Sashe 7
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
08162055134
💝💞 HALIMATU 💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed )
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & writing
By
FATIMA BINTU ABDALLAHI (UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens.............✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Page______________9&10
Tana cikin bacci kawai sai taji an faɗo mata ajikin ta,tana buɗe idanun ta suka haɗa ido da auta yusra tana tayi mata dariya,nan da nan ta rungume a jinta cike da murnar ganin ta,tace"oyo yo my yusra,an dawo daga school??"
ta girgiza mata kai alamar ae
ta dubi HALIMATU ta ce "aunty momy tace tare kuka zo ko??"ta faɗa tana duban ta.halimatu tace "ae tare mukazo da momy auta"
ta washe baki tace "amma ba zaki tafi ki barmu ba ko??"
ta faɗa tana b'ata fuskar ta.
HALIMATU tayi murmushi tace mata "in sha Allah muna tare auta,bazan tafi na barku ba"
nan take ta hau tsalle tana murna.ta kamo hannun ta tace mata"muje in cire miki uniform ɗin inyi miki wanka".
ta miƙe suka fito suka nufi d'akin auta.suna shiga HALIMATU taga d'akin ya burgeta, komai na d'akin pink colour ne,ga kayan wasa na yara,kan gadon an jera mata teddy's a kai gwanin ban sha'awa.
batare da b'ata lokaci ba ta cirewa auta uniform ɗin ta,ta kama hannun ta suka shiga toilet tayi mata wanka ta nad'ota cikin towel.
ta zaunar da ita a kan gado.ta duba kan mirror ta ɗakko lotion ta shafe mata jikinta dashi.
Bayan ta gama ta buɗe wardrove ta ɗakko mata wata simple gown pink colour mara nauyi ta saka mata,ta ɗakko turare ta fesa mata.
Ta ce mata "taso muje na zuba miki abinci ki ci". ta faɗa tana kamo hannun ta suka fice daga d'akin suka sauka ƙasa.
Koda suka sakko sun iske hafiz zaune a kan dining table yana cin abinci, Sadiq da farouq kuwa suna kan kujerar a zaune.shi Sadiq yana ta faman latsar wayar hannun sa, shi kuma farouq yana riƙe da remote a hannun sa yana chanja channels.
Farouq ne ya fara ganin ta ya dube ta da murmushi akan fuskarsa yace"well come home little syster".da sauri Sadiq ya d'ago kai ya dubi inda farouq yake kallo yaga HALIMATU tsaye tana murmushi.
Shima nan take ya saki murmushi yana cewa "barka da zuwa ƙanwar mu,da fatan kunzo lafiya.ai ɗazu da muka shigo kina bacci momy ce ta hana mu tasheki"
ya faɗa da murmushi akan fuskar shi.halimatu ta taho ta gaisheku suka amsa fuskar su a sake.shi kuwa sarkin muskilanci hafiz bai ce mata komai ba.duk abin da ake yi yana ji amma yayi shiru ko d'agowa beyi ba.
yana ta faman kwasar abincin sa.halimatu ta ja hannun yusra suka nufi dining table ɗin.suna zuwa ta rusuna ta ce" yaya hafiz ina wuni? da fatan mun same ku lafiya" ya d'ago kamar bazeyi magana ba,sai da ya gama ƙare mata kallo sannan yace mata "I'm fine,ya hanya??"
tace"lafiya k'alau yaya". daga haka bata ƙara magana ba ta ɗauki plate ta zubuwa yusra abincin ta. ta kama hannun ta suka dawo falon suka zauna akan kujera. tana bata abincin a baki ita kuma suna hira da su farouq.kiran sallar la'asar ɗin da akayi ne yasa mazan suka tashi suka tafi masallaci
ita kuma ta kama hannun auta suka hau sama don suje suyi tasu sallar a d'aki.
wannan kenan.........
A ɓangaren Inna laure kuwa lokacin da tafita daga gidan afujajan bata nufi ko ina ba sai gidan aminiyarta hansai,ko cikakkiyar sallama batayi ba ta faɗa cikin gidan.ta iske hansai tana shirin fita daga gidan.hansai na ganin ta tace "kamar kuwa kinsan inda kike na nufa,amma tunda yanzu kinzo shikenan.ina fatan dai an dace??"
ta ƙarasa maganar tana duban inna laure.inna laure ta buɗe baki da ƙyar kamar tayi kuka tace ina fa,wallahi babu nasara hansai,malam ya bawa matar nan HALIMATU ta tafi da ita.kuma duk yanda boka yace in yi haka nayi.
Hansai tace " kar dai kice min duk kanwar jace ni dake,dan wallahi yarin yar nan ta b'allo mani ruwa ban san yadda zanyi ba.inna laure ta zaro idanun ta tana tambayar hansai me ya faru.
Ai nan take hansai ta fashe da kuka sosai tare da cewa"wallahi laure yarinyar nan lafiya ƙalau tayi wankan maganin nan ta saka kwallin nan a idanun ta,ta fita da niyyar su haɗu da ɗan gidan mai gari,tana cikin tafiya kawai sai ga buba da jama'ar sa sun zo wucewa.
tsau tsayi yasa tayi tuntub'e da ƙafar ɗaya daga cikin su, d'agowar da zata yi suka haɗa ido da buba,nan take ya rungume ta da ƙyar aka samu ya cika ta.ta rugo da gudu ya biyo bayan ta har cikin gidan nan".
ta ci-gaba da cewa "ai ni naga tashin hankali jiya laure,yanzu haka yace babu wadda yakeso a garin nan sai Safara'u,kuma babu wanda ya isa ya hana shi auran ta.dan yace mani ma ya fasa auren HALIMATU.kuma kuɗin da ya baki zaije ya karb'o abin sa ya ƙara yayi hidimar auren Safara'u".
"Wallahi laure na yi kuka iya kuka na rasa yanda zan yi,kin san halin buba ya gagari kowa a garin nan.muddin ana son zaman lafiya dole a yi masa abin da yake so"
ta ƙarasa maganar tana kuka tare da fyace majina.
Inna laure da tun kafin ta ƙarasa jin labarin cikin ta ya ɗuri ruwa,nan take taji fitsari na shirin zubo mata.ai nan da nan tayi sauri ta ɗauki buta tayi ban ɗaki.
ba fitsari kaɗai tayi ba,har da zawo tayi saboda tsabar tashin hankalin da ta shiga.
bayan ta fito ne ta iske hansai zaune tayi ta gumi,taje itama ta samu waje ta zauna tace"na shiga uku!!yanzu hansai ya zamu yi?? Kodai mu koma wajen bokane!! gashi kuma wallahi babu kuɗi a hannu na!!"
Hansai tace"bazamu koma wajen boka makau ba,dan bamu san abin da zamu tarar ba.sai dai mu canza wani wajen,dan bazan taɓa bari shed'anin yaron nan ya auri Safara'u ba".
Wannan ke nan................
*************************************************
ASALIN LABARIN......................
Malam ummaru mahaifin HALIMATU haifaffen garin jigawa ne,a wani local government da ake kira haɗeja .Mahaifinsa malam sale da Mahaifiyarsa rakiya haifaffun garin ne.
Shikad'ai iyayen sa suka haifa,kasan cewar Allah be basu haihuwa da wuri ba sai da suka fara manyan ta. daga shi kuma Allah bai ƙara basu haihuwa ba....
Malam ummaru ya taso cikin soyayyar iyayen sa. mahaifinsa yana da gona babba guda ɗaya da yake nomawa.
Duk lokacin da ya noma idan amfanin gona yazo yakan loda kayan abincin a akori kura ya rage wanda za suci a gida,ragowar kuma ya kai kasuwar cikin birni ya siyar.
Haka yake yi duk lokacin da amfanin gona yazo.lokacin da malam ummaru ya zama saurayi girma ya fara taso masa sai mahaifin sa yake tafiya dashi kasuwar.yana nuna masa yanda yake harkar kasuwancin sa.
Lokacin da tsufa ya tasowa malam Saleh sai ya kasance malam ummaru ne kaɗai yake zuwa ya kai kayan da kanshi idan amfanin gonar yazo.
A kwana a tashi ba wuya gurin ubangiji.kwatsam wata rana mahaifin sa ya kwanta rashin lafiya,watan sa ɗaya yana jinya Allah yayi masa rasuwa.malam ummaru yaji mutuwar mahaifin sa sosai.
Bayan rasuwar mahaifin sa sai nauyin mahaifiyar sa ya dawo kansa.gashi itama girma ya kama ta.sai kawai ya yanke shawarar yayi aure sabo da idan baya nan ya samu mai kula masa da mahaifiyar sa.
A lokacin ne ya nemi auren inna laure yarinyar ma'kocin su,yana tsammanin zata zauna ta kula masa da mahaifiyar sa.
Da farko dai da suka yi auren tana kula da mahaifiyar sa,amma daga baya komai ya canja.idan ya tafi kai kayan amfanin gona kasuwa inna laure tayi ta azabtar da mahaifiyar sa.
Tun tana yi a bayan idanun sa har tazo daga baya tana yi a gaban idon sa.idan ta dafa abinci bata bata sai taga dama,kuma malam ummaru baya iya yi mata magana saboda ta mallake shi.
Kullum mahaifiyar sa abun yana damun ta.dalilin damuwar da tasa a ranta sai hawan jini ya kama ta,nan take ta kwanta rashin lafiya.
Wata rana ta tashi da ciwon ciki, sakamakon rashin wadataccen abincin da bata samu.
Satin ta ɗaya tace ga garinku nan.fad'ar irin baƙin cikin da malam ummaru ya shiga ba'a magana.bayan anyi sadakar bakwai malam ummaru ya ƙaduri niyyar ƙara aure.
A lokacin inna laure nada yara guda biyu,altine da hajara.dama akwai wata bafulatana mai suna hafsatu a kasuwar da yake zuwa kai kayan amfanin gona, ta na kai musu tallar fura da nono ita da ƙawar ta Maryam.
Rugar da suke babu nisa da kasuwar, sai Allah ya haɗa jinin su da malam ummaru.nan take soyayya ta shiga tsakanin su,har maganar soyayyar su taje gaban iyayen su.
Beyi ƙasa a gwiwa ba yaje har rugar su tare da kawun sa suka tambayi auren hafsatu.batare da b'ata lokaci ba suka bashi sabo da sun yaba da hankalin sa da nutsuwar sa.
A lokacin itama ƙanwar ta Maryam ta samu wani da yake zuwa kasuwar sarin kayan abinci yana kaiwa garuruwa.
Sai aka haɗa su ga baki ɗayan su aka aurar da su.ita hafsatu aka kaita haɗeja,ita kuma maryam aka kaita cikin garin Kano rijiyar zaki. auren su ba dad'ewa wata rana cikin dare gobara ta tashi a cikin bukkar da iyayen su suke,dukkan su babu wanda ya fita gaba ɗayansu suka ƙone ƙurmus.lokacin da su hafsatu suka samu labari sun yi baƙin ciki sosai,sunyi kuka ba kaɗan ba saboda mutuwar ta shige su sosai.
Malam ummaru yana matuƙar san hafsatu sabo da tana da hankali ga hak'uri ga tsafta,uwa uba kuma ga ladabi da biyayya.sai Inna laure ta fara cisguna mata kuma malam ummaru baya iyayi mata magana saboda ta riga ta mallake shi......
Haka ta ci-gaba da hak'uri da daɗi babu daɗi babu wanda ta taɓa faɗawa halin da take ciki.
Wata rana ƙanwar ta maryam ta kawo mata ziyara,nan taga halin da take ciki.ai kuwa nan rigima ta b'arke tsakanin ta da inna laure har da dambe.
Ai kuwa tace sai malam ummaru ya sakar mata 'yar uwarta, dan bazata yadda a kashe mata ita a banza a hofi ba sabo da ita kaɗai ta rage mata.
Da ƙyar malam ummaru ya shawo kanta ya bata hak'uri yace za'a gyara.bayan tafiyar ta babu abinda ya ragu sai ma abin da ya ƙaru.