Sashe 48
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta yi rashin mutunci sosai tare da taka duk wanda taso sabo da tana auren mai kuɗi,shi kan sa mijin nata ma bata ƙyale shi ba ruwan rashin mutunci take zuba masa,sabo da tana ganin dai-dai take da shi ta fi ƙarfin ta yi masa biyayya a matsayin matar sa ta sunnah,bai isa ya ya saka ta abu ta yi masa ba,haka nan bai isa ya hana ta abu ta hanu ba, kullum cikin baƙanta masa rai take yi.
Hatta da iyayen sa suma bata raga musu ba,basu da mutun ci da kima a idanun ta,ta mai da su ba'a bakin komai ba,sabo da tana ganin ta mallake ɗan su sai yadda ta yi da shi.
Ko gaishe su bata zuwa ta yi,haka nan idan suka zo ko kallon arziƙi basa samu daga gare ta balle su saka ran zasu samu ko da arziƙin ruwan sha ne.
Haka nan ƴaƴen da ta haifa a cikin cikin ta bata da lokacin su sai dai masu aiki su yi ta ɗawainiya da su,a cewar ta ita baza ta iya wannan wahalar ba ta tsofe a banza da wofi,sai gashi dare ɗaya Allah ya nuna mata ikon sa a kan ta.
Taƙamar da take yi da gadara yau an wayi gari babu ita! haka nan dukiyar da ta mallaka take ta ƙama da ita yanzu babu ita duk ta ƙare wajen siyan magani sai ɗan abin da ba'a rasa bane ya yi saura.
Uwa uba auren mai kuɗin da take taƙama da shi yau babu shi akan ta! mijin ya suɓuce mata! ta yi biyu babu! babu wan babu ƙanin ta tashi a tutar babu!!.
Hakan kuma duk ya faru ne a sanadiyyar iyayen ƙwarai da bata samu ba,basu bata tarbiyyar ƙwarai ba,sun nuna mata ta yi duk abin da taga dama shine dai-dai.
Duk abin da take so shi suke mata ko da kuwa ya saɓawa hukun cin ubangiji, ibada bata dame ta ba kuma babu mai tsawatar mata gudun kar a ɓata mata rai,duk abin da take so sai sun nemo mata shi sun mallaka mata shi ta ƙarfi da ya ji ko da za su kau ce hanya ne.
Haka zalika zata ƙunta tawa mijin ta ta yi masa rashin mutunci amma idan abun ya dame shi ya kai ƙarar ta gurin iyayen ta sai su rufe idon su su ci masa mutun ci su kuma goyi bayan ƴarsu,yanzu gashi an wayi gari daga ita ɗin har iyayen nata sun zama abin tausayi,gaba ɗayan su sun afka ramin dana sani da nadama.
Wasu hawaye ne masu masifar zafi da raɗaɗi ne suka gangaro mata ta gefen idanun ta zuwa cikin kunnen ta,ji take yi kamar zuciyar ta zata kama da wuta sabo da zafi da raɗaɗin da take ji yana fitowa daga cikin ta.
Note( ƙalubale gareku iyaye! ku sani ƴaƴayen mu amana ce a garemu kuma,kuma tabbas zai tambaye mu game da yanda muka tarbiyyan taddasu, sannan mu saka idanun mu akan ƴaƴaƴen mu domin mu gano dawaƴen ne mutane ƴaƴayen mu suke mu'amala.mu basu tarbiyyar ƙwarai irin wadda Allah da manzon sa suka koyar da mu, sannan mu dinga jasu a cikin jikin mu ta haka ne za muji dukkan wani abu da yake damun su,mu sani idan muka basu tarbiyya mai kyau tabbas bamu kaɗai zamu amfana da su ba al'ummar musulmi suma za su amfana da su).
Ta kowa ya yi a hankali yana dogara sandar sa ya ƙaraso cikin ɗakin,zama ya yi a gefen katifar da take kwance tare da saka hannu ya goge mata ya hawayen da yake zuba a gefen fuskar ta.
Juyo da fuskar ta tayi dai-dai sai tin fuskar sa yadda zata ji daɗin kallon sa da kyau,motsin buɗe ƙofa suka ji,hakan ya sa suka kai kallon su gurin domin ganin mai shigowa.
Hajiya Hauwa ce ta shigo Aminu yana biye da ita a baya,waje ta samu ta zauna a ɗaya gefen katifar,ya yin da Aminu ya zauna a kan sofa.
Shiru ɗakin ya yi kamar ba ɗan Adam mai rai a cikin sa,daga bisani Alhaji USAMA ya katse shirun tare da cewa:
"Alhamdulillah, Allah ubangiji ya ƙaddara zan dawo cikin iyalina bayan jarrabawar rayuwar da ta same mu nida marigayi amini na alhaji Garba, wannan ya zama babbar izina ce da Allah ya nuna min.
"Sannan Allah ubangiji ya nufeni da alkhairi shi ya sa ya jarrab ce ni da wannan jarrabawar ni da ƴata,mun tafi wajen ƙulla sharri da mugun ta haɗi da zalunci,amma da yake mutanen da muka yi nufin cutarwa ba suda alhaki akan mu sai Allah ya kare su mu kuma Allah ya mayar mana da mugun abin mu kanmu.
Ko shakka babu rashin lafiyar rufaida yana da nasaba da mugun abin da muka ƙulla,domin boka ya gargaɗe mu akan mu kula sosai da abin da ya bamu kar mu yi sake da shi,idan ba haka ba tabbas za'a samu gagarumar matsala.
Sai dai kuma kash! abin da ake gudu shine ya faru...".
Nan take ya shiga labar ta musu tun daga zuwa wajen boka har lokacin da ƴan fashi suka tare su.
Ya ƙara da cewa:
"A gaban idanu na aka kashe min abokina kuma amini na har lahira! ni kuma suka dinga harbi na a ƙafafu na wanda a sanadiyyar haka ne ya jawo na rasa ƙafata guda ɗaya"
Ya ƙarasa maganar kuka na cin ƙarfin sa.
"Yanzu gashi bamu samu biyan buƙatar tamu ba, sannan duk abin da muka mallaka ya ƙare wajen jinya,gashi na nakasa, ita kuma RUFAIDA ta zama rabin ta mutum rabin ta gawa".
Ya ƙarasa maganar yana fashe wa da wani irin kuka kamar ana ƙona masa sassan jikin sa sakamakon ciwo da ƙuna da zuciyar sa take yi.
Gaba ɗaya ɗakin kuka suke yi gwanin ban tausa yi.ɗagowa ya yi ya dubi Aminu tare da cewa :
"Aminu gobe idan Allah ya kaimu zaka je ka siyar da motocin rufaida duka biyun, sannan ka haɗa da gwala-gwalan da suka rage suma ka siyar sai ka haɗa kuɗin kaja jari ko Allah zai sa mu samu abin da zamu rufawa kan mu asiri, wannan itace kawai mafitar da ta rage mana!!"
Ya faɗa yana share hawayen da suke zarya a kan fuskar sa.
Gobe idan Allah ya kaimu idan malam salihu yazo zan yi masa bayani a kan rashin lafiyar rufaidan ko da wani taimakon da zai iya yi mana".
Cikin murya mai rauni tace:
"Duk abin da ka faɗa gaskiya ne ALHAJI, Allah ubangiji ya sa a dace!!"
Amsawa dukkanin su suka yi da ameen.
Daga haka momy ta miƙe domin kawo wa su Alhaji USAMA abinci..✍🏻
Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni,ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa,ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi 🙏🏻🙏🏻
Daga Alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI(ummu AYSHA)......✍🏻✍🏻
Ga masu neman wannan littafin tun daga farko har zuwa in da aka tsaya su tun tuɓeni ta wannan numbern wayar 👇🏻👇🏻
08162055134.
Share fisabilillahi.
💝💞HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)......✍🏻✍🏻
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens........✍🏻✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages___________61&62
______________bayan dawowar su gida ba ƙaramin farin ciki halimatu ta yi ba sakamakon bayyanar mahaifin ta,ba ita kaɗai ba hatta momy ta ji daɗin ganin mahaifin halimatun sosai ko ba komai idan iyayen mukhtar suka ganshi za su ƙarajin nutsuwar aurawa ɗansu ita.
Waya ta ɗakko ta kirawo daddy ta sanar masa da abin da yake faruwa,shi kansa ba ƙaramin daɗi yaji ba da wannan labarin, yayi murna sosai da sosai,in da yake shaidawa momyn cewa idan Allah ya dawo da shi za su je har gida shida Alhaji Auwal su gaishe shi.
MOMY tace:
"Hakan yana da kyau sosai"
Daga haka suka yi sallama da juna tare da ajiye wayar.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali.
A ɓangaren halimatu kuwa tana ta zuwa makarantar ta,kuma Alhamdulillahi tana fahimta sosai da sosai,da yake tana da ƙoƙari shi yasa karatun bai bata wahala sosai ba, kwata-kwata bata sakarwa mutane fuska.
Bata mu'amala da kowa sai salma,duk da cewar ita ma salman ta daɗe tana ja mata rai kafin ta yarda ta fara kula ta.
Kullum suna waya da mukhtar ɗin ta sau biyu a rana,wani lokacin ma idan yana free har sau uku suke yin waya da shi. zuwa yanzu kuma shirye-shiryen dawo wa gida yake yi domin ya kammala abin da ya kai shi cikin babbar nasara.
Zaune take a gefen bed ɗin ta da waya a kunnen ta tana ta sakin murmushi daga gani hirar tana yi mata daɗi sosai.
Cikin sassanyar muryarta mai haɗe da shagwaɓa ta buɗe baki a hankali tace:
"toh yanzu yaushe zaka dawo.?"
Daga ɗaya ɓangaren MUKHTAR yace mata cikin zumuɗi:
"Kinaso na dawo ne my love.?"
"Eh mana habibi,bakasan na yi missing ɗin ka sosai ba.?"
Wani irin daɗi ya ji mara misaltawa ya mamaye ilahirin zuciyar sa,yanzu kam ya ƙara yadda cewa halumatu ta fara sonsa.
Cike da nishaɗi ya ce:
"Ai na ɗauka ba kiyi missing ɗina ba shi ya sa na ce bari na yi zama na anan kawai"
Kukan shagwaɓa ta saka masa kamar yana gaban ta tare da cewa:
"Ni dai gaskiya ka dawo habibi ina son ganin ka"
Wata iriyar kasala ce ta saukar masa sakamakon kukan shagwaɓar da ta ke yi masa,nan take ya fara saukar da ajiyar zuciya a hankali a hankali,gaba ɗaya ya rasa nutsuwar sa.
Da ƙyar ya iya buɗe shaƙaƙƙiyar muryarsa kamar wanda ya bugu yace mata:
"Sorry my love ya isa haka! ke baki san kukan ki yana ɗaga mun hankali ba! wane ni da zan ƙi dawo wa! ina nan tafe in sha Allahu nan da kwana huɗu! me kike so in taho miki da shi.?"
Ya faɗa cikin sigar lallashi.
"Duk abin da ya yi maka ka kawo min ina so habibi na".
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa:
"Baki da damuwa my love"
"Tun da na faɗa miki ranar da zan dawo mai zaki tanadar min .?"
"Me kake so habibi na.?"
"Tarɓa nake so ki yi min mai kyau sosai my love"