← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 80

Sashe 17

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy ya ci-gaba da cewa "meye dalilin da yasa naga school bus ɗin makarantar yaran nan ta kawo su nan??" mukhtar yayi shiru bai yi magana ba,"kayi min shiru ba kace min komai ba,kai fa nake sauraro!!" ajiyar zuciya ya sauke tare da sunkuyar da kansa ya fara bawa daddy labarin duk abin da ya faru.

Shiru daddy yayi yana girgiza kan sa yana ƙara nazarin abun a cikin ransa.daga bisani ya ɗago da kansa ya dubi mukhtar tare da cewa "gaskiya yarin yar nan ta bani mamaki bata kyautawa kanta,kuma kaima saurin fushi ba naka bane ba,duk da cewa kayi ha'kurin zama da ita,amma in sha Allah idan na d samu time zanje gurin mahaifin nata muyi magana"

Ya ci-gaba da cewa "abu na biyu kuma a kwae yarinyar da na gani Alhaji Ibrahim yana ruƙon ta, mahaifiyar yarinyar yayar matarsa ce uwar su ɗaya uban su ɗaya,inaji ma zaka kasan ta tun da ranar nan da muka dawo da ita aka zo aka tarbe mu a airport,ina fatan dai ka gane ta" girgiza kansa yayi alamar ae, daddy ya ce "Alhmdllhi tun da ka gane ta, to itace na nema maka auren ta wajen Alhaji Ibrahim kuma alhmdllhi ya amsa mana ya bamu"

Ya cigaba da cewa"abin da yasa na nema maka auren ta naga kwata kwata baka jin daɗin auren da kayi,shiyasa na nema maka wannan ɗin a karo na biyu ko Allah zai sa a dace,sai dai kuma nayi karam bani ban fara neman shawarar ka ba,amma yanzu idan kaga bata yi maka ba ka gaya min sai in yi musu magana"

Ai da sauri ya ɗago da kansa ya dubi daddy yace"haba daddy me yasa kake faɗin hakan,kai fa mahaifi ne a gare ni,ai koda a ce bana sonta zan aure ta domin in faran ta maka rai.kuma nasan in sha Allahu baza ka zaɓamin abin da zai cutar da ni ba"ya ƙarasa maganar kansa a sunkuye.daddy yace"haka ne my son, Allah ubangiji yayi maka albarka ya dafa maka a dukkanin al'amuran ka" yace "ameen daddy".

Daddy ya ci-gaba da cewa "yarinyar karamar yarinya ce duka duka shekararun ta ba zasu wuce shekara sha shida zuwa sha bakwai ba,a yanzu haka jam zata zana sabo da haka sai kayi ƙo'kari ka sama mata gurbin karatu,domin ina son kafin ayi auren ku ta fara zuwa makaranta domin shine burin mahaifiyar ta,da cewa ma su kayi sai ta gama makaranta za su aurar da ita,to da na nemi alfarma ne sai akabar mana nan da shekara biyu ,amma duk da hakan na ƙara neman alfarmar a bar mana nan da shekara ɗaya,yace min zasu duba su gani" ya ƙarasa maganar yana kallon shi.

"Yanzu menene ra'ayin ka??" daddy ni duk abin da kuka yanke shine daidai" daddy yace "tom shikenan Allah ubangiji yayi maka albarka son"ya amsa da ameen.ya miƙe tare da cewa "daddy ina so na ɗan yi tafiya zuwa Dubai da London nan ba da daɗewa ba in sha Allah"Okey tom shikenan Allah ubangiji ya kaimu lokacin,amma ya kamata kasa mu lokaci kaje ku gaisa.

"Okay tom shikenan daddy,kamar wacce rana kake gani ya kamata inje ɗin?? daddy yace "bari mu gani nan da kwana biyu sai inyi wa Alhaji Ibrahim ɗin magana in yaso duk yadda muka yi zan gaya maka" girgiza kai yayi al'amar to.daga haka ya tashi ya nufi dining table dan ba ƙaramin yunwa yake ji ba.

HANNE

A ɓangaren hanne kuwa ta saki jiki sosai a gidan yayar ta altine,bata da damuwar komai sai dai ɗan abin da ba'a rasa ba,altine na iya bakin ƙoƙarin ta dan ganin ta faran ta mata rai kuma alhmdllhi.cikin haka ne ƙanin mijin altine da yake zuwa birni karatu ya ƙyalla idon sa yaga hanne,nan take ya faɗa kogin sonta baiyi ƙasa a gwiwa ba ya gaya wa iyayen sa shifa ya samu matar aure .

Su hanne basu san wainar da ake toyawa ba sai da uwar mijin altine ta kirawo ta ta bayyana mata komai,tace dan Allah a tuntub'i hanne aji ta bakin ta,nan take altine ta washe baki cike da murna domin yaron yana da mutunci ga kirki sannan kuma uwa uba ga ilimi,ya haɗa degree ɗin sa a birni yanzu ma ganin gida yazo shine Allah ya haɗa shi da hanne.

Tuntuni aka dameshi yayi aure yace shi sai ya gama karatun sa ya samu aiki zai yi aure,tun ana kawo masa 'yan mata a ce ya zab'a shi kuma sai yace basu yi masa ba,har aka gaji aka saka masa idanu sai gashi tashi daya yana ganin hanne yaji ya kamu da sonta.

Cike da farin ciki altine tazo ta samu hanne ta labar ta mata abin da yake faruwa,cikin Sa'a kuwa itama ta amince.nan take suka ƙulla soyayya mai tsaf ta gwanin ban sha'awa.yanzu ma zaune take a cikin ɗakin altine tayiwa yaran wanka tana shirya su tajiyo sallamar sama'ila saurayin ta,hijabi ta ɗauka ta saka,sannan ta amsa sallamar tare da fitowa tsakar gida.nan ta taradda shi tsaye da ledodi guda biyu riƙe a hannun shi, du'kar da kanta tayi cike da kunya ta gaishe shi,amsawa yayi yana mai kafe ta da kallon so yace mata"ga wannan!! zan ɗan je unguwa ne zuwa anjima zan dawo,ki shirya yau zanzo fira!! me zaki tanadar min??".cike da kunya ta ɗago da kanta ta dube shi tace me masoyi na yake so in tanadar masa??" ya ƙara duban ta a karo na biyu sakamakon jin wata kibiyar santa ta ƙara shiga cikin zuciyar sa yace"duk abinda kika ga ya dace dani ina so ki tanadar min shi masoyiyata". cike da kunya tayi maza ta shige cikin ɗaki ta barshi tsaye anan gurin,binta yayi da kallo cike da tarin sonta kafin ya juya ya fice daga cikin gidan.

Bayan taji fitar sa daga cikin gidan ne ta tura yara tace suje cikin gidan su kirawo mata altine,ai kuwa basu yi ƙasa a gwiwa ba suka she'ka da gudu suka je suka faɗa mata,nan take ta biyo bayan su suka dawo tare.tana shigowa hanne ta nuna mata ledodin da Sama'ila ya bata,jiki na rawa ta buɗe babbar ledar sabo da taji abu mai nauyi a ciki,kaji ne a ciki irin na turawa manya guda biyu gyararru da kuma zabi, ga kuma ledar cefanen kayan miya dasu mai dasu maggi.bud'e ɗaya ledar tayi nan ta yi arba da waya sabuwa key pad m kyau.nan take altine ta rafka gud'a tare da kallon hanne tace"ma sha Allahu ƙanwata kinyi babban goshi wallahi,ina tayaki murna,amma da ya kawo miki waɗan nan abin arzi'kin me yace Miki"ta faɗa tana duban hanne, "cewa yayi in tanadar mai wani abun zaije unguwa idan ya dawo zai zo hira anjima!!".altine tace "to tashi zama bai same mu ba". daga haka suka miƙe riƙe da ledar cefanen suka nufi tsakar gidan....

INNA LAURE

A ɓangaren inna laure kuwa bayan korar karen da malam musa yayi mata bata nufi ko ina ba sai gida,tana zuwa ta saka ɗan mukulli ta buɗe gidan cikin sauri ta sa kai ta shige cikin gidan gudun kar wani ya ganta,tana shiga ɗakinta ta nufa ta shige ciki,ba tare da b'ata lokaci ba ta hau bincike cikin ɗakin ko Allah zai sa ta samu wani abun, haka tayi ta dube dube babu ji babu gani duk inda ta san zata samu wani abun ta duba bata samu komai ba, daga ƙarshe da ta gaji dole ta ha'kura.

Fitowa tayi tsakar gidan ta samu kujera ta zauna tayi shiru tana tunani,ita yanzu ta ina zata fara nemo wa buba kuɗin sa ta bashi ko ta huta,gashi yanzu bata da komai hatta shanun ta da awakin ta na gado da take ta'kama dasu duk ankore su babu abinda ya rage mata yanzu.ta ƙarshe zancen zucin tana share hawayen da ya gangaro mata akan kuncin ta.

Tana tsaka da wannan tuna nin ne ta jiyo ƙarar buɗe ƙofa,ai da gudu ta tashi har tana tuntub'e ta shiga cikin ɗakin ta zaton ta buba ne da jama'ar sa,babu abinda jikin ta yake yi sai rawa kamar wacce zazzaɓi ya kama ta.tana cikin wannan halin ne ta jiyo muryar hansai tana kwala mata kira,nan take ta zabura da gudun ta ta fito tsakar gida,tana zuwa ta iske hansai tsaye tana ta rarraba idanu kamar munafuka duk ta firgice sai kace wadda aka koro ta.

Inna laure tace"hansai me ya same ki haka naga duk kin rame kin kwan tsame?? halan ko kinyi rashin lafiya ne??"ajiyar zuciya hansai ta sauke sannan ta samu kujera ta zauna ta dubi inna laure tace"hmmm laure ke nan!! ai idan rashin lafiya ne me sau'ki ne,kedai bari!! wallahi laure na rasa yanda zanyi da ta'kadirin yaron nan BUBA"ta ƙarasa maganar tare da fasewa da kuka
.

Cike da fargaba inna laure ta dube ta tace "dan Allah hansai kiyi min bayanin abin da ya faru!! wallahi bakiji yanda hankali na ya tashi ba!!"ajiyar zuciya hansai ta sauke ke mai haɗe da sheshe'ka sannan ta fara bawa inna laure labarin duk abin da ya faru, sannan kuma ta ɗora da bata labarin irin neman da buba yake mata.ai tun kafin hansai ta ƙarasa bata labarin ta fashe da kuka tana duban hansai tare da cewa"mun shiga uku hansai yanzu ya zamu yi kenan??".

Numfashi hansai ta sauke sannan ta dubi inna laure tace"ai laure bamu ga komai ba wallahi, tun da duk bala'in da muke ciki kece kika jaza mana shi!! sabo da haka ni yanzu na yanke shawarar da nake ganin zata fushshe ni nida ɗiya ta"inna laure tace "mu ajiye wannan maganar a gefe ni yanzu ki gayamin wacce shawara kika yanke??"

Hansai ta dube ta tace"shawarar da na yanke shine wallahi guduwa zamu yi nida Safara'u mu shiga cikin birni ko ma tsira da ranmu da lafiyar mu,domin bazan zuba ido shaid'anin yaron nan ya aure min 'ya ba".inna laure tace"to ni idan kika tafi kika barni yaya kike so inyi??" tace "oho ke kika sani ai kawai kowa yayi mai fushshe shi kawai" ta ƙarasa maganar tare da ficewa daga cikin gidan, ganin tayi ficewar tane yasa itama inna laure ta ɗauki mayafi ta yafa ta fito daga cikin gidan ta kulle sannan ta ɗauki hanyar gidan 'yar ta rahinatu ƙanwar altine....

BUBA
Chapter 17 · 0% Book details