← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 80

Sashe 18

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafe suke suna ta ifface ifface a kan hanya,a haka har suka ƙarasa shiyar su malam musa . suna shiga suka ɗaga makaman su duk wanda suka ci karo dashi sai sun kai masa sara da suka,babu abinda kake ji sai ihu da koke koke,duk gidan da suka faɗa sai sun sassari mutanan gidan sannan su kore duka dabbobin gidan ko kaza basa bari,a haka har suka iso gidan malam musa.

Suna shigowa suka fara cin karo da
babban ɗan gidan malam musa zai fita waje ya duba yaga abin da yake faruwa sakamakon ihu da suka ji yana tashi,nan take wani daga cikin su ya kai masa sara da suka nan take ya zube ƙasa yana ihu sakamakon yankan da aka yi masa a gadon bayan sa.ihunsa ne ya fito da malam musa da gudu daga cikin ɗaki ko riga babu a jikin sa,lamunde na biye dashi a baya da zani ɗaure a ƙirjinta.

Kafin malam musa yayi wani yun ƙuri buba ya ɗaga adda ya sara mai a ƙafa,nan take ya zube ƙasa yana ihu yana birgima, lamunde na ganin haka ta kurma uban ihu ta ruga a guje zata fita waje,kafin ta ƙarasa wani daga cikin su yayi sauri ya kafta mata adda a gwiwar ƙafar ta ji kake ƙasssss,nan take ta ƙara kurma uban ihu a karo na biyu itama ta zube a ƙasa.

Ganin haka yasa buba ya umarci yaran sa da su bincike ko ina a cikin gidan ko zasu ga inna laure,nan take suka fara dube dube amma basu ga ko me kama da ita ba suka zo suka sanar da BUBA, girgiza kai yayi tare da cewa suje su tattaro duk wani abu da suka gani a cikin gidan.nan take suka je suka tattaro ragowar kaji da zabin da suka rage da kuma manyan ragunan da ɗansu yazo dasu ɗazu daga legas na haihuwar matar sa,gaba ɗaya suka haɗa suka tafi dasu,suka bar su malam musa kwance cikin jini suna numfar fashin wahala.

HALIMATU

A ɓangaren su HALIMATU kuwa bayan sun fita daga gidan direct makarantar islamiyya suka nufa mai suna tarbiyya,suna shiga farouq yayi parking a harabar Makarantar.direct office ɗin shugan makarantar suka nufa,bayan sun gaisa ne farouq yayi masa bayanin komai, nan take shugaban makarantar ya ɗaga waya ya kirawo wani malami yace ya sameshi a office ɗin sa yanzu,babu daɗewa sai ga malamin ya shigo bakin sa ɗauke da sallama, amsawa sukayi farouq ya bashi hannu suka yi musa baha.

Bayan sun gaisa ne shugaban makarantar ya yiwa malam aminu baya ni dangane da HALIMATU yace yana so yayi mata interview.nan take malam aminu ya fara yiwa HALIMATU tambayoyi,daga bisani yayi mata Interview.bayan ya gama ne ya kalli ustaz shugaban makarantar yace masa "Alhmdllhi gaskiya yarinyar tana da ƙoƙari sosai da sosai!! sabo da haka zamu saka ta a aji huɗu in sha Allah" ya faɗa yana kallon HALIMATU ƙasa ƙasa.

Malam ustaz yace"to ma sha Allah, Alhmdllhi,yanzu bari na baka form ka cike sannan ka biya kuɗin sauran abubuwan,in yaso da an ɗinka mata uniform sai ta fara zuwa . farouq yace "okay tom shikenan babu damuwa in sha allah.daga haka aka bashi Form ya cike tare da biyan duk abin da ake biya sannan suka baro makarantar.

RUFAIDA

Zaune suke ita da mahaifiyar ta suna ta ƙullawa suna kwance wa, sallamar mahaifinta ce ta katse musu hirar da suke yi.guri ya samu kan kujera ya zauna,gaishe shi RUFAIDA tayi ya amsa yana mai ƙare mata kallo tare da cewa "ina fatan dai lafiya ko"kafin ta buɗe baki ta bashi amsa umma tayi zuruf tace "ina fa lafiya" nan take ta bashi labarin duk abin da ya faru, girgiza kai yayi fuskarsa babu annuri yace lallai yaron nan!! ni zai wulak'an ta ya sako min ke!! ku biyu Allah ya bamu keda yayanki, sannan kuma ace baza kiyi rayuwar 'yanci ba, to wallahi zai gamu da fushina, yanzu ma bari na je na kirawo uban nasa ayi wadda za'ayi".ya ƙara sa maganar tarda da miƙewa tsaye ya fice daga cikin gidan.

Wannan kenan.....................✍🏻

Ina mutuƙar godiya da tarin addu'o'in ku a gare ni , kuɗin masoya ne na gari,ina yi muku fatan alkhairi ƙwari da gaske..

Sai mun haɗu da ku ranar Monday in sha Allah.

Daga al'k'alamin FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA).........✍🏻

08162055134

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens...............✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Page_____________23&24

"RUFAIDA"

A ɓangaren su rufaida kuwa lokacin da mahaifinta ya fita domin ya kirawo daddyn mukhtar,yana fita ya nufi shago domin siyen katin waya sakamakon ƙarewar da nasa yayi.bayan ya loda katin ɗari biyar ne yayi dialling numbern daddy, ringing ɗaya biyu a na uku ya ɗauka tare da yin sallama,ba dan ya soba ya amsa sallamar.daga ɗaya ɓangaren daddy yace "malam amadu barka da wannan lokaci ya gida ya iyalin??"

Yace "dakata Alhaji Auwal!! ba gaisuwa na kirawo ka muyi ba, sabo da haka ka riƙe gaisuwar ka!!" daddy yace ikon Allah! to me yake tafe da kai??" mahaifin RUFAIDA yace "ai wallahi nasan kasan komai dangane da abinda yake faruwa, sabo da duk irin rashin mutunci da ɗanka yake yiwa 'yata da sanin ka,bama wannan ba yanzu meye dalilin da yasa ya sakar mun 'yata??".

Daddy yace"kayi hak'uri malam amadu,wallahi dama ina da niyyar in zo har gida na same ka a dai dai ta yaran nan,to kuma sai gashi ka rigani" ya ci-gaba da cewa"yanzu tunda mai faruwa ta faru ayi hak'uri"."ai dama dole ka cemin nayi hak'uri, tun da ɗanka ya riga da ya cutar min da 'yata,to wallahi maza maza tun wuri ka saka shi ya mai da ita ɗakinta!!"

Ya ci-gaba da cewa"ai naji komai daga bakin RUFAIDA ta gayamin duk abinda ya faru,akan dalilin banza da wofi zai sakarmin yarinya,to wallahi bari kaji in gaya maka Alhaji Auwal! ni ban haifi 'yata dan taje ta bautawa wani ba!! idan bata huta taji daɗin rayuwarta ba mai kuke so tayi!! Sabo da haka wannan sa'ko ne na baka ka gaya wa ɗanka tun wuri ya zo ya mai da ita!!"ya ƙarasa maganar yana mai bada umarni"

Daddy yace"ka gama naka jawabin??" daga ɗaya ɓangaren yace"na gama!" yace to "bari kaji in gaya maka Alhaji amadu, mukhtar dai ɗana ne nina haifi abuna, Sabo da haka baka da wani iko akansa,kuma da kake maganar yazo ya mayar da 'yarka bazai mayar da ita ɗin ba,ai shiru shiru ba tsoro bane ba,yanzu na ƙara tabbatar da cewa baku da tarbiyya gaba ɗayan ku,to sabo da haka kaje ka koyo tarbiyya sannan ka koyawa taka 'yar itama,muddin mace bazata tsaya tayi bautar aure ba wallahi ban ga amfanin auren ta ba!! sabo da haka mun barmaka 'yarka kaje ka riƙe abarka".daga haka ya tsinke kiran gaba ɗaya ya bar malam amadu da waya a hannu baki sake....

"MOMY"

A ɓangaren momy kuwa bayan ta shiga bedroom ɗin kaya ta canja na alfarma,tare da ƙara gyara jikinta tayi kwalliya mai kyau abin ta,turare masu daɗin ƙamshi ta ƙara feshe jikin ta da su sannan ta sakko ƙasa abin ta,sakkowar ta babu daɗewa daddy ya yi sallama.cike da takun nutsuwa da ƙasaita ta nufi daddy tana sakar masa wani ƙasaitaccen murmushi,nan take yayi sauri ya buɗe mata hannu ta shige ya mayar da hannun tare da rungume ta ya sauke ajiyar zuciya.

Wani irin sanyi da nutsuwa yake ji suna saukar masa tun daga cikin ruhin sa,domin muddin idan yana tare da momy yana samun nutsuwa da kwanciyar hankalin ɗari bisa ɗari, Sabo da Ita ɗin ta musamman ce a cikin rayuwarsa.hannun sa yasa ya ɗago da kanta tare da sakar mata kiss a goshi,cikin sauri ta runtse idanun ta tare da sakin murmushin nan nata mai kashe masa zuciya ...

Buɗe idanun ta tayi tare da saka su cikin ƙwayar idanuwan sa tace"barka da zuwa mijina abin sona kuma abin alfahari na"ta faɗa tare da kai hannu ta shafi sajen fuskar sa.wani irin daɗi daddy yaji mara misaltuwa tun daga ƙasan zuciyar sa.yace"yauwa mar'atussaliha ta ya gida da fatan na same ki lafiya" tace "lafiya k'alau Alhmdllhi my nurul ƙalbi".

Daga haka ya kama hannun ta suka shigo cikin parlon.direct kan dining table ya nufa da ita tare da cewa"zoki bani abinci yunwa nake ji matata" ya ƙarasa maganar yana kallon ta tare da marairai ce fuska.cikin sauri ta tashi tare da cewa"yanzu kuwa mijina" daga haka ta fara saving ɗinsa,bayan ta gama ne ta fara bashi a bincin a baki yana ci yana kallon ta tare da saka mata albarka a haka har ta gama bashi abincin ....

Bayan sun gama ne daddy ya saka hannu ya riƙe ƙugun ta tare da miƙar da ita suka nufi kan three seater sofa suka zauna.hira suka ɗan fara taɓa wa, a cikin hirar ne yake sako mata zancen da suka yi da Alhaji Auwal, bayan ya gama bata labarin ne ya dube ta yace "me kike gani game da abin da yace??" ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "na riga da na baka go a head duk abin da ka yanke shine dai dai in sha Allah, HALIMATU 'yarka ce duk hukuncin
da ka yanke yayi dai-dai".

Daddy yace "tom shikenan ngd da ƙaramawarm da kika yi min,kuma in sha Allahu zamuji daɗin wannan haɗin da yardar ubangiji" ta amsa da "ameen".ya cigaba da cewa "ɗazu bayan mun rabu dashi ya kirawo ni yake cemin mukhtar yana so yazo su gaisa da HALIMATU, shine yake nemar masa izini!! to nace masa yazo ɗin kinga hakan ma tunani ne mai kyau,ko ba komai zasu ƙara fahimtar junan su, shine na ce masa yazo jibi sabo da gobe zasu zana jam" ya ƙarasa maganar yana kallon MOMY.

MOM tace"hakan ma yayi sosai mijina" yace "to sai ku fara shirye-shiryen tarb'ar baƙo" ya faɗa yana dariya, itama ɗin dariyar tayi.nan suka ci-gaba da hirar yanda abin zai kasan ce.suna cikin hirar ne suka jiyo sallamar su HALIMATU sun dawo,suna shigowa suka dur'kusa har ƙasa suka gaida daddy da MOMY suka amsa cikin sakin fuska.
Chapter 18 · 0% Book details