← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 80

Sashe 5

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace "haba laure ai dai kya yi min sannu da zuwa kiji ko na iso lafiya ko!!"
Ta kuma tab'e baki a karo na biyu tace"ai na ganka k'alau,to meye zan wani b'ata bakina wajen tambayar lafiyarka"ya kalle ta ya girgiza kai yace "mai hali dai baya fasa halinsa!!"
tayi masa wani mugun kallo,harta buɗe baki da nufin ta yi masa tijara sai suka jiyo sallamar HALIMATU, malam ummaru ya amsa tare da bata izinin shigowa,bayan ta shigo ta dur'kusa cikin ladabi tace "baba dama momy na ce ta kano tazo shine tace in faɗa maka zata zo Ku gaisa!!"..

da sauri ya ɗago ya dube ta yace"ikon Allah ashe maryam ce tazo ma sha Allah,kice ina yima ta barka da zuwa!bari na fito mu gaisa"ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi....
Ya ɗago da kansa ya dubi inna laure da take yi masa wani mugun kallo yace "bari naje mu gaisa,ga buhu nan a gefen shimfida ta ki d'akko ki raba, tsaraba ce ,
ki bawa kowa tasa sa"....

Bai tsaya jin abin da zata ce ba,yayi ficewar sa daga dakin.
ko da ya fito ya iske hajiya maryam zaune a kan tabarma a ƙofar d'akin HALIMATU,shima ya samu waje ya zauna a kan tabarmar da HALIMATU ta shimfid'a masa a ƙofar d'akin sa.
zaman sa keda wuya inna laure ta fito da sauri ta nemi waje ta zauna kusa da shi.ko ta kanta baibi ba ya kai duban sa gurin hajiya maryam da take gaishe shi yace "lafiya ƙalau Maryam ya mai gidan naki da yaran ki! ina fatan duk kuna lafiya??"
tace "kowa yana nan ƙalau Alhmdllhi"
yace to ma sha Allah.
Bayan sun gaisa ta ɗago ta dubi malam ummaru tace da shi"dama magana ce take tafe da ni baban HALIMATU!!.....
yace "to to to ina jinki bismillah!!"
Tace "dama magana ce a kan HALIMATU, wannan karan ma dai na sake dawowa banyi zuciya ba,ina nan akan bakana na ɗaukar HALIMATU,saboda lokaci yayi da zata koma hannu na domin ta samu ilimi!! Kuma ina so na cikawa 'yar uwata burin ta,na ganin HALIMATU ta samu ilimi.kuma kaima kasan da wannan burin nata lokacin da take a raye!!"...

Kafin wani daga cikin su ya ƙara cewa wani abu Inna laure ta mi'ke a fusa ce tai tsalle ta dire tace"wallahi babu inda za'a tafi da HALIMATU!! kome Za'a yi ba zan bari a tafi da ita ba,eheee" ta ƙarasa maganar tana huci kamar zakanya.
Hajiya Maryam tace"ke dakata bada ke nake magana ba da ubanta nake magana idan tijara kike ji nid'in nan wallahi nafiki iyayin ta,kuma tafiya babu fashi sai dai kiyi duk abinda zakiyi".
Ta ƙarshe maganar tana wurga mata wani banzan kallo.....

Malam Ummaru yace "haba maryam, mai yasa zaki biye mata,naga dai nine na haifi HALIMATU ba ita ba,saboda haka nine zan yanke hukunci ba ita ba!!"...
ya ƙara sa maganar idanun sa akan hajya Maryam, sannan ya ɗora da cewa "zanyi tunani akan maganar zuwa gobe in sha Allah"
Tace to Allah ubangiji ya kaimu....
daga haka ta mi'ke ta shiga cikin ɗaki ta tadda HALIMATU tana kuka, sakamakon jin duk abin da ya faru.tana jin tsoron kar inna laure ta zuga baban ta ya hana momy tafiya da ita.
da sauri hajiya maryam ta nufi inda take zaune ta jawo ta ta rungume ta,tana rarrashin ta,"tace yi shiru daughter in sha Allahu tare zamu tafi"ta ƙarasa maganar tana goge mata hawayen fuskarta.da 'kyar ta samu ta rarrashe ta tayi shiru.....
Bayan tayi shiru momy ta d'ako musu gasashen kifin su da suka siyo a kasuwa da lemo da ruwa,suka ci suka ƙoshi.
bayan sun kammala suka zauna suna ɗan hira kafin su kwanta.......

A ɓangaren malam ummaru kuwa bayan shigewar hajiya maryam ɗaki Inna laure ta fara sauke masa tijara kamar ba gobe ba,tace wallahi muddin ya bari aka tafi da HALIMATU shida kwan ciyar hankali har a bada, domin baza ta taba barin sa ya zauna lafiya ba.
Shi kuwa malam ummaru da yaga abin nata ba mai ƙarewa bane ba,sai kawai ya tashi yayi shigewar sa cikin d'akin sa, yayi addu'a yayi kwanciyar sa ya barta a nan waje tana ta saba bi.

Sai da tayi mai isarta sannan ta yun'kura ta tashi ta bi bayan sa,ko da ta le'ko d'akin sa taga har ya kwanta a kan shimfid'ar sa,haba wa nan take farin ciki ya lullubeta,saboda tana ganin ha'karta zata cimma ruwa!!!............✍🏻

To fa,ya kuke ganin zata kaya a nex page??,shin malam ummaru zai yadda hajiya maryam ta tafi da HALIMATU???

Shin aikin boka ɗan makau zaici HALIMATU da malam ummaru????

Wai ina labarin buba????

Wannan amsar tana cikin nex page ɗin mu in sha Allah!!
Kuci gaba da bibiyata a cikin labarin HALIMATU............✍🏻

Ina godiya da addu'ar ku gareni,ina yi muku fatan alkhairi na gode.........✍🏻

08162055134

💝💞HALIMATU💝💞

(Love,carefice, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & writing

By

FATIMA BINTU ABDALLAHI (UMMU AYSHA)

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITERS ASSOCIATION)

Golden pens...............✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Page________________7&8

Washe gari da safe bayan sun yi sallar asuba momy ta ɗakko musu ragowar gasashiyar kazar nan suka karya da ita.
Momy tace mata taje ta kai mata ruwa banɗaki tayi wanka.ba tare da b'ata lokaci ba ta kai mata ruwan wankan,tazo ta dur'kusa tace mata"momy na kai miki ruwan wankan"....
"Okay,sannu doghter,bara naje nayi idan na fito sai ki shiga kema kiyi wankan".

ta faɗa tana ficewa daga d'akin...

Bayan fitar ta HALIMATU ta share d'akin ta gyara, ta buɗe bayan 'kyaure ta ɗakko kwad'on ramar da inna laure ta kawo mata ta haɗa a cikin shara taje soro ta zubar a cikin bokitin sharar su.

Ko da ta dawo momy har ta fito daga wanka tana shafa mai,cikin sauri ita ma ta fito ta ɗibi ruwa a bokiti ta shiga banɗaki.

Lokacin da ta fito daga wankan yayi daidai da shigowar malam ummaru gidan, tun asuba da ya fita sallah sai yanzu ya shigo cikin gidan.
Cike da ladabi HALIMATU ta dur'kusa har ƙasa ta gaisheshi ya amsa a sake.yace"ina 'yar uwarki Hanne?"
Tace "tana bacci bata tashi ba,amma bari naje na taso ta"har ta mi'ke yace "a'a 'kyale ta har ta tashi jeki ki kirawo min momyn ta ki,kice ina son magana da ita".

HALIMATU tace to............

ta juya ta nufi cikin d'akin, tana shiga ta iske hajiya maryam tana waya da mai gidan ta,inda yake sanar da ita driver na kan hanya ya kusa ƙarasowa,suyi sauri su shirya.tace masa to tare da katse kiran a jiye wayar tayi tare da kai duban ta ga HALIMATU in da take sanar mata da sa'kon baba.

tace mata to, tare da mi'kewa ta saka mayafin ta ta fito tsakar gidan,ita ma HALIMATU ta biyo bayan ta suka fito tare.koda suka fito sun iske malam ummaru zaune a kan tabarma yana jan carbi, HALIMATU ta dakko ta barma ta shimfid'a,har ta juya zata bar wajen yace mata ta dawo ta zauna itama....

Zama su keda wuya sai ga inna laure ta fito daga cikin d'akin buguzun buguzun ta samu waje ta zauna kusa da malam ummaru tana harare harare..

Shiru ne ya ɗan gifta a tsakanin su kafin malam ummaru yayi gyaran murya,ya d'ago da kansa ya dubesu gaba ɗayan su yace.........

"Alhmdllhi maryam nayi tunani akan maganar ki,kuma nayi nazari akai, dama tun farko badan komai na hana miki tafiya da HALIMATU ba sai dan bana so tayi nisa da ni. sabo da ganin ta yana ɗebe min kewar mahaifiyar ta.amma yanzu dole na baki ita ko dan na cikawa mahaifiyar ta burin ta, kuma nima ina so ta samu ilimin zamani da na arabiyya.dan Allah ki riƙe min ita amana,nasan idan tana tare da ke baza tayi kukan maraici ba,zata samu farin ciki sosai , sabo da ke kaɗai na yadda zaki iya riƙe min ita amana".....

Hajiya maryam "tace in sha Allah zan yi iya bakin gwargwado na wajen ganin na inganta rayuwar ta".

yace mata "tom Allah yasa".....…

A fusa ce inna laure ta mi'ke ta na huci ta zunduma ashar tace"wallahi babu inda za'a tafi da HALIMATU,idan kai wannan muna fikar matar ta asirce ka,to ni asirin ta bazai tab'a cina ba, sabo da haka babu inda za'a tafi da ita"

Ai kafin ta ƙarasa maganar malam Umaru ya buga mata wata firgitacciyar tsawar da ta bata mamaki, sabo da tun da suke tare da shi bai taba yi mata irin wannan tsawar ba.

ta d'ago a firgice ta dubeshi inda yake nuna ta da hannun sa yace mata "wallahi laure idan baki shiga hankalin kiba zanyi mummunan saɓa miki "

ta ɗora hannu a kai tare da sub'u cewar baki tace "na shiga uku ni laure wai me yake shirin faruwa dani ne!! malam kana cikin hankalin ka kuwa??"

bai saurare ta ba ya dubi hajiya maryam yace mata"kafin na baki HALIMATU ina so na ji idan tana da ra'ayin binki to bazan hana miki tafiya da ita ba,idan kuma tace a'a to bazan tilas ta taba"

ya faɗa yana kai duban sa ga HALIMATU yace mata"kina so ki bi momyn ki ta tafi da ke gidan ta ko ba kya so??"

HALIMATU ta yi shiru ta sunkuyar da kanta a ƙasa.ganin tayi shiru ta ƙiyin magana yasa inna laure tayi wani makirin murmushi a zuciyar ta tace"idan aikin boka makau bai ci kaba ai ita ya cita.

Malam ummaru yace "ke muke sauraro HALIMATU,kinyi shiru ko bakya son bin ta ne??"...........

Cikinta sauri ta d'ago da kanta ta dubi malam ummaru tace"baba ina so zan bita"...

Yace to "ma sha Allah , Allah ubangiji ya kaiku lafiya,in sha Allahu idan na samu lokaci zan diga kawo muku ziyara".....

kafin wani daga cikin su ya ƙara yin magana wayar hannun hajiya maryam ta fara ringing,ta kai hannu ta d'aga ta kara a kunnen ta,tace "okay tom,gamu nan fitowa" ta faɗa tare da tsinke wayar.

ta dubi malam ummaru tace "driver yazo ɗaukar mu yana jiran mu a waje,bari mu je mu ƙarasa shirya wa"........
Chapter 5 · 0% Book details