← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 80

Sashe 55

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ƙarasa maganar tare da ɗaukar wayar sa ya shiga gallery ya buɗe hotunan ya miƙa wa nura wayar,karɓar wayar Nura ya yi tare da baza idanun sa yana kallon hotunan baki sake cike da mamaki!.
Ɗagowa ya yi ya kalli muktar tare da cewa,
"Dama wannan itace halimatun!!".
Murmushi mukhtar ya yi tare da jin jina masa kai.
"Taɓ ɗi jam!! lallai ka tsin ci dami a kala! to wai ma wannan yarinyar buzuwa ce ko shua Arab.??"
Wannan karan sai da mukhtar ya tuntsure da dariya sosai sannan ya ce,
"Asalin baban ta an ce buzaye ne,ita kuma maman ta bafulatana ce".
"Haba dai! yazu na ji zance, yarinya kamar ita ta yi kanta!ga kyau,ga diri kamar babbar mace,ga ƙuruciya,dan wannan yarinyar ba zata wuce shekara sha ta kwas ko ashirin ba!!"

"Barakallah ma sha Allah,karka cinye min mata, shekarar ta goma sha takwas"
Ya faɗa yana dariya.
"Taɓ ɗi jam!! gaskiya wallahi an cuci yarinyar nan idan akace za'a haɗa ku aure tare! domin ka yi mata tsufa sosai wallahi!!".
Ya ƙarasa maganar yana yiwa mukhtar dariyar mutunta.murmushin da yake kan mukhtar ne ya ɗauke,ya kalli Nura ya ce,
"Toh ɗan baƙin ciki mai hana ruwa gudu! ai sai ka hana mu gani ɗin! duk da tsufan nawa haka ita ma ta ƙyasa tace tana so idan ba ni ba sai rijiya!".

Dariya suka kwashe da ita gaba ki ɗayan su har da tafawa Nura yace,
"Wallahi babu wani nan wayo kawai ka yi mata ka kalallame ta kaga ɗanyar yarinya shakaf!"
"Toh naji na kalallame ta ɗin ɗan baƙin ciki,kuma ma na fasa kai ka gurin na ta"

"Afuwan abokina! ayi haƙuri".
Dariya suka yi gaba ɗayan su.
Ganin la'asar ta gabato ya sa mukhtar ya dubi nura tare da cewa,
"Tashi muje mu yi sallah,domin ina so in fita yanzu da an idar da sallar,za muje mu dubo kakan su sahal ba shi da lafiya ƴan fashi sun tare su akan hanyar su ta dawowa daga ENUGU shi da abokin sa,yanzu zan cen da nake yi maka sun kashe abokin nasa shi kuma sun nakasa masa ƙafafun sa da bullets har an yanke masa ƙafarsa guda! shine daddy yace na shirya muje mu dubo shi"

Shiru Nura ya yi yana girgiza kansa,daga bisani kuma ya ce,
"Gaskiya na tausaya musu sosai wallahi! Allah ubangiji ya bashi lafiya, shi kuma wanda ya rasu Allah ya jiƙansa"
Mukhtar ya amsa da "Ameen" .
Nura ya ce,
"Bari mu yi sallar sai na raka ka mu tafi"
Cike da jin daɗi mukhtar ya ce,
"Na gode sosai aboki na! ina matuƙar alfahari da kai a ko da yaushe"
Murmushi kawai nura ya yi tare da miƙewa ya shiga bedroom ɗin cikin office ɗin domin ya je ya ɗauro alwala,jim kaɗan ya fito yana yarfe ruwan da yake jikin hannunsa, mukhtar ne ya shiga shima ya ɗauro alwalar,ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗun guma zuwa masallacin da ke cikin company domin su gabatar da sallah.
Bayan an idar da sallar ne suka hau mota suka nufi company ɗin daddyn,suna zuwa suka taradda shi a shirye yana zanan jira,ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗunguma gaba ɗayan su a motar mukhtar suka tafi.

A bakin get ɗin gidan suka yi parking motar,fitowa mukhtar da Nura suka yi suka tsaya a ƙofar gidan suna neman yaron da zasu aika cikin gidan.
Wani yaro ne ya fito da gudu daga maƙoftan su hannun sa riƙe da taya yana garawa, kiransa suka yi tare da ce masa ya shiga gidan nan ya ce mukhtar da mahaifinsa ne suka zo,cikin sauri yaron ya gara tayar sa da gudu har cikin gidan tare da yin sallama.
Zaune ya tadda su a tsakar gidan an shimfiɗa babbar tabarma kowa yana zaune,gefe guda kuma rufaida ce kwance a kan katifa ita ma an fito da ita domin ta sha iska.

Sallamar yaron ce ta janyo hankalin su gaba ɗaya in da suka ji yaron yana cewa,
"Wai wasu mutane a ƙofar gida sun ce in zo in faɗa muku mukhtar da babansa ne suka zo"
Ya faɗa tare da juyawa da gudu ya grara tayar sa.
Cikin sauri har suna haɗa baki gurin tambayar yaron cewa,
Suna ina.??"
Yaron ya ce,
Suna ƙofar gidan nan!.
Ya faɗa yana fice wa daga cikin gidan.

Miƙewa Aminu ya yi tare da cewa,
"Daddy bari naje na shigo da su"
Alhaji USAMA ya ce,
"To yi maza kaje ka shigo da su kar su ga anbar su a waje"
Aminu ya ce "to" tare da fice wa wajen.
Bayan fitar Aminu ne hajiya hauwa ta gyarawa RUFAIDA kwanciyar ta tare da lulluɓe mata jikin ta sannan ta ɗakko tabarma ta shin fiɗa musu a gefe.

Hajiya hauwa ta buɗe baki kenan za ta yi magana suka jiyo sallamar su mukhtar, dakatawa ta yi da maganar da take son ta yi tare da gyara lulluɓin jikin ta.
Alhaji USAMA ne ya amsa musu sallamar tare da nuna musu kan tabarmar da aka shimfiɗa musu ya ce su zauna,bayan sun zauna ne aka shiga gaggaisa wa da juna.
Bayan sun gaisa ne suka yiwa Alhaji USAMA sannu da jiki, amsawa ya yi da murmushi a kan fuskar sa ya ce,
"Ina aboki na da matar yawa.?"
Daddy ya ce,
"Suna gida basu san da zuwan mu nan ɗin ba shi yasa,da yake daga office muke,amma suma za su zo su duba ka in sha Allah".

Murmushi Alhaji USAMA ya yi.
Daddy ne ya gyara zama tare da cewa,
"Ashe haka abu ya faru! wallahi bamu sani ba kwana na biyu kenan da jin labarin a wajen wani maƙocin ka dake nan baya kaɗan da ku,shima kaya yazo zai yi oder a Company ni na shi ne yake gaya min wallahi! kayi haƙuri da rashin zuwan mu da wuri,domin ya ce min ka kwana biyu kana jinya!!"

"Eh haka ne yau kusan watan mu ɗaya da sati uku,yau sati na biyu da sallamo wa daga asibiti,ita kuma RUFAIDA watan ta ɗaya da sallamo ta daga asibitin!!"
"Subhanallahi! Ita ma bata da lafiya ne.? me ya same ta ??"
Ya tambaya fuskarsa cike da mamaki.

Kuka hajiya hauwa ta fashe da shi tare da shige wa cikin ɗaki,ya yin da alhaji usama ƙwalla ta taru a cikin idanun sa.
Cikin dauriya ya ɗago tare da kallon su daddy muryar sa cike da rauni ya ce,
"Ai duk kusan lokaci ɗaya abin ya same mu"
Nan take ya basu labarin duk abin da ya faru! amma ya ɓoye musu zuwa wajen bokan da suka yi! ya dai ce musu kasuwanci ne ya kai su can garin ENUGU.
ya ƙarasa maganar tare da nuna musu RUFAIDA dake can gefen su kwance tana aikin kallon su,juyawa suka yi a lokaci guda suka kalli in da take kwance,hawaye suka gani a saman fuskarta shaɓe-shaɓe alamar ta daɗe da fara kukan,da yake ba jin muryar ta ake yi ba shi yasa.
Gaba ɗayan su sun girgiza da ganin halin da RUFAIDA take ciki,basu kaɗai ba dukkanin wani mai imani da tausayi idan ya ganta sai ya tausaya mata,gashi an ce bata iya yin komai sai dai a yi mata.

Nan take suka ji wani irin tsoron Allah ya ƙara shigar su,yau ina izzar ta ta! ina rashin mutuncin nata! ina wulaƙancin da tozarcin da take yiwa mutane!,shi ya sa duk abin da mutum yake yi ya kuka da kansa,domin duk ranar da Allah ya damƙeka a cikin second ɗaya zai mai da kai abin tausayi komai sai dai a yi maka, Allah ubangiji ya sa mu yi kyakkyawan ƙarshe.

Daddy ne ya ɗago ya kalli Alhaji USAMA ya ce,
"Alhaji ya kamata a nemo malamin da zai duba jikin nata.?"
Nan take Alhaji USAMA ya basu labarin zuwan malam jazuli da abubuwan da suka faru!.
Nan take jikin su ya ƙara yin sanyi sosai, musamman ma da suka ji matsalar ta mugayen shaiɗanu ne,kuma kowa ya san yadda rashin lafiyar iskoki take da wahalar warkewa.
Girgiza kai daddy ya yi tare da cewa,
"Allah ubangiji ya bata lafiya,a cigaba da yi mata addu'a sannan a dinga kunna mata karatun Alkur'ani akai-akai! kuma a samu wanda zai dinga tofa mata ayatul kursiyyu da falaƙi da nasi,in sha Allahu za ta samu lafiya".

Godiya Alhaji USAMA ya yiwa daddy sosai tare da neman gafarar su akan abin da suka dinga yi musu na rashin mutunci!.
Murmushi daddy ya yi tare da cewa,
"Wallahi babu komai Alhaji munyafe muku, Allah ya yafe mana zunuban mu baki ɗaya!"
Miƙewa daddy ya yi tare da cewa,
"Mu zamu tafi Alhaji! Allah ya ƙara lafiya!"
Ya faɗa tare da saka hannu a aljihun sa ya ɗakko bandir ɗin ƴan dubu-dubu sababbi guda biyu ya ajiye a gaban Aminu,suma su mukhtar kuɗi suka ɗakko masu yawa suka ajiye musu sannan suka ƙara yi musu sallama suka tafi.

Suna fita hajiya hauwa dake laɓe a cikin ɗaki ta fito kana ganin ta kasan taci kuka ba kaɗan ba,domin ganin da ta yiwa su mukhtar ya ɗaga mata hankali sosai! Ita kan ta tasan sun yi babbar asarar suruki wanda ba za su taɓa samun kamarsa ba.
Domin kallon da ta yiwa mukhtar ta ga alamun ci gaban da ya samu bayan rabuwar sa da yarsu har wata ƙiba ya yi sosai.wannan dalilin ne ya sanya ta kukan baƙin ciki da dana sani.

----------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------

"HALIMATU"

A ɓangaren su halumatu kuwa, daddy da momy suna ta shirye-shiryen su babu kama hannu yaro,duk wannan abin da ake yi halimatu bata da labarin komai domin momy bata faɗa mata komai ba.
Kwance suke a kan haɗaɗen gadon su na alfarma sun sanya kayan bacci a jikin su, daddy ne rungume da momy a cikin jikin sa yana ta rarrashin ta akan maganar auren halimatun,domin har yanzu taƙi kwantar da hankalin ta shi yasa ma bata faɗawa halimatun ba saboda karta ga raunin ta.
Chapter 55 · 0% Book details