Sashe 43
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kina sona ne my love..?"
Cike da yarin ta tace masa:
"Eh mana habibi ina sonka mana sosai"
Wata irin ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauke har tana jiyo sautin ta,nana take wata iriyar nutsuwa ta shige shi sosai hankalin sa ya kwanta.
Ba tare da ɓata lokaci ba yayi bismillah ya fara cin abincin sa,spoon ɗin farko ya lumshe idanun sa Sabo da daɗin abincin da kuma test ɗin sa.
Sai da ya cika cikin sa sosai sannan ya sha haɗaɗɗen Kunun ayar da ta haɗa masa sosai ya yi hamdala ga Ubangijin sa, tissue ta miƙa masa ya goge bakin sa.
Miƙewa ya yi tare da kamo hannun ta ya nufi kan sofa da ita ya zaunar da ita, durƙusawa ya yi a gaban ta tare da saka hannu a cikin aljihun sa ya ɗakko wani ɗan ƙaramin boxs ya buɗe shi.
Wasu kyawawan zobunan gold ne guda biyu a cikin boxs ɗin,ciro su ya yi tare da kama hannun ta na dama ya yi bismillah ya saka mata zoben a ɗan yatsan ta,wani irin shock yaji kamar an jona masa wutar lantarki a jikin sa, ɗaya hannu ya kamo a hankali ya saka mata ɗaya zoben.
Cikin sauri ya janye hannun sa domin wani iri yake ji idan ya taɓa hannun ta,ita ma a nata ɓangaren wani ɓaƙon yana yi taji a cikin jikin ta.
Cikin Murmushi ya kalle ta tare da cewa:
"Wannan shine ɗan ƙaramin tukwicin girkin da aka yi min,ina fatan zaki ƙara dagewa wajen koyar abubuwa masu mutuƙar mahimmanci".
Cike da mamaki ta ƙarewa hannayen ta kallo sannan ta ɗago idanun ta ta kalle shi tare da cewa:
"Habibi ai wannan kyautar tafi ƙarfina!!"
Ta faɗa idanun ta na kawo ƙwalla.
"In ji waye ya gaya miki!ai kin fi ƙarfin wannan sau milions,baki san ke ɗin tsadar tsada bace my love, ke ɗin ƙasaitacciyar mace ce mar'atussalaha fa,dan haka kar na ƙara ji kin furta hakan kin ji my love!!"
Ya ƙarasa maganar yana kashe mata idon sa guda ɗaya.
"Nagode Allah ubangiji ya saka da alkhairi ya ƙara arziƙi mai albarka"
"Amin my love,ai babu godiya a tsakanin mu"
Ledar da ke kan kujera ya ɗakko ya miƙa mata tare da cewa:
"Ga phone ɗin ki nan na kawo miki Sabo da mu din ga gaisawa bana so muna takurawa MOMY,akwai sim card a ciki da numbers ɗina in sha Allahu gobe jirgin mu zai tashi da misalin ƙarfe takwas na safe"
Har ta buɗe baki da nufin yi masa godiya ya ɗaga mata hannu tare da cewa:
"Banason godiyar nan my love".
Badan ta so ba ta yi shiru da bakin ta.
Ya ci gaba da cewa:
"Monday zaki fara attending lectures,banda wasa da kula kulen ƙawayen banza,ban da kula maza kuma,karatu ne ya kai ki Sabo da haka shi nake son ki dage ki yi,da zarar an tashi driver zai ɗauke ki ya mai dake gida okay!"
Girgiza masa kanta ta yi alamar eh.
Kallon ta ya yi tare da cewa:
"Ni zan wuce me kika tanadar min na tafiya"
Ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi.
Cike da kunya tace:
"Na tanadar maka da dambun nama,cake da cookies"
"Iyye duk ni kaɗai haka, gaskiya ana ji da ni sosai ko"
Murmushi ta yi tare da girgiza masa kanta.
"Okay tom je ki ɗakko min sai ki rakani na tafi"
"To" tace tare da ficewa daga parlon ta nufi kitchen,robobin ta ɗakko guda uku ta fito da su riƙe a hannun ta,a parlon ta iske shi bakin ƙofa yana jiran ƙarasowa ta.
Tana ƙarasowa ya karɓi robobin tare da ficewa daga parlon,bin bayan sa ta yi suka nufi parking space in da ya buɗe motar sa ya sanya su a back seat.
Juyowa ya yi ya kalle ta tare da cewa:
"Ni zan wuce my love,pls ki kula min da kan ki kin ji..? Idan na ƙarasa gida zamu yi waya"
"Allah ubangiji ya kai ka lafiya ya dawo da kai gida lafiya, Allah yasa tafiyar ta zamto matakin nasara da ɗaukakar ka ƙwarai da gaske, Allah ya baka abin da kaje nema cikin nasara, Allah ya tsare gaban ka da bayan ka Habibi na,tsau tsayi da asara Allah ya kare ka"
Ta ƙarasa maganar cikin raunin murya.
Wani irin abu ya ji tun daga cikin ƙwaƙwalwar sa har cikin zuciyarsa, iyayen sa ne kawai suke yi masa irin wannan addu'ar sai kuma ita,ba ƙaramin jin dadi adduar tata ya yi ba.
Ɗagowa ya yi ya kalle ta tare da cewa
"Ameen Amin Amin my love, na gode sosai! Pls ki ci-gaba da yi min addu'a kin ji ko..?"
"To habibi in sha Allah".
Daga haka suka yi sallama kamar kar su rabu da junansu.
Wannan kenan........✍🏻
Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni, ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku a gare ni, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa,ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi.
Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA).....✍🏻✍🏻
Ga masu buƙatar littafin HALIMATU tun daga farko zuwa in da aka tsaya su yi min magana ta wannan numbern👇🏻👇🏻
08162055134.
Share fisabilillahi........
💝💞 HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDALLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens.........✍🏻✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages____________53&54
______________Bayan tafiyar mukhtar ita ma ta shige cikin parlo bata iske kowa a parlon ba sai ta wuce zuwa sama, ɗakin MOMY ta nufa domin ta nuna mata abin da MUKHTAR ɗin ya kawo mata.
Da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga cikin ɗakin, MOMY ta iske zaune a bakin mirror tana fesa turare,waje ta samu gefen bed ɗin ta zauna tare da cewa:
"MOMY barka da dare"
"Barka dai HALIMATU, mukhtar ɗin ya tafi ne.?"
"Eh MOMY ya tafi,kinga ma abin da ya kawo min"
Ta faɗa tana tashi daga in da take zaune ta miƙawa MOMY ledar hannun ta.
Wucewa ta yi da sauri ta fice daga cikin ɗakin sabo da kunya,ba tare da ta jirawo ta ji abin da momy zata faɗa ba.
Bedroom ɗinta ta nufa domin ta samu ta ɗan kwanta, Sabo da akwai gajiya a tattare da ita ga shi kuma gobe zata fara zuwa makaranta,night dress ta ɗakko ta sanya bayan ta cire kayan jikin ta,glove ɗin ɗakin ta kashe tare da kunna bedside lamp.
Hawa ta yi bisa gadon tare da yin addu'a ta ja bargo ta kwanta cike da tunanin mukhtar a cikin zuciyar ta.
Washe gari tun asuba ta ta tashi ta yi sallar asuba tare da yin azkar ,bayan ta idar ne ta sakko ƙasa zuwa kitchen domin ta haɗa musu break fast,ba tare da ɓata lokaci ba ta fara shirya musu lafiyayyiyar alaka da kunun gyaɗa mai daɗin gaske da kuma pepper soup na kayan ciki.
Tana cikin yin aikin ne baba ladi ta zo ta kama mata suka ci-gaba da yin aikin,ƙarfe takwas suka gama yin break fast ɗin,cikin sauri ta fita daga kitchen ɗin ta bar baba ladi ta ƙarasa gyara kitchen ɗin ta jera abin cin akan dining,domin sauri take yi taje tayi wanka ta shirya kar ta yi late sabo da yau ɗin nan zata fara attending lectures.
Direct bedroom ɗin ta ta nufa ta faɗa toilet ta yi wanka a gurguje,tana fitowa ta tsane jikin ta da towel tare da shafa mai a jikin ta, doguwar riga ta ɗakko mai dogon hannu ta saka,rigar bata da bauyi ko kaɗan,domin cikin kayan da MUKHTAR ya kawo mata ne na siyayyar zuwa makaranta.
Ɗankwalin doguwar riga ta ɗaura a kanta tare da fesa turare kaɗan mai sanyin ƙamshi,sabon cover shoe ɗin ta ta ɗakko ta saka a kyakkyawar farar ƙafar ta ya zauna cif cif gwanin ban sha'awa.
Cupboard ta buɗe ta ɗakko sabuwar jakar goyon ta mai kyau ta a jiye a kan gadon, buɗewa ta yi tare da saka dukkanin wani materials da tasan zata buƙata game da karatun ta,hijabi ɗin ta ta ɗakko ƙato ta sanya wanda ya zo mata har ƙasa tare da ɗakko niƙaf ta saka a cikin Jakar ta.
Jakar ta saɓa a bayan ta tare da ficewa daga cikin ɗakin ta nufi ƙasa,ko da ta sakko ta iske daddy da MOMY zaune a kan sofa har sun gama break fast ɗin su, a gefe guda kuma yayyin ta ne zaune cikin shirin su na zuwa office.
Gurin su daddy ta nufa ta durƙusa har ƙasa ta gaishe su,cike da fara'a suka amsa mata,juyawa ta yi ta gaishe da yayyin ta tare da haye wa kan dining ta zauna domin ta samu ta yi break fast ɗin ta.
Bata wani ɗauki lokaci ba ta kammala break fast ɗin sabo da gudun ƙure war lokaci, miƙewa ta yi taje gefen momy ta durƙusa tare da cewa:
"MOMY na shirya zan wuce"
Ta faɗa tana sunkuyar da kanta a ƙasa.
Kallon ta MOMY ta yi tare da cewa:
"To doughter yau dai zaki fara zuwa makaranta,banda wasa da kula ƙawayen banza,karatu ne ya kai ki kuma shi zaki yi, pls bana so naji wani abin bayan wannan, Sabo da haka ki kula sosai ki maida hankalin kin ji".
Ta ƙarasa maganar tana tsare ta da idanun masu kaifi.
"In sha Allah momy zan yi yadda ki ka ce min"
"Yauwa my doughter Allah ubangiji ya yi miki Albarka".
Gyaran murya daddy ya yi ya ɗago kansa ya dube ta tare da cewa:
"Ma sha Allahu doughter na Allah ubangiji ya taimaka yasa ki fara a sa'a ya yi jagora,ban da wasa kin ji.?"
Girgiza kai ta yi tare da cewa:
"Tom daddy in sha Allah"
Yace "yauwa Allah ubangiji ya yi miki Albarka,nima yanzu zamu wuce airport farouq nake jira, sabo da ƙarfe goma dai dai jirgin mu zai tashi zuwa uk kiyi mana addu'a kunji.?".
"Toh daddy Allah ubangiji ya kai ku lafiya ya dawo da kai gida lafiya,shi kuma Allah yasa ya fara karatun sa a sa'a cikin nasara, daddy Allah ya haɗa ka da dukkanin alkhairi a tafiyar ka da dawowar ka, Allah ya kare ka daga tsau-tsayi da asara "
Gaba ɗaya parlon babu abin da suke furta wa sai Ameen Ameen Ameen.