← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 80

Sashe 64

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ya kasan ce biki saura kwana huɗu,a yau ɗin ne kuma aka tafi yi wa amaren jere a gidajen su, daddy ya yi ƙoƙari sosai da sosai in da ya yiwa halimatu kayan ɗaki masu tsadar gaske sosai set uku kujeru set biyu sai kuma dinning table mai kyau,ya yin da momy ta yi mata kayan kitchen na gani na faɗa.duk da cewar mukhtar ya zuba wasu amma haka aka ƙara loda mata wasu.
Sannan ta saka aka yi mata turarurruka na ƴan mai dugurin asali masu bala'in ƙamshi da kama jikin mutum sosai,abin dai sai wanda ya gani gida ya yi kyau sosai gwanin ban sha'awa.

Ita ma HANNE an yi mata jeran ta a gidan da sama'ila ya kama musu,baba ya yi mata kayan ɗaki na waje masu kyau da tsada,ita kuma aunty amina ta yi mata kayan kitchen, gida ya yi kyau ma sha Allah.
Yau ya kasan ce bikin su halimatu saura kwana uku kuma a yau ɗin ne aka fara bikin,in da aka shirya musu haɗaɗɗen kamu ita da HANNE a gidan baban su halimatun,ƙwararriyar make-up artist momy ta ɗakko ta zuba musu kwalliya mai kyau da tsari,wani irin maroon colour da golden ɗin lace mai shegen kyau da tsada halimatu ta saka,an yi masa ɗin kin doguwar riga mai kyau sosai,gashi ɗinkin ya zauna a jikinta sosai tare da bin shafe ɗin jikin ta,ya yi mata bala'in kyau sosai abin ka da farar mace,takalmi da ƴar pos ɗin ta kalar kayan jikin ta, sai babban net da aka rufe musu jiki da shi, ita ma HANNE kayan da aunty AMINA da baba suka ɗinka mata su ta saka.

Sun yi kyau sosai kamar ka sace su ka gugu musamman ma halimatu.ba bu abin da yake ta shi a jikin su sai daddaɗan ƙamshin turaruka masu sanyaya zuciya.
Ba tare da ɓata lokaci ba motoci suka kwashi amaren da ƴan biki zuwa wajen kamu,an tsara gurin sosai an yi masa decoration mai kyau da tsari,gurin ya yi kyau sosai ga mutane nan sun cika wajen sosai.

Lokacin da amaren suka ƙaraso gurin kamun take guri ya kaure da shewa da guɗa,nan take aka fara gudanar da kiɗan ƙwarya aka saka amare a tsakiya ana yi musu liƙi,masu pictures da masu video na ta faman aikin ɗaukar su ,sai da aka raƙashe aka chashe sannan dan gin ango suka biya kuɗin kamu dubu ɗari biyu sannan aka kama halimatu,babu abin da take yi sai kuka.
Ƙarfe tara na dare taro ya tashi.

Washe gari kuma da misalin ƙarfe goma goma na safe dubban mutane suka shai da ɗaurin auren

MUKHTAR AWWAL MAI
MAI GOLD.

Da

HALIMATU UMAR SANI.

HAFIZ IBRAHIM ADAM

Da

AMINA AWWAL MAI
GOLD.

SAMA'ILA YUNUSA
DAUDA

Da

HANNATU UMAR SANI.

An ɗaura auren a kan sadaki dubu ɗari bibbiyu,yayin da na hanne kuma ya kasance dubu hamsin.ɗaurin auren ya samu halartar dubban manyan mutane waɗanda ake ji da su a ƙasar,
Sai dai muce Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya.

A cikin gida kuwa zazzaɓi ne ya rufe halimatu ruf,da ƙyar momy ta tilas ta mata ta tashi ta yi wanka ta sha magani da tea, sannan me make up tazo ta tsantsara mata kwalliya mai kyau da burgewa,farar shadda ce ta saka wadda aka yiwa wani irin adon aiki da golden ɗin zare, ɗinkin ya yi kyau sosai ya sha ai ki,domin anko suka yi ita da mukhtar ɗin ta,ɗauri aka naɗa mata mai kyau irin mai fitar da gashin mutum ɗin nan,nan take gyararren dogon gashin ta ya bayyan har gadon bayan ta.

Muktar ne ya ƙaraso gaisuwar iyaye shida abokanan sa,da ƙyar aka samu halimatu ta fito domin ayi musu hotuna,kama hannun ta ya yi ya rungume ta a jikin sa,a haka aka yi ta ɗaukar su hotuna masu kyau shi da ita da kuma sauran mutane.
Ƙarfe 12 na rana zuwa ƙarfe huɗu aka gudanar da yinin biki,ya yin da aka gudanar da walima ƙarfe huɗu zuwa shida na maraice,malamai daban daban sun yi lecture mai ratsa jikin amare sosai har sai da ya kai su da yin kuka,anci ansha an kuma raba kyaututtuka daban daban gwanin ban sha'awa,daga bisani kuma taro ya tashi kowa ya koma gidansa lafiya.

Ƙarfe takwas na dare yawan cin mutane sun hallara a wajen da za'a gabatar da dinner,saboda ƙarfe tara na dare za'a fara, HAFIZ ne ya shigo ɗakin momy ya sha wata arniyar shadda mai kyau light blue wadda aka tsatsara mata aiki mai kyau har da babbar riga da ka gan ta ka san kuɗi sun yi kuka sosai,duk in da ya gitta ƙamshi ne kawai yake tashi a jikin sa.

Kusa da momy ya zo ya zauna fuskarsa cike da fara'a ya ce,
"Momy har yanzu baku shirya ba lokaci fa yana ƙurewa,ga mutane chan sun taru suna ta faman jiran mu, ga kuma mukhtar can a waje yana jiran halimatu tun ɗazu,nima yanzu zanje na ɗauki MEENA mu tafi"
Kallon sa momy ta yi tare da cewa,
"Muma mun gama shiryawa yanzu zamu wuce ni da sadiq da sauran mutane,ita kuma doughter yanzu zata fito su tafi domin Salma da ƙawayen su tun ɗazu duk sun tafi".

Miƙewa ya yi tare da cewa,
"Toh ni dai na tafi sai kun taho"
"Allah ya tsare muma gamu nan tafe in sha Allah"
Daga haka ya miƙe ya fice daga cikin ɗakin.
Atine ce ta fito hannun ta riƙe da halimatu da aka rufe mata fuskar ta da wani irin haɗaɗen net,buɗe fuskar ta momy ta yi tare da cewa,
"Ma sha Allah doughter kin yi kyau sosai, Allah ubangiji ya tsare min ke daga sharrin maƙiya da mahassada".
Murmushi halimatu ta yi tare da rungume momy ƙwalla na taruwa a cikin idanun ta.

Ta yi masifar kyau kamar ka sace ta ka gudu,ta saka wata iriyar haɗaɗɗiyar gown royal blue colour an yi mata ado da ratsin silver tana ja da ƙasa,takalmi da ƴar pos ɗin ta duk siver ne,ya yin da net ɗin da aka rufe mata fuskar ta da shi ya kasance da silver da adon royal blue a jiki,head ɗin kan ta ma mai adon siver da royal blue ne.
Sarƙa da awar waro da zobe da ɗan kunne da sarƙar ƙafa duk silver ne,gashin kanta ma sai da aka yi masa wani irin ado mai jan hankali aka saka masa stones da sarƙa duk silver,gaba ɗaya jikin ta walwali yake yi,ta haɗu ta ko ina kamar wadda aka canja ta.

Rufe mata fuskar ta momy ta yi tare da cewa altine ta fita da ita waje mijinta yana nan yana jiran ta za su tafi,kama hannun ta ta yi suka sakko ƙasa suka fita daga cikin parlon,a parking space suka samu wata danƙareriyar jeep black colour sabuwa dal sai ƙyalli ta ke yi , Nura ne ya fito daga gaban motar shi da wani abokin su sulaiman suka gaishe da altine tare da buɗe wa halimatu ƙofa.
Shigewa ta yi cikin motar a hankali kamar mai jin tsoron wani abu ta samu guri ta zauna a takure,rufe motar Nura ya yi tare da cewa sulaiman abokin su ya ɗauki su altine a motar sa su taho shi kuma ya buɗe gaban motar su mukhtar ya shiga domin shi ne zai tuƙa su.

Wani irin sanyi da ƙamshi ne yake tashi a cikin motar ga ƙira'ar shekh sudais da take tashi a cikin motar.
Kallon halimatu mukhtar ya yi tun daga kan ƙafafuwan ta har i zuwa saman kan ta,wata iriyar gawurtacciyar ajiyar zuciya ya sauke! nan take ya cije leɓen sa na ƙasa kamar zai huda shi,cikin sauri ta ɗaga kan ta domin ba ta yi zaton akwai mutum a kusa da ita ba...✍🏻✍🏻

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi,ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin Alkhairin sa ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi.🙏🏻🙏🏻

Daga alƙalamin
FATIMA BINTU ABDALLAHI(UMMU AYSHA)...✍🏻✍🏻

Share fisabilillahi.

Ga me buƙatar littafin HALIMATU tun daga farko zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻

08162055134.

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens...✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2014 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages___________83&84

___________Cikin sauri ta ɗago kanta tare da juyawa domin ba ta yi tsammanin akwai mutum a kusa da ita ba, gani ta yi ya kafe ta da idanunsa masu kaifi kamar ya samu television yana kallo,da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da cewa,
"Ina wuni!"
Hannu ya ɗora a saman kwantaccen sajen fuskar sa ya shafo cike da nishaɗi ya ce,
"Sai yanzu aka kula da ni.??"
Cikin sanyin murya kamar mai shirin yin kuka tace,
"Ka yi haƙuri ban san kana cikin motar ba".

Murmushi ya yi tare da matsowa kusa da ita ya saka hannayen sa guda biyu ya jawo ta cikin jikin sa sosai har suna jin ɗumin saukar numfashin junan su,wani irin sanyi ya ji ya ratsa shi tun daga kan ɗan yatsar ƙafar sa har zuwa cikin ƙoƙon zuciyarsa,nan take ya sauke wata iriyar ajiyar zuciya yana ƙara rungume ta a jikin sa kamar yana jin tsoron wani zai ƙwace masa ita.
Nan take jikin ta ya kama rawa kamar mazari,sabo da sabon yana yin da bata taɓa jin sa a tattare da ita ba, cikin sauri ta yi ƙoƙarin raba jikinsa da nata amma kuma yaƙi yadda ya bata haɗin kai,hannu sa ya saka ya tallabo fuskar ta yana ƙare mata kallo kamar ya lashe ta sabo da tsananin son da yake yi mata,nan take ta yi sauri ta runtse idanun ta dan gaba ɗaya yau ɗin nan wani irin tsoron sa take ji.
Chapter 64 · 0% Book details