan sun yi wanka sai da suka yi sallar isha'i sannan kowa ya sakko ƙasa,basu daɗe da sakkowa ba samarin gidan suma suka shigo.
Gaba ɗayan su kowa ya hallara akan dining table.halimatu ce ta tashi zata yi saving ɗin su.tuwon shinkafa ne da miyar vegetable,sai jollof ɗin kuskus da yaji kayan lambu sai ƙamshi yake,ga kuma gas meat shima da yaji had'i na musamman,ga kuma yoghurt fruit salad a gefe da ya ɗauki sanyi sosai.
Momy ta fara zuba wa tuwo, sannan ta zuba mata gas meat ɗin a wani ɗan bowl.cup ta ɗauka ta zuba mata fruit salad ɗin tare da saka mata spoon a ciki ta tura mata gabanta.
Fuskar ta ɗauke da murmushi tace "thank u my sweet daughter". Allah ubangiji yayi miki albarka"tace ameen momy"hafiz da Sadiq suma tayi saving ɗinsu, sannan ta zuba wa faruq nasa ta tura masa gaban sa.cikin d'aure fuska yace lallai ma yarinyar nan wato sai da kika gama zubawa kowa sannan zaki zuba min dan kin rainani ko!!"
Ya ƙarasa maganar yana hararar ta.momy tace masa"to sannu sarkin san girma, HALIMATU dai sa'arka ce sati biyu ne tsakanin ku,bar ganin ka fita girma ka zama ƙato kayi zatan wasu shekaru ka bata,to duka duka sati biyu ne rak ka bata".ta ƙarasa maganar tana hararar shi.sadiq ya kalle shi yana dariya harda yi masa gwalo.
"Momy kinga yana yimin dariya ko,salon ya jawo min raini a gurin yarinyar nan ko" yafad'a yana ƙara kumbure fuska, shi a dole ga babba. Itama dariyar tayi tace "ai dole yayi maka dariya baba farouq".
Gaba ɗayan su sai da suka kwashe da dariya, farouq ya d'ago ya dubi HALIMATU da take bawa yasmin abinci a baki ya ga itama dariyar takeyi yace"momy kinga abin da nake gaya miki ko?? gashi nan itama dariyar take yi min ai".kafin momy ta ƙara cewa wani abu hafiz yayi gyaran murya.
'Dagowa suka yi suna kallon sa,ya dubi momy yace"momy munyi waya da abba ɗazu yace min yana nan tafe gobe in Allah ya kaimu"tace ae nima haka yace min ɗazu da muka yi waya da shi.ta kalli farouq tace "kai kuma kafara shiri dan next week zaka tafi Malaysia karatu Sabo da abban ku ya gama maka komai".
Nan da nan farouq ya hau murna sabo da yana son zuwa Malaysia yayi karatu a can ɗin, shiyasa abba ya samo masa scholarship a can ɗin.murnar da yake yi ne tasa ya mance da b'acin ran da yake ciki.
Momy ta kalli hafiz tace"gobe idan kana da lokaci ina son ka ɗauki HALIMATU kuje kayi mata shopping, idan kun dawo zamu mufita unguwa tare da ita"yace wallahi momy gobe 7 zan bar gidan nan, sabo da ina da aiki sosai, ga kuma baƙi da zamu yi a company,kuma kinga shima sadiq yana da aiki sosai a office".
Tace"to shikenan babu damuwa ni sai na kaita goben da safe in Allah ya kaimu".suka amsa da ameen.
Hafiz da farouq duk suna aiki ne a kamfanin dadyn su wanda ake sarrafa ta kalma da jakun kuna.hafiz ya bawa sadiq shekara biyu, tare suka taso su biyun kansu ɗaya, wannan dalilin ne ma yasa aka saka su makaranta tare.tun daga primary har secondry,daga nan suka tafi Egypt sukayi degree ɗinsu na ɗaya da na biyu a fannin business.
Bayan sun dawo gida ne suka ci-gaba da kula da kamfanin dadyn su.sabo da dadyn nasu bai cika zama ba yanzu.
Bayan momy ta haifi sadiq sai haihuwar ta ɗauke mata tsawon wasu shekaru,sai daga baya ta samu cikin farouq.satin ta biyu da haihuwar sa aka haifi HALIMATU,shiyasa suka zamo sa'anni.
A yanzu haka hafiz shekarar sa ashirin da takwas ,shi kuma sadiq yana da shekara ashirin da shida ,farouq kuma yana da kusan shekara sha bakwai,ita kuma auta tana da shekara tara.farouq yana da girman jiki sosai shiyasa yake ganin kamar ya bawa HALIMATU wasu shekaru.bayan sun gama cin abincin ne mazan suka tashi suka tafi part ɗin su,su HALIMATU kuma kowa ya haye sama ya nufi d'akin sa.
Wannan kenan..........
A ɓangaren muktar kuwa bayan ya gama aikin da yake yi ne ya rufe laptop ɗin tare da tashi ya fito daga cikin d'akin ya sauka ƙasa, kitchen ya nufa ya jona kettle. domin bazai iya kwanciya ba sai ya sha coffee,bayan ruwan ya tafasa ya ɗakko coffee powder ya zuba tare da saka suger guda uku ya zuba ruwan zafi ya juya sosai.
'Daukan cup ɗin yayi ya fito daga cikin kitchen ɗin ya samu waje ya zauna a parlon yana kurb'ar coffee ɗin a hankali,sai da ya gama shanyewa tas sannan ya mai da cup ɗin cikin kitchen ya kashe wutar kitchen ɗin da ta parlon ya haye sama.
'Dakin rufaida ya nufa bakin sa ɗauke da sallama,ta d'ago ta dube shi ta amsa masa sama ,dan ita a zaton ta ma yayi bacci dan har ta fara murna, sabo da bata san takura wallahi.
Muktar ya dube ta yace"ki same ni a ɗaki na yanzu" har ya juya zai fita ya jiyo muryar ta tana cewa"gaskiya babu inda zani,dan wallahi a gajiye nake.kai kullum baka gajiya sai bak'ar jaraba,to idan kai baka gajiba gaskiya nina gaji "ta faɗa tana harare harare.
Wani irin 'kululun baƙin ciki ne ya tokare masa zuciya,cikin mutuwar jiki ya jawo sanyayyun ƙafa fuwan sa ya fito daga cikin d'akin ya nufi d'akin sa ya faɗa kan gado.yana ta juyi sakamakon cikin sa da yake yi masa ciwo.idan da sabo ya saba da halin rufaida,kwata kwata bata da tausayi.
Idan kuma ya kai ƙarar ta kuma sai ace ya ci-gaba da hak'uri ƙuruciya ce take cinta.tashi yayi yaɗau ki magani sa ya b'alla ya sha sannan ya koma ya kwanta,cikin ƙan'kanin lokaci bacci yayi awon gaba dashi................✍🏻
Daga al'kalamin FATIMA BINTU ABDALLAHI UMMU (AYSHA).........✍🏻
08162055134.
.
💝💞HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & writing
By
(FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens..............✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Page_____________13&14