← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 80

Sashe 66

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zabuwa guda ɗaya ya zube musu cikin plate ɗin tare da haɗin gas meat guda ɗaya, sannan ya buɗe ɗaya ledar ya ɗakko fresh milk da drinks ya zuba musu a cups.miƙewa ya yi tare da kama hannun ta ya sakko da ita ya zaunar da ita a kusa da shi tare da ya ye lulluɓin fuskarta, janyo plates ɗin ya yi gaban ta tare da cewa,
"Bismillah!"
A hankali tace masa "na ƙoshi"
Ɗebo tsokar naman ya yi tare da kaiwa bakin ta yace,
"Buɗe bakin ki bana son gardama!!"
Ganin da ta yi babu wasa a cikin idanun sa ya sa bata yi masa gardama ba ta buɗe bakin ta a hankali ya shiga bata naman,sai da yaga tana kauda kan ta gefe alamar ya ishe ta sannan ya ƙyale ta.

Fresh milk ya bata ta sha sannan ya fara cin naman shima,bayan sun gama ya tattare kayan ya kai kitchen ya wanke sannan ya shiga bedroom ɗin sa ya ɓallo paracetamol guda biyu ya ɗakko ruwa mara sanyi sosai ya bata tasha da ƙyar, domin halimatu bata son magani sai dole.

Kama hannun ta ya yi ya kai ta har bedroom ɗin ta tare da cewa ta shiga toilet ta yi brush da alwala sannan ya fice ya barta a cikin ɗakin, alwala ta shiga ta yi tare da yin brush sannan ta fito daga cikin toilet ɗin ta zauna a gefen bed ɗin ta,zamanta babu daɗewa ya shigo cikin ɗakin sanye da pajamas milk colour masu santsi hannun sa ruƙe da sallaya.
Shimfiɗa musu ya yi tare da yi mata umarni akan ta tashi su yi nafila raka'a biyu domin su godewa ubangijin su bisa ni'imar da ya yi musu,ta shi ta yi ta bi bayan sa suka gabatar da sallar, bayan sun idar ne ya kama kanta ya yi ta kwararo musu addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin rayuwar auren su.

Bayan sun shafa ne ya juyo ya kalle ta tare da yi mata tambayoyi game da addini,cike da mamaki yake kallon ta domin bai yi zaton zai iya samun amsar su daga bakinta ba,miƙewa ya yi tare da buɗe wardrove ɗin ɗakin ya ɗakko mata wata rigar bacci mai kyau iya gwiwa.
Matsowa ya yi kusa da ita tare da miƙa mata rigar yace,
"Ki cire waƴannan kayan na jikin ki sun yi nauyi da yawa ki saka wannan"

Yana gama magana ya juya ya fita daga cikin ɗakin.
Ganin ya yi ficewar sa ne ya sa ta shiga toilet ta chanja kayan ta fito tare da kashe fitilar ɗakin ta rufe ƙofar ta tare da yin addu'a ta kwanta a kan gadon.....✍🏻✍🏻

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi,ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin Alkhairin sa ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi🙏🏻🙏🏻

Daga alƙalamin
FATIMA BINTU ABDULLAHI(, UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻

Share fisabilillahi.

Game buƙatar littafin HALIMATU tun daga farko zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ni ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻

08162055134.

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)...✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens....✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages___________86&87

_____________Kiran sallar asuba ne ya tashe ta daga nannauyan baccin da ya yi nasarar ɗaukanta ba tare da ta shirya ba, sakamakon gajiya da kukan da ta sha ga kuma ciwon kai sune suka haɗu guri ɗaya suka bada gudunmawar saukar mata da bacci mai nauyi ba tare da ta shirya yin baccin ba, saboda tsoro da fargaba da suka cika mata zuciya.
A hankali ta janye bargon da ta lulluɓe jikin ta da shi ta tashi zaune tare da yin addu'ar tashi daga bacci, zuraro ƙafafuwanta ƙasa ta yi tare da miƙewa a hankali ta nufi cikin toilet bakin ta ɗauke da addu'a,wanka ta yi da ruwa mai zafi ta yi brush tare da ɗauro alwala ta fito daga cikin toilet ɗin ƙugun ta ɗaure da towel.

Lotion ɗin ta ta ɗan shafa da body misk sannan ta zura doguwar riga da hijabi ta shimfiɗa sallaya ta tada sallar nafila kafin a tada sallar asuba ɗin,turo ƙofar bedroom ɗin nata mukhtar ya yi domin ya tashe ta ta yi sallah ya tarar da ita tana sallah.
Wannan lamari ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba sosai domin bai saba ganin haka a cikin gidan sa ba,cike da murmushi ya juya ya fita zuwa masallacin da yake kusa da gidan su zuciyar sa wasai ko ba komai tun daga yanzu ya fara ganin chanji a game da sabon auren da ya yi.

Ba ita ta tashi daga kan sallayar ba sai da ta yi addu'o'i ta yi azkar tare da yin karatun Alkur'ani, lokacin da ta idar har gari ya fara yin haske,cikin sauri ta miƙe tare da gyara ɗakin ta sannan ta fito ta nufi ɗakin da take tunanin a nan muktar ya kwana ta shiga ta gyare masa shi tsaf ta wanke toilet ɗin ta fesa air freshener a toilet ɗin da betromm ɗin.
Fitowa ta yi ta gyara parlon saman duk da ba wani datti ya yi ba ta kunna turaren wuta da air fresheners masu daɗin ƙamshi sannan ta sauka zuwa parlon ƙasa ta gyare shi tsaf shima.
Ƙofar da take tunani nan ne kitchen ta nufa tare da ƙarewa kitchen ɗin kallo tsaf,domin ba ƙaramin haɗuwa ya yi ba kana gani kasan an kashe masa dukiya sosai,gaba ɗaya gidan ma an zuba masa furniture's masu tsada sosai irin na ƴar gata,gaskiya momy da daddy sun yi ƙoƙari sosai,domin sun fitar da ita kunya wallahi,babu abinda za ta ce musu sai dai godiya da addu'ar fatan Alkhairi.

A hankali ta ji wasu hawaye masu ɗumi sun gangaro mata saman fuskar,cikin sauri ta saka bayan hannun ta ta goge hawayen tare da fara duba abubuwan da suke cikin kitchen ɗin,kusan komai akwai a cikin kitchen ɗin kama daga shinkafa, taliya,macaroni,indomie,cuscus,semi,flour,irrish,doya,eggs da sauran su.
Kusan komai na amfani akwai shi,ga manyan freezers guda biyu da suke ɗauke da kalolin nama daban daban da kifi, sannan ga kayan miya da vegetables da fruit's da dai sauransu,cikin sauri ta ɗebo irrish ta feraye ta wanke tare da tsane shi a cikin coolender, sannan ta kunna gas cooker ta ɗakko sabon frynpan ta zuba mai ta ɗora a kan wuta,sai da man ya yi zafi sosai sannan ta fara soya irrish ɗin.
Tukunya ta ɗakko ta wanke tare da zuba tea spice mix acikin ta zuba ruwa ta ɗora a kan wuta, sannan ta buɗe freezer ta ɗakko ragowar kajin jiya ta ƙara gyara su tare da yin warming ɗin su a cikin oven.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta soya irrish da sauce ɗin ƙwai da hanta, sannan ta haɗa da gashin kaza da kuma tea ta zuba a kyakkyawan food wamers masu kyau ta kwashe ta kai dining ta jere su tsaf,gaba ɗaya gidan ya gauraye da ƙamshin turare da na girkin ta.tana cikin gyara kitchen ɗin mukhtar ya shigo cikin gidan domin ya tsaya a waje suna gaisawa da maƙoftan sa.
Wani irin daddaɗan ƙamshi ne ya daki hancin sa tare da sanyin ac ɗin da yake aiki a cikin parlon,nan take ya lumshe idanun sa yana jin wani irin farin ciki da annashuwar da bai saba jin su ba,cikin sauri ya nufi cikin kitchen ɗin domin yana jiyo motsin mutum a ciki,tsayawa ya yi ta bayan ta yana ƙare mata kallo ganin yadda ta gyara kitchen ɗin tsaf kamar ba ayi amfani da shi ba.

Ƙamshin turaren da ta ji ne ya sa ta juyo bayan ta da sauri,ganin wanda yake tsaye ne ya rungume hannayen sa a kan ƙirjinsa yana ƙare mata kallo ne ya sa ta yi sauri ta durƙusa a ƙasa ta muryar ta na rawa tace,
"Ina kwana"
Murmushi ya yi tare da ƙarasowa in da take tsugune ya kamota ya miƙar da ita tsaye tare da juyar da ita ya saka ta a jikin sa ya zuro da kan sa saman kafaɗar ta yana shin shinar wuyan ta tare da sakar mata kiss a wuyan ta ya ɗora hannun sa guda ɗaya a cikin jikin ta yana yawo da shi,nan take jikin ta ya kama rawa kamar mazari ta yi ƙasa da nufin durƙushewa ƙasa sakamakon rawar da ƙafafun ta suka kama yi domin sun gaza ɗaukar ta.
Cikin sauri ya taro ta tare da juyo da ita suna fuskantar junan su,a hankali ta buɗe baki zata yi magana ya yi sauri ya haɗe bakin su waje ɗaya ya fara yi mata wani irin French kiss mai tsayawa a rai kamar mawuyacin zaki,cikin sauri ta fara kiciniyar ƙwatar kanta amma ina bata da wannan ƙarfin domin ya yi mata irin ruƙon da bazata iya ƙwacewa ba.

Sai da ya ji ta fara kuka sannan ya cika ta ba tare da hakan ya gamsar da shi ba,cikin shaƙaƙƙiyar muryarsa ya kalle ta tare da cewa,
"Daga yau haka ake gaisawa da miji kin ji ko.?"
Jinjina kan ta ta yi tare da cewa,
"To" tana share hawayen fuskar ta.
Hannun ta ya kamo ya saka ta a cikin jikinsa yana rungume da ita suka fito daga cikin kitchen ɗin, direct upstairs suka nufa ya jata zuwa ɗakin sa,zama ya yi akan sofa ɗin da take gaban gadon tare da cewa,
"My love taho ki taya ni cire kayan jikina ki yi min wanka kin ji!!"
Ya faɗa fuskarsa babu alamun wasa a cikin ta.
Cikin sauri ta kalleshi idanun ta sun yi wuƙi- wuƙi tana shirin yin kuka tace,
Chapter 66 · 0% Book details