← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 80

Sashe 57

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hmmm Nura kenan! wallahi ina jin tsoro da fargaba kar in rasa ta, saboda idan na rasa ta komai zai iya faruwa da ni!domin Allah ya jarrab ce ni da mugun son ta,shi yasa na rasa yadda zan yi da rai na!". dafa kafaɗar sa Nura ya yi tare da cewa,
"Be a man mana aboki na! kaga duk ka tashi hankalin ka har zazzaɓi mai zafi ya kama ka,ka kwantar da hankalin ka babu abinda zai faru in sha Allah"
"Hmmm Nura kenan! wallahi baza ka gane irin son da nake yiwa yarinyar nan ba!"
"Tom shikenan na ji! yanzu tashi mu tafi asibiti daga nan sai na kai ka gida ka kwanta ka huta"

Ɗago idanun sa da suka yi jawur ya yi tare da duban Nura cikin murmushin takaici ya ce,
"Babu in da zani Nura! saboda asibiti basu da maganin da za su bani!"
Ya faɗa cike da murya mai rauni kamar ya yi kuka.
"Okay tom kirawo min wayar halimatun ina so zan yi magana da ita!!"
"Tun ɗazu nake ta kiran wayar ta amma bana samu! ta kashe wayar ma gaba ɗaya! amma bari na sake kira"

Ya faɗa yana ƙara dialling numbern ta steel dai har yanzu a kashe wayar take.
Nan take hankalin sa ya ƙara tashi,ganin haka ne ya sa nura yace masa,
"Tashi muje gidan su halimatun mu sameta"
Cikin rauni ya ce,
"Kana ganin idan muka je zata saurare mu"
"Ai dolen ta ne ma ta saurare mu! kai dai tashi mu tafi"
Ya faɗa yana kama hannun sa suka miƙe a tare suka fito daga cikin office ɗin,lift suka hau ya sauke su a ƙasa, ba tare da ɓata lokaci ba suka hau haɗaɗiyar Jeep ɗin mukhtar ɗin nura ya jasu suka tafi......✍🏻✍🏻

A yi haƙuri da wannan🙏🏻

Ina matukar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi,ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa,ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi🙏🏻

Daga alƙalamin

FATIMA BINTU ABDALLAHI(UMMU AYSHA).....✍🏻✍🏻

Share fisabilillahi.🙏🏻

Game buƙatar wannan littafin tun daga farko har zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ni ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻

08162055134.

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDALLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S

ASSOCIATION)

Golden pens.......✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages___________73&74

__________basu zame a ko ina ba sai bakin get ɗin gidan su HALIMATU,horn suka yi ba maigadi ya leƙo ta ƙaramar ƙofa domin ganin mai yin horn ɗin,ganin ɗaya daga cikin motocin da mukhtar yake zuwa da su ne ya sa ya koma da sauri ya wangale musu get ɗin.
Danna hancin motar Nura ya yi cikin gidan ya yi parking ɗin motar a parking space, fitowa su ka yi tare da tsayawa a jikin motar suna kallon baba maigadi da ya nufo inda suke tsayen,yana ƙarasowa ya basu hannu suka yi musabaha cikin girmamawa.

Mukhtar ne ya kalli baba maigadi ya ce,
"Baba daddy yana nan ko ya fita.?"
Cike da girmama wa baba maigadi ya ce,
"Alhaji bayanan sun fita office tun safe gaba ɗayan su shi da yaran! hajiya ce kawai a cikin gidan".
Cikin sauri Nura ya ce,
"Halimatu bata nan ita ma??"
Girgiza kai baba mai gadi ya yi tare da cewa,
"Eh to! gaskiya yau banga fitowar ta ba gaba ɗaya ma, domin drivern da yake kai ta makaranta ma da yazo shi kaɗai naga ya tafi ba tare da ya ɗauke ta ba, gaskiya ina kyauta ta zaton ita ma ɗin tana cikin gidan,amma ku kirawo wayar ta ku ji!"
Ya ƙarasa maganar yana kallon su.
Da sauri MUKHTAR ya ce,
"Wallahi baba mun yi ta kiran wayar ta akashe bama samu! ko zaka je ka bincika mana wajen hajiya!!"
Shiru baba mai gadi ya yi na ɗan wani lokaci daga bisani kuma ya ɗago da kansa ya dube su tare da cewa,
"Toh shikenan! bari naje na duba na gani Allah ya sa suna ƙasa ,domin idan suna can saman benen nan sai ka yi ta sallama ka ji shiru"
Nura ya ce,
"Tom shikenan baba mungode"

Juyawa baba ya yi tare da cewa,
"Babu komai ƴaƴa na"
Lokacin da baba mai gadi ya iso ƙofar parlon ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama cikin sa a kuwa ya ji muryar momy da ke zaune a kan sofa ta amsa masa sallamar ta sa tare da bashi izinin shigowa,tura ƙofar ya yi a hankali tare da shiga ciki ya tsaya a bakin ƙofar, gaisawa suka yi da momy in da yake sanar mata da maganar zuwan su mukhtar wajen halimatu.
Mamaki ne ƙarara akan fuskar momy domin dai tasan in dai mukhtar zai zo yana sanarwa da halimatu zuwan na sa,domin bata gaya mata batun zuwan mukhtar ɗin ba, kasancewar basu daɗe da rabuwa da halimatun ba ta hau sama tace zata je ta kwanta kanta yana ciwo.

Ɗago kanta ta yi cike da mamaki ta dubi baba mai gadi da yake tsaye a bakin ƙofar parlon ta ce,
"Baba ka je ka ce musu su shigo daga ciki,bari na je na kirawo musu doughter ɗin".
Ta faɗa tana miƙewa tsaye tare da hayewa sama, juyawa baba maigadi ya yi ya fito daga cikin parlon ya nufi inda ya bar su mukhtar tsaye suna jiran sa, ƙarasowa ya yi kusa da su tare da cewa,
"Hajiya ta ce ku shiga daga ciki zata kirawo muku ita".
Ajiyar zuciya mukhtar ya sauke mai ƙarfi har suna jiyo sautin ta,kallon baba maigadi Nura ya yi tare da cewa,
"Mun gode sosai baba".
Murmushi ya yi tare da wucewa ya koma wajen zaman sa ya ɗakko ƴar radio ɗin sa ya kunna yana sauraren labarai.

Dafa kafaɗar sa Nura ya yi tare da cewa,
"Be a man mana mutumi na,ka kwantar da hankalin ka in sha Allahu komai zai dai-dai ta ka ji"
Cike da ƙarfin hali ya ce,
"Allah ya sa abokin na"
Kama hannun sa Nura ya yi suka nufi parlon da sallama a bakin su,shiru parlon yake babu kowa sai wani irin daddaɗan ƙamshin turare da yake tashi gauraye da sanyin ac mai ratsa jiki da ɓargo.
Jagora ya yi musu zuwa haɗaɗen parlon baƙin da idan yazo suke zama su yi hira,suna shiga suka zauna a kan sofa suna jiran fitowar ta.

A ɓangaren momy kuwa lokacin da ta shiga ɗakin halimatu kwance ta iske ta tana ta sauke ajiyar zuciya alamar ta ci kuka ta ƙoshi,zama ta yi a kan gadon tare da kamo hannun halimatun ta miƙar da ita zaune,ganin yanda idanun ta suka kumbura ya sa ta ce,
"Subhanallahi doughter wai har yanzu kukan kike yi baki dena ba! gashi har idanun ki sun fara kumbura!!"cikin marairai cewa cike da shagwaɓa tasa hannuwan ta biyu ta rungume momy tare da cewa,
"Momy ni bana son auren gaba ɗaya na fasa wallahi! shima yaya mukhtar ɗin bana son shi!!"
Ta faɗa hawaye na zubowa daga cikin idanun ta.
Wani irin faɗuwar gaba momy ta ji a karo na farko tana fargabar kar halimatu ta ɓallo musu ruwa tasa su ji kunya,cikin ƙarfin hali ta kalle ta tare da cewa,
"Ba mun yi magana da ke ɗazu ba doughter! ko so kike yi ki tayar mana da hankali ne ni da daddyn ku kisa mu ji kunya! kinga idan baban ki ya ji ba zai ji daɗi ba,kuma ai na gaya miki zai dinga kawo min ke gida kina gani na ko.?"

Girgiza kai ta yi tare da ɗago idanun ta ta kalli momy ta ce,
"To momy a bar shi sai nan da shekara uku ko huɗu mana!!"
Cike da mamaki momy ta kalle ta tare da sauke ajiyar zuciya cikin raunin murya ta ce,
"Na fuskanci so ki ke yi ki saka ni kuka ko doughter.??"
Cike da tashin hankali ta ɗago idanun ta ta kalli momy muryar ta tana rawa ta ce,
"A'a momy ki yi haƙuri ki yafe min na dena bazan ƙara ba!"
"Toh na ji in dai ba kya son nayi kuka karki ƙara faɗin haka kin ji.??"
Girgiza kanta ta yi tare da cewa,
"Na dena momy kar ki yi kuka bazan ƙara ba".
Murmushi momy ta yi mata tare da shafa kan ta tana cewa,
"Good girl, Allah ubangiji ya yi miki Albarka,tashi kije ki wanke fuskar ki ki gyara jikin ki ga mukhtar nan yazo tun ɗazu yana parlon baƙi yana jiran ki".
Girgiza kanta ta yi tare da mikewa ta shige toilet.
Ajiyar zuciya momy ta sauke tare da ficewa daga cikin ɗakin.

Bata wani jima ba a cikin toilet ɗin ta fito hannun ta riƙe da towel tana tsane ruwan dake ɗiga a fuskar ta,kujerar mirror ta jawo a hankali tare da ɗaukar lotion ɗin ta ta matso ta shafa a fuskar ta.
Powder ta ɗan shafa da lipstick, sannan ta ɗakko mascara da eye liner ta saka tare da zizara ɗan kwalli a cikin kyawawan idanun ta.
Ba ƙaramin kyau ta yi ba duk da idanun ta sun ɗan kumbura kaɗan sakamakon kukan da ta yi,tashi ta yi ta buɗe closet ɗin ta ta ɗakko black abaya ta cire kayan jikin ta ta saka ta, comb ta ɗakko ta taje dogon gashin ta mai cika tare da fesa hair spray akan gashin ta yi parking ɗin shi tare da sakin sa baya.
Body spray ta fesa masu ƙamshi haɗe da turaruka masu daɗin ƙamshi sannan ta saka black plate shoe a ƙafar ta tare da yafa mayafin abayar ta yi baya da shi gashin ta na lilo a gadon bayan ta.
Chapter 57 · 0% Book details