Sashe 2
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya k'arasa maganar yana wata iriyar dariya irin ta 'yan duniya,bakinsa yayi bak'ik'k'irin alamu sun nuna yana shaye shaye,
HALIMATU ta kalleshi ranta a b'ace tace masa "Allah ya kiyaye in aure ka!!"ya kalleta ya wani tuntsure da dariya irin ta k'auraye yace"yo in banda nid'in ma da nakeso na rufa miki asiri wazai aure ki,yanda kika girma ɗinnan kika yi kwantai,duk sa'anninki sun yi aure sun barki,
sannan duk garin nan babu wanda ya taba cewa yana sonki idan bani ɗinnan ba,ko ni ɗinma wallahi rufa miki asiri zanyi"ya ƙare maganar yana dariya.
HALIMATU ta zagaya tabi ta gefensa tayi wucewarta ta barshi tsaye a gurin yanata wata iriyar dariya.
tana yin sallama ta iske inna laure zaune a tsakar gida,suna cin kwad'on zogale ita da 'yarta hanne,hanne k'anwar HALIMATU ce,shekara biyu HALIMATU ta bata.
"HALIMATU ta tsuguna tace inna na dawo!"inna laure ta wani d'aure fuska tace "ai naganki"ta mik'a mata hannu tace"bani kuɗin cinikin!!"HALIMATU ta mik'o mata kuɗin,hannun inna laure yana rawa tayi sauri ta karɓe kuɗin tana faɗin "ashe yau ɗan albarkar nan yazo" ta faɗa fuskarta cike da fara'a.
ta d'ago ta kalli HALIMATU tace"to kokefa ai kinga hakan yafi,ina fatan dai bakiyi masa rashin mutuncin naki ba"
HALIMATU dai tayi shiru batace komai ba.inna laure tace" ni kinga tashi kibani waje kinzo kin wani tsare ni da waɗannan mayun idanun naki"hanne tace"haba inna wai me yasa kike yiwa yaya HALIMATU hakane duk ƙoƙarin da take yi miki amma meyasa bakya ganine yanzu fa ta dawo daga tallan gyad'a amma ko hutawa batayi,ko abinci fa baki bata ba,amma kin hauta da faɗa,gaskiya nidai inna bana son haka" ta ƙarasa maganar cikin faɗa.
Inna laure tace "to uwata ai saiki dakeni!!tunda na yiwa ƙanwar uwarki faɗa,to da kike cewa ban bata abinci ba cewa nayi bazan bata baneba!!? ta ƙarasa maganar ta mik'e a fusace ta shiga d'aki ta d'akko wata roba mai ɗauke da ragowar ɗumamen safe ta dan gwara mata ita a gaban ta.HALIMATU ta saka hannu ta ɗauka ta koma can k'ofar d'akinta ta ajiye,taje ta d'ebi ruwa a randa ta wanke hannun ta, ta zauna tayi bismillah ta fara cin tuwo.bayan ta gama cin tuwon ta ɗauke robar taje ta d'ebi ruwa a randa tasha ta wanke hannun ta,ta d'auraye robar ta kife a cikin kwandon da suke kife kwanika.
tana shirin shiga d'akinta taji ana sallama,cikin sauri ta d'aga kanta domin ganin mai yin sallamar,ai da gudu ta tafi cike da murna ta rungume ta, tana mai fashewa da kukan murna....................✍🏻
💝💞 HALIMATU 💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞
Story & writing
By
FATIMA BINTU ABDALLAHI (UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITERS ASSOCIATION)
Golden pens...............✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pg__________________3&4
Ta rungume ta tana kukan murnar ganin ta,hajiya maryam tace"to kuma kukan na mene ne?? daga gani na kuma sai ki saka min kuka?? haba HALIMATU kodai baki yi murnar gani na bane in koma??"HALIMATU ta ƙara rungume ta sosai tana sauke ajiyar zuciya tace"momy wallahi kukan duk na murnar ganin ki ne,kin yi min suprise saboda ban yi tsamma nin ganin ki ba".
Ta ƙare maganar hawayen farin ciki na zubuwa daga kyakkyawar fuskarta.
Cikin farin ciki hajiya maryam ta ƙara rungume ta sosai a jikin ta,tana shafa bayan ta alamar rarrashi ,ta ɗago da fuskar ta,ta zuba mata idanu tana ƙare mata kallo saboda ganin irin ramar da tayi duk ta zabge, alamar tana cikin wahalar rayuwa tace" I'm sorry my daughter ai gani nan yanzu tare da ke,kuma in sha Allahu da ke zan koma, saboda na gaji wallahi ha'kurina ya ƙare,sai dai duk abinda za'ayi sai dai ayi,amma wannan karon da ke zan koma in sha Allah".
*************************
Cikin tsananin farin ciki HALIMATU ta ƙara rungume ta,ta kamo hannun ta suka ƙarasa shigowa cikin gidan.
ganin babu kowa a tsakar gidan yasa hajiya maryam ta ɗago ta kalli HALIMATU tace "ya kuma naji gidan shiru??ko babu kowane sai ke kaɗai??"
HALIMATU tace mata "a'a momy bani kaɗai bace a gidan,nida inna laure ne,tana nan a cikin d'akin ta,bari na sanar mata da zuwan ki.
Kafin HALIMATU ta ƙarshe maganar da takeyi inna laure ta ɗaga labulen d'akin ta,ta le'ko da kanta waje tana cewa "wai wanene yake ta faman kwad'a mini sallama ne kamar ana bina bashi".ta ƙarasa maganar tana mai ɗora idanun ta akan hajiya maryam,nan take taji gabanta yayi mugun fad'uwa,saboda bata yi tsammanin ganin hajiya maryam a wannan lokacin ba ..
*************************
Hajiya maryam tace"sannu laure,da fatan na sameku lafiya".
Mu'kut inna laure ta haɗiye yawun da ya tsaya mata a ma'koshi, saboda ta san hajiya marya bata ɗaukan rainin wayon ta,da 'kyar ta iya buɗe baki ta gyara yanayin fuskarta,saboda kada ta fahimci wani abu tace"lafiya k'alau Maryam"daga haka bata ƙara cewa komai ba,ta saki labulen d'akin ta, ta mi'ke
tsaye tana ta safa da marwa a cikin dakin.
Hajiya maryam ta tab'e baki ta kalli HALIMATU da kanta yake ƙasa tace"daughter mu shiga daga cikin d'akin,domin na gaji ina son na huta.
HALIMATU tayi gaba Hajiya Maryam tana biye da ita har cikin d'akin ta,wanda ada shine a matsayin d'akin mahaifiyarta. Sai da ta gama ƙarewa d'akin kallo, sannan ta kai duba inda HALIMATU takar kad'e mata tabarma ta shimfid'a mata sannan ta kawo wata tsohuwar dadduma ta shimfid'a mata akai ta zauna.
HALIMATU ta fito tsakar gidan, taje bakin randa ta d'ebo mata ruwa mai sanyi a cikin kofin silba,tazo ta dur'kusa a gabanta ta ajiye mata ruwan tace"ga ruwa momy ki sha,ya gajiyar hanya?? dafatan kinzo lafiya".
Tace"lafiya k'alau Alhmdllhi HALIMATU da fatan na sameku lafiya".
Ta ƙarshe maganar tana mai ɗaukan ruwan tana sha.
"Momy ina su Mahmud , Sadiq farouq da auta yusra??"hajiya maryam tace" duk sunce a gaisheki".
Murmushi HALIMATU tayi mai 'kayatarwa tace "nima ina amsawa".
Ajiyar zuciya hajiya maryam ta sauke ta dubi HALIMATU tace"dama na kuma dawowa ne akan naganar mu, har yanzu ina nan akan baka na,na ɗaukan ki na tafi da ke,shiyasa nazo a daidai lokacin da kika kammala makarantar ki.
Dama tuntuni naso tafiya da ke,tun bayan rasuwar mahaifiyar ki,amma muguwar matar nan ta zuge mahaifin ki ya 'ke ƙasa ƙasa ya hana ni tafi dake,nayi nayi ya bani ke,amma fafur ya hanani ke,
dole na ha'kura na koma gida ba'a son raina ba,
amma wallahi yanzu ko yana so ko baya so sai na tafi da ke, ƙafata ƙafarki".
ta ƙare maganar zuciyar ta tana mata ƙuna".
HALIMATU ta ɗago da fuskar ta , idanun ta cike taf da ƙwalla tace"dan Allah momy karki ƙara tafiya ki barni, wallahi inna aure zata yimin da da buba,tace sai ta aura min shi ko ina so ko bana so,kuma gashi baba ya kasa hana ta.buba bashida wani aiki sai shaye shaye da lalata yaran mutane da har kar daba, sannan kowa tsoron shi yake ji a garin nan an zuba masa ido an kasa tsawatar masa,shine take so ta aura min shi"ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.
Cikin sauri hajiya maryam ta jawo ta jikin ta, ta rungume ta tana share mata hawayen da yake gangarowa a kan fuskar ta.
tace"share hawayen ki,babu wanda ya isa yayi miki auran dole indai ina raye da ikon Allah,har yaushe ma kika isa auran??duka duka fa shekarar ki goma sha shida fa,amma shine don rashin imani akeso a kassara miki rayuwa,to wlh bazata yiwu ba".ta ƙarasa maganar tana rarrashin ta .
Sai da taga HALIMATU ta samu nutsuwa, sannan ta jawo jakar da ta shigo da ita,tare da wata leda babba,ta buɗe cikin ladar ta fito da take a way guda biyu da lemo da ruwa,ta ɗauki take a way guda ɗaya da lemo ɗaya da ruwa guda ɗaya ta mi'kawa HALIMATU tace"maza karb'i kici, dan na san ba wani abincin kirki kike samu ba".
Cike da ladabi HALIMATU ta mi'ko hannu ta karb'a tana godiya,ta gyara zamanta ta buɗe take a way ɗin.
Fried rice ce da coleslaw da naman kaza,tayi bismillah ta fara cin abincin cikin farin ciki da annashiwa.itama Hajiya Maryam nata abincin ta fara ci.
Bayan sun kammala cin abincin ne hajiya maryam take tambayar ta ko mahaifin ta malam ummaru yana nan?
HALIMATU tace"baya nan momy,amma yau satin sa ɗaya da tafiya,kuma in sha Allah u yau zai dawo"momy tace"ma sha Allah,gaskiya naji daɗi da nazo akan lokaci, Allah ya kawo shi lafiya"
Ta amsa mata da amin.
*************************
A ɓangare inna laure kuwa tunda ta koma cikin ɗaki ta kasa zaune ta kasa tsaye,ta sa'ka wannan ta kwance wannan,ta rasa mai yake mata daɗi.
Tana ganin indai ba tayi da gaske ba to lallai matar nan tafiya zatayi da HALIMATU,ita kuwa ina zata bari a tafi da HALIMATU,yarinyar da take ɗorawa talla take samo mata kuɗi,gaskiya da sake.
ga mutumin nan da yake siye gyad'ar gaba ɗaya ya bata ma'kudan kuɗi,sannan kuma ace za'a tafi da ita, ina ai dole na san yanda zanyi na hana wannan matar tafiya da ita.
Ita bata damu ba,kome mutumin nan zai dinga yiwa HALIMATU indai zai bata kuɗi to bata da damuwa,ta sauke ajiyar zuciya,ita ba wannan ba ma, yanzu yaya zatayi da buba,bayan ta yi ta karb'an kuɗi a hannunsa,saboda tayi masa alƙawari zata aura masa HALIMATU, kuma tasan buba ba ƙaramin tijararre bane,muddin bata aura masa HALIMATU ba,to wallahi kashin ta ya bushe,domin ta san ba zai taba gyale ta ba.
gashi ta riga tayi masa alƙawari,ta kuma san halin buba sarai ba shida mutumci,duk garin nan babu ga gararre kamarsa,gashi bashida mutunci kwata kwata.
A yanda yake son HALIMATU zai iyayin komai idan bata aura masa ita ba.
to ita yanzu ya zatayi,ina ma taga kuɗin da zata biya buba kudinsa,lallai dole tayi wani abu akai.
ta sauke ka'k'karfar a jiyar zuciya,duk wannan zancen a cikin zuciyar ta takeyinsa.
Tana cikin sa'ka da warwara ne hanne ta shigo cikin d'akin bakin ta ɗauke da sallama,ta ɗago ta dubi inna laure wadda tayi nisa a duniyar tunani,sam bataji motsin shigowar hanne ba.
hanne ta matso kusa da ita ta saka hannu ta girgiza ta,a firgice ta ɗago kai ta dubi hanne da ke riƙe da kafad'ar ta ce" yaushe kika shigo??"