Sashe 56
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy ya ce,
"Haba mar'atussalaha ta,wai har yanzu baki saki ranki ba akan batun auren nan! kiyi haƙuri mana mu yi mata addu'a Allah ya sa hakan shi yafi zama alkhairi a rayuwar ta!"
Da ƙyar ta amsa da"ameen"
"Yauwwa my happines haka nake so na ji,yanzu kinga visa ɗinku ta fito, nan da kwana biyu zaku tafi Dubai da China, idan kuka gama siyayyar duk abin da kuke so daga nan sai ku wuce saudia ku yi umara ko.?"
Girgiza masa kai ta yi tare da cewa "toh"
"Allah ubangiji ya yi miki Albarka,shi yasa nake ƙara son ki a koda yaushe ƴar kyakkyawar mata ta"
Murmushi ta yi tare da kai masa dukan wasa a ƙirjin sa,hannu ya sa ya rungume ta sosai a ƙirjinsa tare da haɗe bakinsa da nata...✍🏻✍🏻
Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni,ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa,ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi🙏🏻🙏🏻
Daga alƙalamin
FATIMA BINTU(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻
Game buƙatar wannan littafin tun daga farko zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ni ta wannan numbern wayar 👇🏻👇🏻
08162055134.
Share fisabilillahi.
💝💞 HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA).....✍🏻✍🏻
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens......✍🏻✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages____________71&72
_____________washe gari bayan sun yi break fast momy ta zaunar da ita ta fara yi mata nasiha mai ratsa jiki da ɓargo,sai da taga jikin ta ya yi sanyi sosai sannan ta sako mata magar auren su ita da mukhtar tare da gaya mata lokacin da aka saka na auren na su.
Ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba da jin wannan labarin,dama abinda momy take jiyewa kenan shi ya sa taƙi ta faɗa mata maganar auren,kamo hannun ta ta yi ta jayota jikinta ta rungume ta tare da shafa bayan ta alamar rarrashi.
Da ƙyar ta samu ta rarashe ta ta yi shiru,ɗago kan ta ta yi ta dubi momy tare da cewa,
"Yanzu momy shikenan aure za ku yi min, za a ɗauke ni daga gidan nan a kai ni wani gidan da bansan kowa ba,kuma bazan dinga ganin ki ba kullum.?"
Ta faɗa hawaye na zubowa daga cikin idanun ta,hannu momy ta sa ta goge mata hawayen tare da cewa,
"To ya zamu yi doughter haka baban ki ya ce,kinga kuma babu dama mu ce masa a'a saboda ya ce yafi so kiyi aure tunda ƙuruciyar ki, saboda haka ne ma ya haɗe auren naku keda ƴaruwar ki HANNE, saboda haka kiyi haƙuri doughter ki bar kukan nan haka kar ya samiki ciwon kai kin ji,ki kwantar min da hankalin ki nima ko na samu hankali na ya kwanta, shi aure da kike gani ibada ce babba,kuma ko ba yanzu ba dole watarana ki kiyi aure ki tafi ɗakin mijinki kinji.? sabo da haka ki kwantar da hankalin ki duk lokacin da kike son gani na zaki ganni kin ji.?"
Jin jina kai ta yi tare da cewa,
"Toh amma momy na yi ƙarama da yawa fa!"
Maganarta ce taso ta bawa momy dariya,lallai har yanzu akwai ƙuriciya a tare da ita.
"Karki damu doughter ba komai in sha Allahu kin ji,babu abinda zai faru sai alkhairi kin ji ko.?"
"To momy"
"Yauwwa good girl ko ke fa"
Momy ta faɗa tana mata Murmushi,murmushin ita ma ta yi tare da ƙara rungume momy.
Kiran sunan ta momy ta yi a hankali tare da cewa,
"Gobe idan Allah ya kaimu zamu tafi Dubai zamu je mu yi siyayya,daga nan zamu je Chaina nan ma mu yi siyayya idan mun gama zamu wuce saudia muje mu yi Umrah, Sabo da haka ki shirya kayan ki zuwa an jima kin ji ko.??"
"To momy in sha Allah"
"Yauwa my lovely daughter, Allah ubangiji ya yi miki Albarka"
Ta faɗa tare da manna mata kiss a goshin ta.
Murmushi ta yi tare da miƙewa tsaye tace,
"Momy bari naje na ɗan kwanta kai na yana yi min ciwo"
Ayya sorry doughter kin ji,make sure kafin ki kwanta ki sha paracetamol kin ji"
"To momy"
Ta faɗa tare da miƙewa tsaye ta haye up stairs.
Tana shiga cikin bedroom ɗin nata ta zauna a gefen gado tare da jawo bedside drawer ta ɓalli paracetamol guda biyu ta mayar cikin drower ɗin tare da rufe wa,miƙewa ta yi ta je gaban fridge ta buɗe ta ɗauki ruwa mara sanyi sosai ta sha maganin da shi.
Gadon ta koma ta kwanta tare da jayo bargo ta rufe ƙafafun ta da shi,ko five minutes bata yi da kwanciyar ba ta ji wayarta da ke kan bedside drawer na ringing alamar kira ya shigo.
Hannu ta ta miƙa ta ɗakko wayar domin ta san me kiran sabo da ringing tone ɗin da ta saka masa,sai da wayar ta tsinke wani kiran ya sake shigowa a karo na biyu ya kusan katse wa sannan ta yi picking call ɗin.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa,
"Ina ki ka shiga ne tun ɗazu ina ta kiran wayar ki baki ɗauka ba.??"
Shiru ta yi bata amsa masa ba,shirun da ya ji ne ya sa ya ciro wayar daga kunnen sa domin ya yi zaton yi ko wayar ta tsinke ne,cike da mamaki yake kallon wayar domin bata tsinke ba, kuma alamu sun nuna tana jin sa shiru kawai ta yi masa ta ƙyale shi.
Mayar da wayar ya yi ya ɗora ta a kunnen sa tare da cewa,
"My love, kina jina ki ka yi shiru kika ƙyale ni"
Steel dai har yanzu bata yi maganar ba.
Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi har tana jiyo sautin ta.
"My love, so ki ke yi in yi miki kuka ne.??".
Steel nan ma dai shiru babu amsa.
Cike da tashin hankali ya ce,
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!! my love so kike yi zuciya ta ta buga ya mutu ne ki huta.??"
Fashe masa ta yi da kuka kamar wadda a ka daka,shiru ya yi yana sauraron kukan nata kamar ana watsa masa tafasashen ruwan zafi a cikin zuciyar sa,nan take jikin sa ya kama rawa kamar mazari hankalin sa ya tashi sosai.
Buɗe baki ya yi daƙyar muryar sa cike da rauni ya ce,
"Me ya same ki my love.?, wa ya taɓa min ke.?,gaya min kin ji.??"
Duk a lokaci ɗaya ya jera mata tambayoyin.
Cikin kuka ta ce,
"Bana son ka!! kuma na fasa auren bazan aure ka ba!!"
Dum Dum Dum ya ji gaban sa ya yi masifar faɗuwa.
Muryar sa na rawa ya ce,
"Me yake faruwa my love.? me na yi miki ne??"
Cikin kuka ta ce,
"Ni wallahi banason na yi aure yanzu sai nan da shekara uku!! idan kuma ba haka ba wallahi na fasa auren ka!!"
Wani irin gumi ne mai zafi ya shiga kwaranyo masa tun daga goshin sa har izuwa tafin ƙafarsa,gaba ɗaya ji ya yi zuciyar sa ta yi masa wani irin nauyi kamar an aza masa ƙaton dutse a kanta,nan take duk wata huda da take cikin jikin sa ta shiga tsatstsafo da gumi mai zafi,gashin jikin sa duk suka miƙe ya rasa in da zai saka kansa ya ji daɗ,babu abin da yake fitowa daga bakin sa sai huci.
Cikin wata iriyar murya mai mugun rauni ya ce,
"Kiyi haƙuri my love haka iyayen mu suka zartar da hukuncin nan, yadda kika ji labari nima haka naji wallahi! dan Allah ki yi haƙuri mu yiwa iyayen mu biyayya kin ji my love, wallahi ina mutuƙar sonki da ƙaunarki,kuma in sha Allahu zan riƙe ki amana sosai da gaske har ƙarshen rayuwa ta ,zaki ji daɗin zama da ni sosai kin ji!"
Kuma fashe masa da kuka ta yi tare da cewa,
Ni wallahi bana so!kawai a fasa auren yanzu, idan kuma ba haka ba zan fasa auren ka gaba ɗaya wallahi"
Tana kaiwa nan ta kashe wayar.
Kiran ta ya kuma yi taƙi ɗaukar wayar,sai da ya yi mata kira shida amma bata ɗauka ba,daga ƙarshe ma kashe wayar ta yi gaba ɗayan ta.
Wani irin shiɗewa ya yi,nan take ya kama yin wata iriyar shaƙuwa babu ƙaƙƙautawa,a daddafe ya tashi ya buɗe fridge ɗin da yake cikin office ɗin sa ya ɗakko ruwa mara sanyi sosai ya buɗe ya kafa bakin sa ya fara kwankwaɗa har yana ƙwarewa,sai da ya shanye ruwan gaba ɗaya sannan ya yi jifa da gorar gefe.
Komawa ya yi kan kujera ya zauna saboda wani irin masifaffen ciwon kai da jiri da yake ji,nan take zazzafan zazzaɓi ya kama shi jikin shi babu abinda yake yi sai rawa.
Cikin ƙarfin hali ya jawo wayar sa ya yi dialling numbern wayar Nura tare da ce masa ya same shi a office ɗin sa yanzu.
Cikin minti uku Nura ya iso office ɗin cike da fargaba domin tun a waya ya ji muryar ta sa sai a hankali,yanayin da ya same shi a ciki ne ya ɗaga masa hankali sosai! nan take ya ce masa,
"Dama baka da lafiya ne sosai haka kuma ka fito office.? ta shi maza mu tafi asibiti!!?"
Cike da dauriya ya ce,
"Ciwo na bana asibiti bane Nura! idan ban sameta komai zai iya faruwa da Ni!!"
Kallon sa Nura ya yi cike da mamaki hankali tashe ya ce,
Me kake nufi ne.? nifa ban gane ba dan Allah ka yi min bayani!"
Cikin ƙarfin hali ya buɗe baki da ƙyar ya bawa Nura labarin duk yadda suka yi da halimatu.
Cike da ɓacin rai Nura yace,
"Ita ta isa tace bazata aure ka ba! kuma maganar a ɗaga biki ma ai bata taso ba, domin babu abin da za a fasa kuma dolen ta ta aure ka!!"