Sashe 29
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin haka ne baba lado ya umarci HARUNA mijin altine da mazan nan da suka ruƙe baban kamilu da suzo su ruƙe masa Inna laure,ba tare da ɓata lokaci ba suka ruƙeta tare da danne ta baba lado ya ci-gaba da aikin sa.wani irin firgitaccen ihu inna laure ta kurma tare da saka hannu ta fizge ɗankwalin da yake ɗaure a kanta ta fara fizgar gashin kanta sabo da azaba.
Babu Abin da kake ji yana tashi a cikin gidan sai ihun inna laure da koke koken su Hanne.gaba ɗaya inna laure ta gama jigata,hawaye da majina duk sun ɓata fuskar nan tata,fitsari kuwa tayi shi ya kai sau biyar sabo da a zaba,a haka malam lado ya gama gyaran ƙafar tata.shi kanshi ba ƙaramar wahala ya sha ba, Sabo da karaya uku ta samu da tsagewar ƙashi,shi yasa ya wahala wajen dai dai ta ƙasusuwan nata.
Bayan an gama ne altine ta gyarawa inna laure jikin ta,ita kuma HANNE ta gyara gurin da aka kwantar da ita, HARUNA mijin altine ya umarci altinen da HANNE su zauna a wajen inna laure domin su kula da ita,idan yaso yaran sai su zauna a wajen mahaifiyarsa.shi kuma baban kamilu tuni rahine ta gyara masa jikin sa,yayin da ƙannen sa guda uku suka zo suka cicciɓe shi suka tafi dashi gida,dole rahine tabi bayan su domin kula da mijin ta .
"HALIMATU"
A ɓangaren su HALIMATU kuwa, tun da ta kwanta bata farka daga bacci ba sai a suba,gabatar da sallah tayi tare da yin azkar sannan ta ɗauki ƙur'ani ta fara karatu cikin daddaɗar muryar ta.bayan ta gama karatun ne ta ajiye ƙur'anin tare da nunke hijab ɗin da tayi sallar da sallaya ta ajiye akan side drawer.zama tayi a ƙasa tare da jawo Ledodin da MUKHTAR ya kawo mata, buɗewa ta fara yi domin ta ƙagu ta ga abin da yake cikin su.
Ledar farko wasu irin manya manyan biscuits ne masu tsadar gaske kala kala shaƙe da ledar,mayar dasu tayi gefe tare da jawo ɗayar ledar ta buɗe, chocolate ne manya manya masu tsada kala kala shaƙe a cikin ledar,sai kuma ledar ƙarshe wadda tafi kowacce girma, ƙunshe take da tarkacen alawoyi,chewngum,kalolin yoghurt da kuma lemuka.
Samun kanta tayi cikin matsanan cin farin ciki da annashuwa,ajiye kayan tayi tare da sakkowa down stairs.bata iske kowa a parlon ba, direct kitchen ta nufa domin ɗora break fast. tsaya wa tayi tana tunani abinda ya kamata ta ta ɗora,ƙwai ta ɗebo guda ashirin ta wanke tare da zubawa a tukunya, fridge ta buɗe ta ɗakko ɗanyar hanta ta yanka ta ƙana tare da wanke ta tas ,tukunya ta ɗakko ta zuba hantar da ƙwan sannan ta yanka albasa da tafarnuwa da citta da seasoning,ta kunna gas ta ɗora akai.wake ta ɗebo ta gyara ta wanke shi tsaf, sannan ta sanya shi a cikin blender taɗan bubburga shi kaɗan yanda zai surfu,sannan ta juyeshi ta wanke shi tsaf ta ajiye a gefe.
Fridge ta buɗe ta ɗebo tattasai da attaruhu ta gyara,sannan ta ɗebo albasa a store itama ta gyara ta haɗe su waje ɗaya,blender ta ɗakko babba ta zuba waken da ta gyara tare da attaruhu da tattasai da albasa,tafarnuwa da citta da black papper ta ɗan zuba akai,sannan ta ɗakko seasoning da mix spices ta zuba akai tare da zuba mai da ɗan manja.
Bayan ta gama haɗa komai tayi blending ɗin su gaba ɗaya,sai da ta tabbatar sun yi laushi sannan ta juye a cikin wani babban bowl,ƙwan ta tsame ta zuba a cikin ruwan sanyi ta ɓare su,ita kuma hantar ta juye ta a cikin ƙullun alalar,leda ta ɗakko ta fara zuba ƙullin alalar ta a ciki,duk ledar da ta zuba ƙullin sai ta jefa ƙwai guda ɗaya a ciki,haka tayi tayi har ta gama ƙullawa gaba ɗaya.
Steammer ta ɗakko ta zuba ruwa a ƙasan ta, sannan ta rufe tare da jera alalar a ciki ta rufe ta ɗora akan wuta tare da rage wutan a medium low flame.markaɗaɗɗiyar gyaɗa ta ɗakko a cikin bucket ta ɗiba a cikin bowl,ruwa ta zuba ta dama gyaɗar sosai sannan ta tace ta zuba a cikin tukunya.kus kus ta ɗebo ɗan kaɗan ta watsa a ciki sannan ta ɗebo kamu a cikin fridge ta zuba ruwa kaɗan ta dama a cikin cup ta ajiye a gefe sannan ta ɗebo suger kaɗan ta zuba a ciki.
Tafasa kunun ya fara yi,sai da ta ga gafin gyaɗar ya ɗan rage sannan ta sauke a ƙasa,ƙullin ta ɗakko taɗan zuba kaɗan ta saka abin juyawa ta juya sosai,sai da taga kaurin yayi mata yan da take so sannan ta ɗakko ruwan lemin juice ta zuba kaɗan a ciki tare da juya wa.madarar gari ta ɗakko ta ɗibi three cup ta dama da ruwan sanyi sannan ta zuba a cikin kunun ta motsa shi sosai,sannan ta ƙara ɗakko condence milk itama ta zuba three cup a ciki ta sake motsawa.
Kyakkyawan flacks babba ta ɗakko ta zuba a ciki,sannan ta zubawa su inna laure da su baba mai gadi nasu.zuwa tayi ta buɗe alalar ta taga ta nuna tayi kyau sosai Sai tashin ƙamshi take yi,ba tare da ɓata lokaci ba ta sauke tare da ɗakko haɗaɗɗun food wamers ta zuba a ciki.cikin sauri ta haɗa haɗaɗɗiyar source ɗin ƙoda mai ɗan karan daɗi,gaba ɗaya gidan ya bure da ƙamshin girkin HALIMATU.
Tana gamawa ta gyara kitchen ɗin tsaf tamkar ba'ayi girki a cikinsa ba,sannan ta kwaso kayan ta jere su a kan dining table. up stairs ta haye zuwa ɗakin ta domin ta yi wanka ta shirya, sabo da yau zata fara zuwa makarantar islamiyya ƙarfe takwas.
A ɓangaren MOMY kuwa lokacin da ta sakko down stairs domin shiga kitchen,sai taji wani irin ƙamshin girki mai daɗi da yake tashi, kitchen ɗin ta nufa domin duk a tunanin ta baba ladi ce,turus tayi a bakin ƙofa lokacin da tayi arba da HALIMATU ta haƙiƙan ce tana ta aikin haɗa musu break fast.murmushi tayi tare da juyawa ta koma sama ba tare da ta bari HALIMATU ta ganta ba, domin dama tana da niyyar fara practice ɗinta a wajen girki.
Kowa ya hallara a dinnig ɗin ana yin break fast,ba su MOMY kaɗai ba hatta su yaya ya hafiz sun cika da mamakin cewa HALIMATU ita ce tayi girkin nan, daddy kuwa gyaɗa kansa kawai yake yi sakamakon daɗin da girkin yayi masa.halimatu kuwa babu abin da take yi sai murmushin jin daɗi,ita kanta ta yaba wa kanta ƙokarin girkin da tayi.
Bayan sun gama yin break fast ɗin ne daddy yayi gyaran murya tare da kallon HALIMATU yace "gaskiya naji daɗin abincin da kika girka mana ƴata Allah ubangiji ya ƙara zaƙin hannu,ki ci-gaba da maida hankali kina koyon abubuwa kinji" HALIMATU tace " tom daddy in sha Allahu na gode" MOMY ce ta kalle ta tace " tun da kin shirya tashi farouq ya kai ki makaranta" cike da zumuɗi da jin daɗi tace"to". Miƙewa tayi tare da ɗaukar jakar makarantar ta suka fita .
"MUKHTAR"
A ɓangaren mukhtar kuwa, lokacin da ya koma gida wanka yayi tare da yin sallar isha'i yayi addu'a,yana idar wa ya sakko ƙasa zuwa kitchen ya haɗa coffe ya zuba a cikin mug.plate d bowl ya ɗakko ya zuba spring rolls da samosa,sannan ya zuba dambun nama,sauran ragowar kuma ya zuba a cikin frizer.ɗakkowa yayi ya fito daga kitchen ɗin zuwa dining, zama yayi tare da yin bismillah ya fara cin abincin sa, sai da yacin ye gaba ɗaya yana santi sannan ya tashi ya kai kitchen ya ɗauraye ya kife tare da kashe glove ɗin ya rufo kitchen ɗin.
Glove ɗin parlorn ya kashe tare da haye wa sama yayi kwanciyar sa.ƙarfe huɗu ya tashi yayi nafil fili tare da yin addu'a sosai Allah ubangiji ya tabbatar musu da Alkhairin sa shida HALIMATU.bashi ya tashi a gurin ba sai da aka kirawo sallar asuba sannan ya sakko ya nufi masallaci.sai da gari yayi haske sosai sannan ya baro masallacin,yana shigowa gida kitchen ya nufa ya haɗa coffee tare da warming ɗin snacks ɗin sa yayi break fast.
Bayan ya gama ne ya haye up stairs zuwa ɗakin sa tare da yin wanka ya shirya cikin suit black colour baƙaramin kyau MUKHTAR yayi ba sai tashin ƙamshin ddaɗan turarukan shi yake yi.brief case ɗin sa ya ɗauka tare da sakkowa ƙasa,cikin sauri ya fice daga cikin gidan sabo da yana da ayyukan da zai yi da yawa a office..
Ina matuƙar godiya a gareku masoya na masu Albarka abin alfharina,babu abin da zance muku sai godiya tare da fatan Alkhairi
Dafa alƙalamin FATIMA BINTU (UMMU AYSHA)...................✍🏻
Share fisabilillahi......
O8162055134
💝💞HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens...............✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
Pages____________32&34
"MUKHTAR"
A ɓangaren mukhtar kuwa lokacin da ya isa zuwa office ɗin ya taradda ayyuka masu tarin yawa akan table ɗin sa,hakanne ya ɗauke shi lokaci mai tsawo yana duba ayyuka da dama,ba shi ya samu kansa ba sai wajejen sallar la'asar.bayan sun yi sallar la'asar ne suka jero tare shida Nura abokin sa suna tafe suna ɗan tattaunawa akan wasu muhimman ayyukansa, direct office ɗinsa suka suka wuce.
Suna shiga suka samu waje suka zauna akan sofa,fridge nura ya buɗe ya ɗakko musu ruwa da lemo masu sanyi ya ajiye musu akan center table.gorar ruwan ya buɗe tare da kafawa a bakin sa ya sha fiye da rabin ruwan sannan ya ajiye ragowar ruwan tare da sauke ajiyar zuciya, ɗago kai Nura yayi ya kalleshi tare da cewa "ya dai! Ina fatan kana lafiya!"
Ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na biyu tare da cewa "ina lafiya ƙalau Alhmdllhi abokina,ka tayani murna wani abun Alkhairi ne ya same ni!".gyara zama nura yayi fuskarsa ɗauke da murmushi ya kalli MUKHTAR ɗin yace "ai naga alama tattare da kai! bani labari abokina!!". Murmushi yayi tare da gyara zama ya fara bawa nura labarin HALIMATU tun daga farko har ƙarshe.